← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 113

Sashe 103

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka yayi ta kewaye da ita tana samun karamci daga wurin mutanen Sokoto da basu san komai ba sai alheri.

Sai maghrib suka isa hotel dinsu. Ya dawo daga sallah isah, ya dinga yi mata rawar da lallashi kala kala, amma ta yi funfurunfus ta 'ki ko da kula shi, balle ta bashi hadin kai.

"Ashe duk nasihar Umma ta bayan kunnen ki ta bi? Duk yadda na gama yawo dake a gari, dan ki mini yadda nake so, sakayyar da zaki mini kenan?
Wallahi cikina ciwo yake yi, marata a daure take, ki yiwa Allah ki bani dama, ban son na yi miki dole plz my Sa'a".

Ko motsi ta ki yi balle ta tanka, ya gaji ya kwanta a gefenta, yana ta murkususu.

Can kamar awa daya ya kasa hakuri ya janyota, ya fara shafata, ta yi firgit ta tashi, ta fizge, ya kalleta ya gano har yanzu rarrashi baya tasiri akanta, dan haka ya bita ya danne yana jin komai zai faru a yau kam sai dai ya faru amma ba zai 'kyale ba.

Ya fara kici kici da doguwar rigar atamfar da ta sanya, wadda ta kamata soasai, amma dan ta takura shi, yasa da ta yi wanka ta daukota a akawatinta ta sanyata a daren ta kwanta da ita.

*Gashi nan har da na gobe*

SURAYYA DAHIRU.
✍️.

*HALIN YAU*!

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916

*Ga Dukkan daliban UNITY KACHAKO*
*Mussaman aji na 2008*.
*Fatan alheri a duk inda kuke.*

*Sakon taya murna ga dukkan ahalinmu bisa samun karuwar 'Ya mace da muka yi a ranar alhamis 21-7-22.*
*Ina addu'ar Ubangiji ya Raya Rabi'atu akan tarfin islama, ya albarkaci rayuwarta. Allah ya bawa mahaifiyarta lafiya, ya bawa Mahaifinta ikon kulawa da su*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

109-110.

Duk kokarin Sa'a ta kasa kwatar kanta a hannun Mk! Domin gaba'daya a rikice yake, ba zato ta ji yasa dukkan hannuwansa da 'karfinsa ya keta rigar nan, wadda sabuwace ko ruwa bata shiga ba.
Haka ya cire mata tare da yin wurgi da ita.

Ya matu'kar jigata kafin ya samu, ya isa inda yake nufin isa, saboda yadda ta ki bashi hadin kai ko kadan. Sai da ya gwada mata karfin kwanji.

Ya matu'kar jimawa yana abu guda, ba karamin kidima ya shiga ba, a lokacin da ya zo samun nutsuwa, saboda yadda ya ji wata irin jijjiga tunda kansa har kafarsa. Karshe ya kammala cikin kuka tamkar ba Namiji ba. Dukkansu kuka suke yi, mai tsuma zuciya, na Sa'a mai sauti, na Mk kuma hawaine zallah, na tsananin farin-ciki, ya da'de yana ro'kon ubangiji ya sake nuna masa lokacin da zai kebe da Sa'a a matsayin miji da mata.

Gefe kuma takaicinta ne ya kama shi na yadda ta wula'kanta shi, tamkar bata san shi ba, duk irin ro'konta da ya yi.

Ya yi shiru yana jin kukan da take tamkar wadda ba aure suka yi ba.

Ba'kin cikin ke nukurkusarta, mussaman idan ta hararo haka fa yake yiwa Farida.

Ta kasa daina kukanta, shikuma Mk wani irin zazzabi ba zato ya saukar masa, tun yana daurewa har hakoransa suka fara kadawa, jikinsa ya dinga bari.

A farko share shi ta yi, sai da ta ga tabbas jikin ne, tasa hannunta, ta ji zafi sosai a jikinsa, ga hawaye sai zubo masa suke yi.

