← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 113

Sashe 25

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu kuma na dauko wayar da nufin na kira sai kika riga ni, Ina fatan kin yini lafiya?"

Haushin sa ya kama ta sosai ta kasa tanka masa, amma tana raya cewa wai ya manta da jin muryarta.

Jin ta sake masa shiru sai ya kashe wayarsa.

Ita ma ta ajiye wayar daga kunnenta, tana gaskata zarginta na zaton MK da gaske ba son ta yake yi ba.

Kafin ta yi yunkurin yin wani abu kiransa ya sake shigowa ta yi kamar ba za ta dauka ba sai kuma zuciyarta ta kasa jarumta. Haka ta sa hannu ta amsa, ba tare da ta yi magana ba.

"Kina jina?"

Abin da ya furta ke nan, ta sake yin shiru! takaici ya kama shi cikin fa'da fa'da ya ce, "Kin san ba za ki yi magana da ni ba mene ne zai sa ki kira ni?"

Sai kawai ta saka masa kuka mai tsananin gaske irin mai cin rai! Ya yi shiru yana jin kukan nata wanda yake rasta dukkan sassan jikinsa musamman yadda take yi tana ajiyar zuciya.

Jikinsa ya yi sanyi sosai sannan kuma hankalinsa ya tashi, duk da ya san ma'abociyar kuka ce ita din, amma wannan ba na zallan shagwaba ba ne, da alamun damuwa sosai a cikin kukan.

Ya yi kasa da muryarsa sosai ya ce, "Me ya faru, fada mini mene ne yasa ki kuka haka?"

Jin ya karya murya yana tambayar ta sai wani kukan ya sake kwace mata sosai wanda ya tayar da hankalin MK sosai.

A gigice ya dinga fadin "Don Allah ki yi shiru ki fada mini me ya faru, kin tayar mini da hankali."

Ta kasa magana saboda kukan ya ci karfinta ita kanta so take yi ta daina amma ta kasa sai shesshka da ajiyar zuciya ta ke yi.

Ya yi shiru yana jinta, yana jin shi ma tamkar ya rushe da kukan ko ya sami sau'kin yadda zuciyarsa ke bugawa.

Ya lankwashe murya ya ce, "Sa'adah! so ki ke ni ma na yi kukan ne? Don Allah ki taimake ni ki yi shiru haka nan , ko so ki ke kanki ya yi miki ciwo?"

Cikin kukan ta ce, "Ka damu da ni ne da har kake gudar mini jinya?"

Ya ce, "Haba Sa'adah wacce irin magana ce wannan! Ai ni gani nake yi Baffa da Inna ne kawai suka fi ni damuwa da ke "

Ta yi fit ta ce "A hakan?"

Ya nisa sannan ya ce, "Ke matsala ta da ke ba ki fahimce ni ba, har yanzu kin kasa gane manufata. Kowanne Dan adam yana da tsarinsa, don ina sonki ba zan miki karya ba, abin da nasan zan iya shi zan miki, amma tun ba mu je ko'ina ba, na gane kin raina kulawar da nake ba ki gaba'daya"

Ya dan yi shiru sannan ya nisa ya ci gaba da fadin, "A farko tsakanina da Allah kamar yadda na fada mikil saboda jarrabawar da za ki yi yasa ban cika yawaita zuwa da kuma kiran ki a waya ba, sai ke kuma hakan ya zama dalilin da kika mini kishiyoyi, alhalin kin san har a gidanku na bayyana kaina ina son auren ki"

Ya fada muryarsa da rauni sosai.

Yayin da ita kuma kukan ya tsaya mata cak, tana jin wani irin abu na taso mata da ta kasa tantace mene ne shi.

Ya sake cewa, "Sa'adah duk motsin ki akan idona kike yin sa, ta ya ya ki ke tsammanin zan saki jiki da ke alhalin na tabbatar zuciyarki tana rawa a kaina! Na dade da gane kin samu mai kudi, na dade da sanin kina tare da Khalil har yanzu, ba don ina son ki sosai ba ai kamata ya yi na janye kaina a cikin 'yan takara amma kullum ina karfafa wa kaina guiwa da cewa idan rabona ce ke zan same ki, duk da haka dole na yi kaffa-kaffa don ba ni da tabbacin kina so na bare nasa rai Sugar Daddy ba zai kada ni ba!"

Kunya ta lullube ta, da kyar ta iya cewa "Ba ka da tabbacin Ina son ka fa ka ce?"

Da sauri ya amsa da cewa, "E wallahi da kina so na ba za ki saurari kowa ba, kin ga ni namiji ne zan iya hada mata biyu ko sama da hakan a rana na aura, amma tunda ke nake so, ke na aminta ta zamo mini uwar 'ya'yana ban sake kula wata da sunan soyayya ba. da na lura ba ki ba ni irin wannan matsayin ba, shiyasa na ke janye jikina, musamman yadda kika ci gaba da kula fitanannen yaron nan."

