← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 113

Sashe 62

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fili ya ce "ban da tabbas, amma idan har yanzu kuna tare na tabbatar kun tabbata wakilan manyan shedanu a doron 'kasa".

Ta 'kara karfin kukanta ta ce "Mala.. ya katseta ta hanyar jifanta da takalminsa da hagu. Tare da cewa "ki mini shiru, dama ai na fada miki ba zan sake yi miki uzziri akan shedanun yaron nan da baisan kimar da darajar aure ba".

Ya jima yana ambaton addu'ar we yayewar ba'kin ciki, *"YA HAYYU, YA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGIS*.

Ya 'dan sami nutsuwa ka'dan ya kalleta ya ce " kin yi wankan ko ba ki yi ba?"

Da'di ya kamata mussaman da ta tuna da asuba ya gama mitar hakurinsa ya 'kare, wannan karon period dinta takes too long. ta yi dariya ta ce bai 'karu ba kawai matsuwar da ka yi ne, amma dai nasan ba tantama I will be ready today.

Tunaninta nemanta zai yi tunda dabi'arsa ce ya kusanceta a lokacin da ya ga shaidan zai dagula zaman lafiyar su.

Da hanzari ta ce "Na yi".

Ya zuba mata ido sosai yana so ya ji ko akwai sauran gurbi a zuciyarsa da zai sake yi mata uzziri, sai ya ji babu saura, yana jin idan bai rabu da ita ba, tabbas ba'kin cikinta ne zai zama ajalinsa.

Dan haka muryar sa cike da rauni, hawaye na zirarowa ya ce "*Na sake ki, saki daya Sa'adatu*! Na ba ki dama ki zama yantacciyar da ki ke fata".

Ta 'kwala uban ihu mai gigitarwa.

30/04.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_

*Godiya ga makaranta*
*Ina matu'kar Jin dadin yabawar ku kan rubutuna, Hakika da kune Halin Yau ya je inda ban yi zaton zai je ba. na gode muku dukkan makaranta littafin HALIN YAU da fatan ana lura da sakon da nake nufin isarwa, ana watsi da shiriritar da yake ciiki, Ubangiji ya bamu damina Mai albarka*.

*Bari na sada zumunta da ku masoyan Sa'adah*
*Hajiya Rabi Sani*
*Aisha(cisse)*
*Tababa ta Malam*
*Asma'u Umar Ingawa*
*Samira Annuri*.
*Khadija Sadiq*
*Safara'u Niger*.
*Zainab Abdallahi*
*Aishatu maina*
*Khadija Bishir(Dijengala enterprises)*.
*Masoyan da yawa mu tara a shafin gaba*.

* SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

78.

Kuka ta ke yi tamkar ranta zai fita, ta rarrafa ta ri'ke kafarsa ta dama.
Cewa ta ke yi " Kar ka mini haka Malam, laifina bai kai ka 'dau wannan hukuncin ba, dan Allah ina sonka, ina son zama da kai".

A hanzarce ya fincike kafarsa, ya nunata da yatsa amma ya kasa bude baki ya mata magana saboda yadda yake jin wani irin sanyi na ratsa shi duk kuwa da yanayin garin a daure yake da zafi, saboda hadarin da ya hadu amma ruwa bai sauko ba.

Da 'kyar ya mike, ya shiga dakinta, ya dauko mukallin motar wadda yana tsakar dakin a yashe, rashin nutsuwa ya hana shi ya gani.

Ya fito, ya tsaya yana kallon yadda take kuka mai tsananin ciwo, irin kukan nan da ba ya sa a ji sau'kin tashin hankalin da aka tsinci kai a ciki.

A hankali ya ce "Tashi muje na kai ki gida".

"Dan Allah Malam ka yi hakuri Ni bazan tafi ba".

Fuskar nan a daure tamkar hadari ya ce " Ba za'bi na baki ba, ki tashi na kai ki cikin mutunci, tun ba ki tafi dutse a hannun riga ba".

Hawaye face face a fuskarta, Ta ce "iddah zan yi a dakina kamar yadda shari'a ta tanadar, ka girmama shari'a.

A kufule ya ce "wallahi ba anan gidan ba, ki je, ki yi a gidanku duk wata zan aiko miki abin da zai ishe ki! Na 'ki na girmama shari'ar, ke iyakokin ubangiji nawa ki ka take saboda son zuciyar ki, yanzu ne ki kasan ka'idojin shari'ar?"

Ta yi 'kasa da kanta dan kaucewa kallon tsanar da yake mata.

"Tashi muje" ya fada a kausashe.

Ta 'ki koda motsin kirki, sai shesshekar kukanta kawai, wadda ta ke yinsa har cikin 'bargonta.

A hasale sosai ya ce " Sa'adatu taurin kai a yau ba zai amfane ki da komai ba, bazan dauke ki da karfi ba, amma ki sani idan har ba ki tashi na mayar da ke cikin mutunci kamar yadda aka bani ke cikin mutunci ba, komai zai iya faruwa a tsakanin mu, na tsani na bude ido na ganki".

Nan ma ko uffan ba ta ce ba, sannan kuma ta 'ki tashin.

Ai kuwa ya ce "shikenan! Komai ya faru ki kuka da kanki, ya shiga 'dakinsa, mintina biyu ya sake fitowa ya dubeta tana kuka tamkar Baffah da Innah sun mutu rana 'daya, amma ko tausayi ba ta bashi ba.

A kausashe ya ce "Zan fita yanzu! kuma wurin Baffan zani na fada masa yau na mayar da ke 'yantacciya, amma ki sani Billahillazi idan har na fita ni ka'dai na haramtawa kaina ke, idan haka ta faru, shari'ar ta ce ba dalilin ki zauna kimin idda a gida ko?".