Ta yun'kura ta laluba akawatinta ta dauko rigar barcinta ta saka, ta debo ruwa, tare da 'karamin tawul 'dinta, ta dinga goga masa a jiki. Hankalinta ya matu'kar tashi, ba ta san har yanzu haka son Mk yake da karfi a zuciyarta ba, sai da taga yana zazzabi nan, saboda gaba'daya jijjiga yake yi.
Damuwarta ta kai kololuwa, ta dinga jin inama ita take wannan ciwon shi kuma yana jinyarta.

Ta dauko paracetamol ta bashi da kyar. Tana hawaye, tana tofa masa addu'a.

Mk bai samu sassauci ba sai wajen 'karfe biyun dare. Barci ya yi awon gaba da shi.

Sai da ya yi barcin sannan itama ta kwanta kusa da shi, hannunta rike da nasa hannun.

'Kiran farko akan kunnensa, ya tashi baya jin ciwon komai sai kasala, ya jima yana zaune yana kallon yadda take barci, tana sauke numfashi a hankali. Gashinta da ya sha gyara, yanzu duk a hargitse.

Wula'kancin da ta yi masa na rashin yarda da shi a farko ya matu'kar tayar masa da hànkali, zuciyarsa tana gasgata sonsa ne da gaske ba ta yi a yanzu.
Amma damuwar da ya gani a fuskarta a lokacin da bashi da lafiya, ya fahimci sonsa take da dukkan zuciyarta, kishi ne babban matsalar da idan ba'a yi taka tsan tsan ba zai sake ruguza musu rayuwar aurensu a karo na biyu.

Ya kudiri aniyar yi mata addu'ar samun sassauci akan kishinsa da take yi da ya wuce ka'idar Sharia da mizanin hankali, tunda ko aka ran kanta ba zata ji dadin rayuwarta ba.

Da kyar ya sauka ya shiga bayi, ya yi wanka, ya doro alwallah, sai da ya yi nafila, sannan ya tashe ta, ya fice zuwa masallaci.

Ya dawo, ya tarar da ita zaune akan sallayah da hijab a jikinta.
Ya cire jallabiyar jikinsa, ya kishingi'da a bakin gado, tana daga zaune a inda take.
Ta ce "Ina kwana, Ya jikin?"

A hankali ya amsa da cewa ", Lafiya lau Alhamdulillah".

Daga nan kowa ya yi shiru, sai tunanin zuci suke yi.

Tsawon lokaci kafin ta ji ya yi gyaran murya ya ce "Yau nake son mu tafi, amma jikina babu kwari, ba zan iya tukin nan ba".

A hankali ta ce "Ubangiji ya baka lafiya, sai mu jira zuwa gobe, mu ga mai zai zartar."

Ya yi shiru! Yana kallonta, yana jin sonta da tausayinta suna neman kassara shi.

A hankali ya ce "sanyi nake ji, da sauri ta mike ta fara kokarin ware bargo, Dan ta rufa masa.

Ya kalleta ya ce "Ba shi ba".

Zuciyarta ta buga, ta sani tun fil'azal idan yana zazzabi, sai dai ta cire kayanta ta mannu da shi, dumin jikinta shine maganin sanyin da zazzabi ke sababa masa ji.

Ta yi sororo bata san me yasa a duk sadda ya nemi ta'ba ta ba, sai ta ji wani irin bacin rai ya taso mata ba.

Tsayuwar da ta yi, yasa shi fahimtar abin da yake son ta yi masa ne, ya sake sanyaya jikinta.

Ya waske kamar bai gane halin da take ciki ba, ya sake cewa "Dan Allah".

A sanyaye ta cire rigar jikinta, ta bar pant dinta, ta isa gare shi, ta kwanta, ya yi mata wata irin runguma mai tsananin gaske.

Suka dinga sakin ajiyar zuciya! Ya dinga rada mata "Hold me tied please".

