← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 113

Sashe 65

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin sa ya tashi, ya fara 'ko'karin fahimtar da ita da hujjoji, amma fur ta hau dokin na 'ki.

Ganin da gaske ta ke yi, shikuma a yanzu wani irin tsoro da firgicin zama da Sa'adah ne ya ke kama shi, bai ta'ba tunanin za ta yi abin da ta yi ba, mussaman yadda ya ke wadata da komai, uwa uba kuma yadda ya ke tarairayarta da gudun zuciyar ta, idan har hakan bai sa ta kiyaye masa amana ba, bai ga kuma me zai mata ba.

Kansa har zafi yake wurin tunanin, me yasa ta yin hakan? Ya tabbatar shi baya ha'intar ta akan me ita zata ha"ince shi?

Wani irin tsimin bacin rai ya taso masa, mai hade da kishin da ya haddasa tsanar Sa'adah, ya kasa bu'de baki ya yi magana kawai ya kife kansa akan guiwowinyasa ya fashe mata da kuka tamkar yana cikin shekarun 'kuruciya.

Wannan kukan ya matu'kar ta'ba zuciyar Hajiya, ta shiga ru'dani da wasiwasi akan lamarin Sa'adatu, kan dole, ta ha'kur'kurtar da zuciyar ta, ta ce ta janye takunkumin dolen da ta yi masa.

Amma a zuciyarta sai hasashen wanne irin abu ta yi mai muni haka?.

Sati guda da faruwar wannan lamarin, amma har lokacin Sa'adah na kwance ba lafiya., saboda ta 'kuntata zuciyar ta, ta 'ki cin abinci, kullum cikin kuka ta ke, ta yi wata irin rama mai tayar da hankali, kuka ta yi shi irin wadda ba ta yi tunanin akwai mahalu'kin da ya yi irinsa ba, ko ya ya ta ayyana Mk ya saketa, shikenan sun rabu? sai dai Inna ta jiyo ta 'barke da kuka tana fadin na tafka asara, na yi nadama.

Sannu a hankali zance ya shiga kunnuwan dangi, kowa ya ji mutuwar auren sai ya shiga alhini saboda yadda aka shaida soyayyar da Mk ya ke yiwa Sa'adah, mussaman Auntyn Lagos, Maman Gombe da Samira, hankalinsu ba karamin tashi ya yi ba, da kuka Antin Lagos ta 'kira Hajiya tana tambayarta gaskiyar magana, cike da tausayi Hajiya ta tabbatar mata sun rabu tabbas.
Da rawar murya take fadin "Hajiya ki matsa masa ya dawo da ita, na tabbatar duk inda ya ke, ba ya cikin nutsuwa, yana sonta".

"Hmmm kawai ki musu addu'a amma lamarin na su akwai tashin hankali." Inji Hajiya .

Wata guda Mk ya 'dan wartsake, ya koma harkokinsa da 'karfin zuciya irin ta namiji, sai dai abin na nan ma'kale a zuciyar sa yana jin har ya koma ga mahallicinsa ba zai manta ba, idan ya tuna dalilan da zai hana Sa'adah ta bashi wayar nan sai ya ji bugun zuciyar sa ya karu, wani lokacin har jiri ke dibansa.

Ga Sa'a kuwa wannan watan ta cinye shi ne a kwance tana 'dan'danar azabar ciwon so da nadama, tunda gyatumarsu ta kawo ta duniya bata taba fuskantar tashin hankali irin wadda ta ke ciki ba, fata take mutuwa ta dauketa ta huta da wannan zugin da zuciyar ta take mata, inama ta bashi wayar nan ya gani?
Wata'kila da ba zai zafafa lamarin har haka ba, tun shekaranjiya da ya aiko mata wasu cikin kayanta shake cikin akwati babba, yini ta yi a ranar tana kuka, ba abin da ta ke fata irin ta ji ko da Muryar Mk, amma abin ya faskara, ga tunanin Jawad rabon da ta ganshi tun ranar da suka rabu da Babansa, ta yi dalilin da suke rayuwa a wuri daban daban, wannan kadai ya isheta ladabtarwa.

Cikin wannan 'kangin ta sake cinye wani watan har da 'karin kwanaki goma, zullumi ya ishi Sa'a, saboda kwanakin iddarta na gab da kammala, duk wadda ya ganta yanzu, muddin ya santa a wattannin baya, sai ya tausaya mata, gashi dai ba ta rasa komai ba, amma ta rasa kwanciyar hankali, satin ta biyu a gidan Mk ya aiko da kayan abinci kala kala wadda za su kwashe rabin shekara suna ci, sai kuma ya mata siyayyar komai na bukatunta tun daga kan kayan shayi har sabulai, da tarkacen abubuwan da zata bu'kata, amma ko taba su ba ta yi ba, hakanan abinci sai Inna ta tausaya mata, ta zauna kusa da ita, ta matsa mata sannan za ta yafita .

A lokacin Sa'adah ta fahimci ba abin da yafi nutsuwar zuciya da'di, addu'a ta ke sosai akan ta sami sau'kin tashin hankalin da take ciki, idan ta ji yo su Baffah na hira har da raha shi da Inna sai ta tambayi kanta yaushe za ta fara dariya ne ita?.

Yanayin da ta ke ciki ya fi kama da na mai takabar da mutuwar managarcin miji ya zo mata kwatsam.

Daidai wannan lokacin Sumayya ta iso Kano dan jajantawa yar'uwarta halin da tsinci kanta a ciki.
Halin da tarar da Iyah a ciki ya bala'in girgiza ta.
Cike da tausayawa tace " Na sha fada miki halin da kika jefa kanki ba inda zai kai sai nadama, gashi tun ba a je ko ina ba, kina fuskantar Halin Yau! duk wadannan kawayen na ki da kika mayar allon kwaikwayon ki YAU suna Ina?"

