← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 113

Sashe 80

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce " Amma Jawad wadannan sunyi kudi da yawa".

Ya kwakkwabe fuska ya ce Ni dai su nake so Malam"

Mk ya ce "To wadannan ragowan rigar da takalman da ka kwaso fa, kasan ku'din takalmi daya ma kuwa?"

Kai tsaye Jawad ya ce "Mami zan siyawa a kudina tunda bata zo ba".

Mk ya yi shiru ya ce "to ai kudin naka ba zai isa ba, sai ka mayar da zoben".

Ya ce "Ka cika mini ko ka ara mini ni dai ina son su".

Kan dole Mk ya biya kudin kayayyakin nan, wadda ba karamin jijjiga asusun ajiyar sa yayi ba, hatta Farida sai da abin ya mintsine ta, ta lura kusan kullum idan suka fita siyayya irin haka sai Jawad yasan me ya siyo wa uwarsa, Mk kuma baya iya tsawatar masa, kafin su tafi ta san ba karamin kaya zai tara mata ba.

Kawai shanyewa take bata ta'ba bari abin ya bayyana ba, Amma abin na tsaya mata a Rai, sai dai ana jimawa take kokarin mantawa.

Mk bai sha mamakin Jawad ba sai da ya bishi dakinsa ya ga ya dauko katuwar ledar da yake tara kayan da yake siyowa da sunan Iyah kayayyaki ne masu tsadar gaske.

Ya zauna a bakin gado ya ce "to kawo kudin da kace na ara maka, tunda ai kasan ciko mai yawa na yi maka"

Haka kawai Mk ya fada Jawad ya fashe masa da kukan shi kudinsa Mami zai siyawa jirgi tunda antaho anbarta a gida kuma Baffa bashi da kudin da zai biya mata.

Jikin Mk ya yi sanyi ainun ya kasa cewa komai, da kyar ya ce "Ai ba a haka Jawad! kenan wayo ka mini? Kullum ka yi ta fa'din jirgi za ka siyawa Mami ko zaka biya mata, amma ni ko keke banji kana cewa zaka siya mini ba, alhalin na fita sonka".

Yana goge idonsa da rigarsa ya ce "Zan siya maka Malam amma dai ka yi ha'kuri na fara yiwa Mami, kai kana da ku'di, Baban Anty yana da kudi, ita kuma basu da kudi".

Mk ya ji haushin Sa'adah ya cika masa zuciya na yadda ta zauna ta yi maganganu da yaro 'dan karami, gashi maganar ta shiga zuciyarsa ainun, ya tsinci kansa da fadin "me za'a yi da halin wannan yarinya".

Jawad ya ce "wacece?"

Ga mamakin Mk sai ya kasa cewa Sa'aadah, sai ya buge da fadin "wata fitananiyar student dina ce mai baudadden hali, mai wuyar sha'ani".

Haka suka cigaba da rayuwar su har wa'adin da Mk zai yi a kasar ya cika. Ya tattara ya taho ya bar Farida da Jawad tunda ita saura wattani uku suka rage mata, Dan haka ya bar mata Jawad dan shima ya kammala third term dinsa.

Duk juyin da Mk ya yi da jawad ya bashi kayan tsarabar sa da ya tara cikin katon akwati, baisa ya bayar ba, ya ce shi da kansa zai taho da kayansa domin ba ya so a kaiwa Sa'adah kafin ya dawo.

Har Suka kammala watan ukunsu Jawad ba ya bata matsalar komai, sai duk sadda suke hira Rabin hirarsa kuwa ta uwarsa ne.

Da azahar Suka sauka a Kano.
Kai tsaye gidan Hajiyar Bichi suka zarce suka samu kyakkawan tarba daga Hajiya ga abinci ta tanadar musu ba karmin mamakin girman Jawad ta yi ba

Ta kalle shi ta ce yanzu a shekaru biyun nan ka yi wannan uban girman wa zai ce shekarunka sha biyu?".