Amma Sa'a ta kasa yin komai, saboda rashin sukunin zuciya.

Tana jin yadda ya gyra kwanciyarsa ya fara laluben kirjinta da bakinsa, kan dole ta kyale shi ya zama tamkar sabon jariri saboda yadda yake tsotsar su.

Jikinta gaba'daya ya amsa, sai tsuma take yi, shi kuma rashin 'karfin jikinsa ya masa cikas din tafiya second round ko da ta 'karfi ne kuwa irin na daren jiya. A hakan da suke barci ya yi awon gaba da su.

9:18am dai dai Sa'a ta bude idonta, har lokacin kuma Mk barcinsa yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Fuskarsa na manne da kirjinta sai ka rantse baya samun iskar zukar numfashi.

A hankali ta zare jikinta, ta mayar masa da filo gurbinta, kamar yadda take yi masa a baya.

Bata tsaya a ko'ina ba sai a bayi, kai-tsaye ruwa mai zafi ta ha'da, ta yi wanka sosai, ta fito, ta shirya cikin matsakaiciyar kwalliya, ta zauna akan stool ta kasa daura dankwali saboda yadda take jin tsananin yunwa.

Bata son tashinsa, gashi kuma ji take tamkar ta ci babu saboda tsananin yadda cikinta yake yi mata karta.

Ta dauko hijabinta ta saka, ta dauko jakarta, ta nufi kofa da nufin fita ta nemi abinci.

Ta bude kofar kenan ya tashi, da azama ya ce "Ina zaki?"

Ta dawo da sauri ta ce "yunwa nake ji, tamkar an mini yasa a ciki".

Ya bata rai sosai ya ce "shine dalilin da zaki dauki hijab ki fita babu izni, alhalin kina kallona, Wai ke wanni irin raini kika mini ne? Ke ce zaki fita siyan abinci? Karatun naki abinda ya koya miki kenan?"

Ta yi shiru, ta kasa cewa komai. Idonta ya ciko da kwalla.

Ya ja tsaki ya mike ya shige bayi.
Bai wani jima ba ya fito, amma ita sai ta ga tamkar ya kusan awa guda.

Jallabiya ya zura ya dauko wallet din sa ya fice.

Mintina Kamar biyar, ya dawo dauke da ledoji a hannunsa.

Ya tarar da ita tana kan stool din mirror tana faman goge hawaye da tissue.

Ya ajiye ledar a gabanta ya ce "gashi sauko ki ci".

Ta yi tamkar ba ta ji shi ba, shikuma ya shige bayi, ya fara wanka.

Amma da yake yunwa ba kanwar uwa ba ce, sai ta sauko, ta hau duba ledar.

Leda daya dankalin turawa da kwai ne, 'dayar kuma doyace da aka soyata cikin kwai. Sai kuma leda mai dauke da daurin kunu biyu, na gyada da na tsamiya.

Doyar ta hau ci a yunwace, kafin ya fito ta cinye tass, sai ragowan kunun tsamiya a hannunta da take shirin zuke shi.

Sai da ya shirya, sannan ya zauna yana cewa "yanzu duk doyar nan kin cinye ke ka'dai, yaushe kika zama mai cin abinci haka? "

Takaici yasa ta cigaba da matso kwalla ta na gogewa, shikuma ya hau cin abincinsa hankali kwance, yana jin wani irin shau'ki. Bai san me yasa iskancin Sa'a ke tafiya da shi ba, ya lura a yanzu bata da burin kayayyakin 'kawa, ba ta harkar kawaye, cikin dabi'unta masu Muni kaifin harshe ne ya rage mata, shima kuma dole ta rage indai tana gabansa.

Amma sakalci, sai ya ga tamkar tana girma, yana sake bin jikinta ne. Ya tabbatar har kukanta yana jerin abubawan da yake kewarsu.
Chapter 103 · 0% Book details