Kalamansa sun sa mata kasala sosai bayan kunyata ta da suka yi.

Da kyar ta bude baki a hankali ta ce, " Na daina!"

Ya yi murmushin da ya iso har cikin kunnenta, ya ce, "Mai ki ka daina din?"

"Abin da nake yi da ba ka so! Sannan kai ma ka daina mini wulakanci, kana nuna mini ba ni da daraja a gunka"

Ya sake murmusawa ya ce, "Akwai darajar da ta wuce na aure ki, na killace ki a gidana?"

Kunya ta kama ta, ta yi shiru dadi na cika mata zuciya.

Ya lankwashe murya sosai ya ce, "Ke ba ki san idan na tsananta zuwa ina kallon ki, za a samu matsala ba? Ko fa waya mu ka yi mai tsayi sai wanka ya kama ni, ya kike ganin kuma idan kullum zan gan ki a kusa da ni?"

Kunya mai tsananin gaske ta kama ta ta kashe wayar tare da rufe idanuwanta tamkar yana tsaye a gabanta.

Ya kira tana gani har ta katse amma ta kasa dauka ya ci gaba da kira har sau uku ta kasa dauka saboda yadda ya ba ta kunya.

Sai ga text ya shigo ta bude ta karanta kamar haka

_"Da gaske nake yi Sa'adah, don haka na roke ki, ki daina kallon rashin zuwana akai-akai da sunan rashin daraja ki, kokari nake yi mu kiyaye dokokin shari'a! zan zo gobe bayan Masallaci amma plz kisa hijabi ki 'boye wadannan abubuwan da suke karya mini alwala. Good night!"_

Ta karanta yafi sau ashirin tana jin shauki mai dadi na fizgar ta, tana jin ta tamkar a gajimare take yawo tsabar dadin soyayya. Ta hakikance MK shi ne mabudin farincikinta, duk wata damuwar zuciyarta ya wanke mata tas.

Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*TALLAH*

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._

40.

Washegari tun safe Inna ta lura da yadda Iyah ta tashi da kuzari da walwala, duk ayyukan gidan cikin kuzari take yin su sabanin kwanakin biyun da suka gabata da ta ke sukuku.

Kafin La'asar ta shirya, sai dai ta rasa hijabin da za ta saka. Gabadaya hijaban ta guda uku ne, biyu na Islamiyya ne, dayan kuma sallah take yi da shi, ta yi shiru tana nazari sai ta zabura ta fita. 'Dakin mahaifiyar ta shiga ta lalubo wani hijabinta da ta sayo a Jos amma ba ta taba sawa ba, a tsakar gidan ta ware shi kalar fari da maroon fulawa a jikinsa ya yi kyau sosai, ta saka ta ga ya zarta guiwarta da kadan, ta isa kusa da Inna da take zaune ta na tsinkar zogale ta ce, "Inna na dauko Hijabin nan."

"To." Kawai ta ce mata ta bita da ido, tana mamakin yau Iyah ce za ta saka hijabi ba don zuwa makaranta ba? 'Dakinta ta koma ta gama shiri, ta fito sanye cikin riga da siket na wani yadin material mai laushi, maroon colour! Hijabin ya hau sosai, ba karamin karbar ta suka yi ba.

Tana fitowa Inna ta juyo ta zuba mata ido tana raya komai Iyah ta saka sai ya mata kyau, ta ce, "Da kin san yadda Hijabin nan ya miki kyau da kin daina saka mayafi kin koma ado da hijabai."

Dariya ta yi tare da cewa, "Allah Inna tsokana ta kike yi"

"Da gaske nake yi miki, ba ki gan ki ba tamkar bakar Balarabiyar Habasha."

Dariya Sa'adah ta dinga yi sosai tana cewa, "Ashe har haka autar ki take da kyau Inna?"

Can kuma ta katse dariyar ta ce, "Inna Uncle Mukhtar ne zai zo kuma ya ce zai shigo ya gaishe ki."

Dadi ya sake kamata da sauri ta ce, "To! Kamo mini Baffanku a waya na fada masa."

"Kai Inna don zai gaishe ki ne za ki ce a fada wa Baffa?"

"Dole na fada masa mana tunda dai bai san wani zai shigo masa gida ba, idan bai amince ba ai kin san kuwa ba yarda zan yi ya shigo ba."

Sa'adah ta tura baki gaba alamun maganar Inna ba ta mata dadi ba ta ce, "Inna Uncle din ne wani?"

"Wani ne mana tunda ba mu da alaka da shi, sai ya aure ki tukun, zai zama cikin ahalinmu, amma a yanzu kam dole yana da iyaka."
Chapter 25 · 0% Book details