Yamma na yi Mk ya dauki Farida zuwa gidansa da suka zauna da Sa'adah, bai san me yasa ya kasa shigar da ita wanccan gidan da Sa'adah ta tsara shi ba, sai ya gyara ainihin gidansa. gaba'daya gidan ya sha gyara na mussaman hatta fasalin ginin ancanza shi ya zama mai upstairs (bene) an mayar da shi na zamani kwarai da gaske , haka nan ba karamin jere na garari aka yi wa Farida ba. Duk wadda ya shiga gidan sai ya burge shi sosai saboda tsarin ginin tamkar gidajen turawa.

Duk yadda Mk ya so ya tafi da Jawad Hajiya kin yarda ta yi ta ce "Ai dama daga nan gidan ka dauke shi, dan haka dauki matarka kuje ta huta gajiya, sosai Jawad ya yi murna da hakan domin yasan goben nan zata sa Uncle Ahamad ya kai shi wurin Maminsa.

Leda guda Jawad ya ajiyewa Hajiya na tsarabar ta ta dinga murna tana fadin "Na san zaka yi Imani Jawad".

Washagari kuwa Hajiya tasa Ahamad ya kai shi da katon akwatinsa da sai da ya nunawa Hajiya duka kayan ciki, ko kadan bata yi ba'kin cikin uban kayayyakin da Sa'adah ta samu ba, a ranta kuwa murna take yi tana fa'din "Haihuwa wadar sarari ko kana gudu haifi ka Yar".

Murna soasai Sa'a ta yi tana fa'din "ai Ni ka yiwa tafiyar nan Jawad, ubangiji ya raya mini kai, ya maka albarka mai yawa".

"Amin Mami" ya fada yana kwanciya a jikinta, tare da sake cewa "kina addu'ar na samu kudin ya kai na siyan jirgin naki kuwa?"

Inna da take gurin ta ji Hawaye na neman kwace mata, ta mike ta shige dakinta, tana jin dadi da tausayin yadda Jawad yake girmama lamarin uwarsa.

Dawowarsu Nigeria ya sake wayo sosai, aka saka shi a makarantar Intercontinental college tsananin hazakarsa yasa suka dauke shi J s 3, maimakon aji biyu da zai shiga.
Iya turanci gangariya da Jawad ya yi ya janyo masa farin jini ainun a gurin malamai hatta student son abota suke da shi.

A haka ya Saba da wani dan ajinsu Muhsin Sani Yar-gaya, a hirar su da Muhsin Jawad ya fahimci Malam da Mami sun rabu ne, wato divorce ne a tsakanin su.

Kusan Muhsin ne ya cusa masa dabi'ar kin Farida a dalilin shi Muhsin din mahaifiyarsa ta rasu shekaru biyu, sannan amaryar Baban su azabtar da su take yi, shi da yayarsa makaranta nan da suke zuwa ne kawai bata yi nasarar rabasu da ita ba, hatta magana da mahaifinsu sai a sace suke yi da shi domin shima tsoronta yake ji.

A hankali Jawad ya fara janyewa Farida idan ana son aga damuwar sa to weekend ne ace zai tafi gadon kaya. Ba irin rarrashin da Farida bata yi masa amma ya kame daga yawan yi mata hira, idan kuwa yaje gidan a takure zai zauna tamkar bai santa ba, abin ya damu Farida sosai hatta Mk ya damu, ya tabbatar kuma ba zaluntarsa take yi ba tsiya ce kawai irin ta 'Dan Yau.

Har aka kai jallin da kuka yake zuwa gidan, idan Hajiyar Bichi ta ce da Mk ya barshi tunda baya son zuwa, ya kafe sai yaje.

Rannan dai da abin ya ishe Mk a gaban Hajiya ya dinga fa'din "ko zai shide sai ya je gidan, da suka rayu shekaru biyu tana masa wahala bai 'ki ta ba, sai yanzu saboda ya samu shashar uwa tana kitsa masa maganganun iyashege to kanta zata cuta ta kuma cuci 'danta.