Tamkar tab'ab'biya ya ga ta mike ta fita waje a guje, ya bi bayanta dan ya lura tamkar ta zauce ne.

Ba ta tsaya a harabar gate din su ba, waje ta fita kai tsaye, ta yi kicibus da wani tsoho sosai, zai wuce, a gabansa ta zube cikin fitar hayyaci tace "ka taimake ni Baba"!

Dai dai lokacin Mk ya fito ya tarar da su a hakan.
Da sauri ta dinga cewa "ga shi nan Baba, bashi ha'kuri saki na ya yi, fa'da masa Allah ba ya son saki, yana kuma tare da masu hakuri"

Kallonta kawai za ka yi ka gane sakin nan ya susuta ta, ya gigita ta sosai.

Tausayinta ya cika zuciyar dattijon, ya kalli Mk ya ga shima a gigicen yake kwarai da gaske.

Duk da hakan sai yace "zo kusa da ni 'dana, Mk bai 'ki ba, hakan nan ya matsa kusa da shi ya tsugunna, a tausashe yace "ka yi hakuri ka ji! da gaske Allah na tare da masu ha'kuri, ba a biye sha'anin mata, yanzun nan za su rufe ido su yi abin da za su shekara suna nadama".

Mk dai baice masa komai ba, bai ji kuma zai janye sakin nan ba, tabbas sai ta je ta banbance tsakanin zaman gidan miji da rayuwar da take hari wannene 'yanci?

A hankali tsohon ya kuma fa'din "na tabbatar ko iya haka ka barta ta gane bakin Rijiya ba wurin wasan makaho bane".

Murya ba sauti Mk ya ce "Baba kar ka sa na yi abin da zan zalunci kaina, ina ro'kon ka, ka yi ha'kuri, al'kawari 'daya zan maka, matu'kar zuciyata ta huce da lamarin yarinyar nan, to kana cikin wadda zata ci darajar su na yafe mata, amma a yanzu idan ka tirsasani na mayar da ita, auren namu zai iya lalacewa gaba'daya, ka yi ha'kuri ka fahimce Ni".

Kafin Dattijon ya yi magana Sa'adah ta zabura ta sake kwasa a guje ta shige gidan.

Tausayinta ya cika zuciyar wannan tsohon, ya riko Mk sosai ya ce " Na fahimce ka 'dana, ba kuma zan maka dole ba, mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo! Amma ina son ka ri'ke a ranka cewar yarinyar nan tana sonka sannan uwar ya'yan ka ce, dan haka kar ka yi amfani da zato wurin hukunta ta, ka boye laifin ta, Allah ya muku albarka gaba'daya, ya kuma huci zuciyarka".

Da ga haka ya saki Mk ya juya, ya tafi, ga mamakin Mk sai ya ga cikin sakwanni mutumin nan har ya yi tafiyar da ya bacewa ganin sa, ya dinga wasiwasi anya kuwa wannan mutum ne? a tsufansa ba zai iya irin wannan sauri haka tamkar walkiya ba, ya shiga gida yana ayyana ko dai aljanine cikin aljanun Sa'adah.😂

A bakin motar ya tarar da ita, tana tsaye hawaye ya ki tsaya mata.

Ya bude gate din, sannan ya karasa ya bude motar suka shiga, sai da ya rufe gidan sannan suka tafi.

Ta by pass hanyar 'Dorayi ya bi dan haka hanyar ba yawan motoci, sun zo daidai Wailari ya ga ta fara wata irin jijjiga tana cewa "Laifina bai kai wannan hukuncin ba, kar kasheni da raina, Baffa ba zai bar Ni na zauna masa a gida ba, ina ka ke son na tafi?" Sai kawai ya ga ta sume.

Kan dole ya gangara gefen titi ya bude ruwan roba na Highland da ke gaban motar mai dan sanyi, daga gidan Mahmoud ya taho da shi, ya watsa mata, ajiyar zuciya ta saki tare da rushewa da kuka sosai har muryar ta fara dashewa, fadi take yi "Ka ji tausayina mu koma gidanmu, Jawad zai yi kukan rashi na, komai ka ce na yi bazan kuskure ba, na yarda ka 'Kara aure, ka sake 'karawa, ka sake 'karawa, ya fi mini sau'ki da na rasa ka".

Idan ya ce jikinsa bai yi sanyi ba, ya yi 'karya, idan yace maganganun ta basu yi yunkurin karya masa zuciya ba ya yi munafunci.

Ya zuba mata ido yana kallon yadda tashin hankalin awa daya rak ya susuta ta, yaci gaba da kallonta yana so ya samu dalili gamsasshe da zai mata afuwa, amma da zuciyarsa ta hararo masa cewa "Hai'ntarsa take yi shiyasa ta 'ki bari ya ga ta'addacin da ta ke yi da aurensa akanta, sai ya ji zuciyar sa tana zafi tamkar ana gasa burodi.

Ya zuba mata ido ya ce"Sa'adatu kowanne bawa da irin kaddararsa, Allah ya sani na iya bakin kokarina na mu zauna lafiya, kuma shine shaida akan son da nake miki, matu'kar gaskiya zan fada miki, zuciyata ba za ta nutsu da ke a yanzu ba!
Al'kawarin da zan miki daya ne, ba wadda zai ji mai ya ha'damu, Ina tabbatar miki zan dauki laifin a idon kowa, kema kuma kar ki fa'dawa kowa ko da Baffa ne kuwa".

Ya yanko tissue yana goge'kwallar da ta cika masa idanuwa.
Chapter 62 · 0% Book details