Karon farko da Sa'adah ta fara jin sassauci domin sai a ranar ta Sami wadda ya mata fa'da, iyayen ta sun zuba mata ido, ba wadda ya buda baki ya mata fa'da, sun mata dungu suna gasa ta da idanuwan su kawai, hatta Baffah da ta tabbatar ba abin da yake so a duniya irin ta, wannan karon ta na hango ko oho da yake yi da lamuranta.

Ta ri'ke hannun Sumayya ta na wani irin kuka, tana fadin "kin fada mini, ba irin gaskiyar da ba ki fada mini ba, sai dai an riga an kadddara mini yanka kazar wahala, dole kuwa sai na figeta tas, Mukhtar mutumin kirki ne, laifin duk nawa ne, sai dai nima kadddara ce da bazan iya kauce mata ba, ki taimake ni Aunti! ki bashi ha'kuri, Tunda Baffa ya barni da kaina".

Ta shide tsabar kuka! Hankalin Sumayya ya ru'banya tashi, amma hakan ta daure, ta tausasa murya ta ce " ki daina irin wannan kukan, idan har kin yi amanna kaddara ce ta hau kan ki, to ki yi hakuri ki bita da istigifari, yawan kuka da 'kauracewa abinci da takurawa zuciya ba abin da zai haifar miki sai ciwon da zai kayar da ke, ina tabbatar miki duk wadda zai shiga damuwa a dalilin rashin lafiyar ki, ke ce dai mai jin jiki?"

"Na gode sosai Anty dan Allah ki 'kira shi, ko zai ga girmanki".

Sumayya ta nisa ta ce "Bana jin girmana zai sa ya janye kudirinsa tunda har bai janye saboda Baffah ba".

Hawaye ya kwaranyowa Sa'adah ta ce " Baffa ba ya son na koma ne, a gaban mu Mukhtar ya ce ya bashi umarnin ya mayar da ni, amma 'kememe Baffa ya 'ki, ya barni na ji da dabarata".

Sumayya ta yi shiru, tana jin tausayin 'kanwarta na sake kamata, ba ta gane muhimmancin mijinta ba sai da ya kubuce mata, ta tuna wani lokaci da ya shude tana mata fadan ta bi mijinta su zauna lafiya.

Ta nisa ta sake tuno amsar da Sa'adah ta bata a waccan lokacin, "Anty ki ta cemin na bishi, na masa biyayya ko da yana cutar da ni, akan me zan yi irin wannan rayuwar auren alhalin ko yau Mukhtar ya barni Ina da yakinin zan samu wadda ya fi shi."

Ta dago ta kalle ta, yau Mukhtar ya barta, da ya tashi barin nata ba shi kadai ya tafi ba, sai da ya yi awon gaba da dukkan nutsuwa da walwalarta, bugu da 'kari hatta kyaun da ya sa take ta'kamar zata samu wadda ya fi shi, ya tsiyaye tas, ta kai duba ga kirjinta , ta ga sun yamushe a cikin riga, mamaki ya kama Sumayya bata taba sanin nonon Iyah zai iya zubewa haka ba, domin ko da take shayarwa a tsaye kuma a cike suke, irin wadda suke ma'kale ne a kirjin mace, amma tashin hankalin da take ciki suma ya tabasu, hakanan gashin kanta sai saukewa yake yi, ga uwar rama sai ido gwara gwara tamkar idon agolan Banufe.

Ta ke Sumayya ta dinga neman tsari da shiga tashin hankali kwatankwacin irin wadda Iyah ke fuskanta, ta kuma nemawa yar'uwarta samun sassauci da mafita.

A hankali ta ce "zan 'kira shi, sai zuwa dare tunda yanzu yana gurin aiki, fatana dai ki kwantar da hankalin ki, ki karbi kaddarar ki da hannu biyu, yanzu a ina Jawad ya ke?"

" Ni ma ban sani ba" Sa'adah ta fada a sanyaye.

A daren ranar kuwa Sumayya ta 'kira layin Mk, da girmamawa ya amsa wayarta, suka gaisa, ta fara da tambayar Jawad, ya amsa da yana nan lafiya Lau, shima ya tambayi nata iyalan, da 'kyar Sumayya ta iya masa maganar Iyah, ga mamakinta sai taji ba alamun zafafawa, ya ce "Anty ku bimu da addu'a da ga ni har Sa'adatu abin ya zo mana a ba zata, muna bu'katar mu nutsu, zuwa gaba muga me ubangiji zai zartar mana, har yau ina sonta, Ina fatan mu sake zama, sai dai muna bu'katar hutu da nutsuwa, idan dukkan mu mun fahimci manufar auren, zamu dawo mu sake zama abu guda, amma for now, ya kamata mu bar komai a hannun mai juya al'amuransa ya mana zabi".

Sumayya ta amsa da "Hakane" tare da yi masa godiyar amsa 'kiranta da ya yi, ta rufe maganar da ro'kon ya kawo mata Jawad yaranta suna ta tambayar shi. Ya amsa da gobe juma'ah zai kawo shi ya yi week end tare da su".

Ta ajiye wayar, tana kallon Sa'adah da ta yi mata 'kuri tana son jin abin da ya ce.

Kasancewar Sumayya na cikin jerin mutanan da basa yiwa 'karya kwaskwarima dan su da'dawa wani, kai tsaye ta ce "Iyah ki barwa Allah zabi kin ji, idan zaman ku bai 'kare ba, za ki koma dakin ki, idan kuwa iya adadin da aka deba muku za ku yi kenan, ina tabbatar miki ba za ki koma ba, hakan kuma ba shine 'karshen farin ciki ba".
Chapter 65 · 0% Book details