Ya kalli Jawad da yake bayan Hajiya yana kuka da hawaye ya zare masa ido ya ce "idan na kuma jin kace mini zaka unguwa uku sai jikinka ya fa'da maka ai can ba gidanku bane, kana kin gidan ubanka kana kwadayin gidan wasu, zo ka shige girma da arziki tun ban tashi ba, kuma nan din ma ba zaka dawo ba can din da baka so a can zaka zauna".

Jawad ya rushe da kuka yana cewa "Hajiya ki ce ya dawo da Ni dan Allah".

Aikuwa haka ya tafi da shi yana kuka , sai dai kaya kala biyu Hajiyan ta bashi tabbacin zai dawo kenan.
Shiyasa ya rage sautin kukan nasa.

Wannan matsalar gaba'daya Mk Sa'adah ya jinginawa ita ya dinga tunanin hanyar da zai magance ta.

Ana haka Jawad ya dinga wani irin zazzabi, karshe farankama(chicken fox) ta feso masa a jiki.

Hajiyar Bichi da kanta ta bugawa Inna waya ta sanar musu, Inna bata yi kasa a guiwa ba ta zo ta duba shi har da tsarabar kayan dubiya, ba yadda bata yi da Sa'adah akan su tafi tare su dubo Jawad amma ta ki.

Da kyar Inna ta shawo kanta bayan taje da kwana biyu, Suka shirya Suka je da Zainab Ma'aji wacce a lokacin wattannin ta biyar da aure, da kuma cikin wata hudu a jikinta. Ma'aikaciya ce a hukumar kidaya ta kasa reshen jahar Kano.

Cikin kwalliya sosai Sa'adah take, ta dawo wata irin mace da gayu da ilimi suka ratsata mussaman da Alhaji Mamman ya sake dawowa cikin rayuwar ta, ba karamin kudi yake sakar Mata ba, ita kuma bata kwangen yin sutura ta daukar hankali.

Komai nata daukar ido yake yi, ado take a yanzu irin wadda bata yi zaton zata yi irinsa ba, amma kuma cike da hankali da nutsuwa. A wannan lokacin ta kammala karatunta tana makarantar horar da lauyoyi ta Bagauda(call to Bar).

A motar mijin Zainab Suka je bayan sun tsaya a hanya sun masa siyayya ta sosai, kai tsaye suka shiga gidan ba wani nauyi domin dai Sa'a ta kan zo gaida Hajiyar duk da ba kasafai ba.

A falon Hajiyar suka tarar da Mk yana shafawa Jawad calamine lotion a jikinsa ko ina jikin Jawad din maganin ne adalilin duka jikinsa ta feso masa har fuska, farin maganin ya maida Jawad wani iri.

Suka gaisa da Hajiya cike da girmamawa, suka tambayi mai jiki.

Zainab ce ta gaida Mk cikin mutunci, har tana cewa "Uncle rabon da na ganka har na mance".

Ya yi murmushi yana cewa "kina cikin daliban da nake cikiyarsu Zainab! Ya mijinki da Yara?"

Ta 'kasa kuma kallon Sa'a kawai ya ke yi zuciyarsa na wani irin tsalle, yayin da ita ta yi tamkar bata ganshi ba, ko arzikin gaisuwa bai samu ba, ko Jawad da yake kusa da shi, sau daya ta masa sannu ta maida hankalinta wurin Hajiya.

Rashin gaisawar da basu yi ba, ya ta'ba Hajiya kwarai da gaske, yayin da Mk ya dinga fargabar wayewar da cigaban da ya gani a tare da ita, kwarai da gaske ta banbanta da Waccan Sa'adan da ya rayu da ita.

Zainab sai zungurar ta take yi akan ta gaishe shi, amma ta yi mirsisi.
Chapter 80 · 0% Book details