← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 113

Sashe 24

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ganin kiran MK sai shigowa yake yi amma ba ta katse ba, tunda ta san shi ba wani lokaci mai yawa zai dauka yana lallabar ta ba, sai daga baya ta katse kiran Khalil bayan ta dauki excuse akan ya ba ta mintina biyar tana zuwa.

Tana kiran sa ya katse ya kira ta bai mata complain din da wa take waya ba, hakan ma yasa ta sake jin haushinsa, ya tambayi lafiyarta, ya kuma sanar mata cewa gobe zai zo abokinsa na son ganin ta, to kawai ta ce, a ranta kuma tana cewa abokinsa ne yake son ganina ba shi ba.

Washegarin kuwa suka zo shi da amininsa Mahmoud Karfi, wani abu mai kama da almara Mahmoud na dora ido a kan Sa'adah ya ji son ta ya cika zuciyarsa, ta zo masa a yadda yake burin samun matar aurensa ta kasance.

kwalliyarta, yangarta, shan kamshinta duk sun tafi da shi, amma sai ya yi yaki da zuciyarsa ya danne ta yana nanatawa kansa MK ya wuce ya hada soyayyar mace da shi, ya tabbatar idan MK ya gane yana son ta to tabbas zai bar masa.

Idan kuwa haka ne shi ne ya kamata ya haramta wa kansa wannan yarinyar da a yau ya dora ido a kanta, a daddafe aka yi hirar Mahmoud ya ba ta kyautar kudi dubu biyar suka tafi yana ta neman tsarin shaidan da zuciya da suke sake kawata masa Sa'adah.

Madalla da aboki irin Mahmoud wanda yake daraja abota da kuma sadaukarwa, ba wanda zai zagaye ya yi wa abokinsa kafar ungulu ba.

*BAYAN WATA UKU*.

Zuwa wannan lokacin Sa'adah ta canja sosai domin ba karamin kudi Alhaji Mamman ke sakar mata ba, ta mallaki zobunan Dubai Gold a boye har guda biyu. Ta mallaki waya mai kyau Sliding 'kirar Nokia da SIM a ciki, wayar dai Inna ta sani amma zobuna ta kife ta musamman da Innar ba ta san Gold ba.

Tun MK bai lura da canjawar Sa'adah ba har ya fara ankara da yadda kwallliyarta ta karu, ta daina dokin amsa masa waya, ta daina mitar rashin zuwansa, sannan dan flashing din da take masa ta daina idan zai kwana ya yini bai kira ta ba, baya taba ganin text ko flashing dinta.

Duk da bai san tana da waya ba har zuwa wannan lokacin shi da layin Inna ya ke kiran ta, so yake ya mata bazata jiran fitowar results dinsu yake yi, idan har ya yi kyau, waya zai siya mata, idan ma bai yi ba dai zai siya mata. Ashe shi bai san ta kerewa rike kananun wayoyi irin wanda yake harin siya mata ba.

Jikinsa ya fara sanyi don haka ranar wata Laraba ya kasa jiran Juma'a ta zo, ya shirya ya nufi gidansu da yamma.
Sai dai yana zuwa ya tarar da Alhaji Mamman zaune a kan tabarma, yana tsayawa a bakin zauren ita kuma ta fito daga cikin gidan ba ta 'karasa isowa zaure ba, amma idanuwansu sun sarke da juna, bai ce kala ba ganin Alhaji Mamman bai ganshi ba sai kawai ya yi murmushin da babu nisha'di a cikinsa ya juya abin sa.

Sai ta tsinci kanta da diriricewa, ta ji tamkar ta ruga da gudu ta ce masa ka dawo, kai nake fatan ace kai ne a zaune ba wannan mutumin ba, amma ba damar yin haka, a daddafe ta gaishe shi, ta gabatar masa da uzurin zazzabi take yi don kar ya ji ba dadi ne yasa ta daure ta fito. Ya gamsu a yadda ya ga duk jikinta ya saki ta yi wani iri, tashi guda, don haka ya fita ya je mota ya kwaso mata sayayyar da ya jido mata, bayan ya ajiye mata rafar yan 200 sabbi kal.

Tayi godiya ta shiga gidan zuciyarta daya tunda Inna ta je cikin Unguwa yinin biki don haka ta rage wasu kayan ta boye akan sai wani zuwan ta nuna mata.

Jikinta na rawa ta shiga lalubo lambar MK, amma har ta katse bai dauka ba, ta sake kira har sau uku nan ma bai dauka ba.

Alkalamin
*SURAYYA GWARAM*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan, ba tare da iznin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*Fatan alheri ga*
*Asma'u Sani*
*Aisha Lagos*
*(Mrs Dan manya)*.
*Shafin na ku ne ku yi yadda kuke so da shi*.

38_39.

Haka ta ci gaba da kiran har ta gaji, tana 'kiyasta adadin kiran da ta yi masa ya kai ashirin, jikinta ya mutu tamkar marar laka, zuciyarta ta cunkushe da fargaba, tasan tana son MK sosai amma a yau ta sake sanin son da take masa marar adadi ne, duk da kasancewar ba lokacin zafi ba ne sosai, amma zufa sai karyo mata take yi. Waya kuma na hannunta, tana ci gaba da kiran sa.

Tunda ya bar gidansu Sa'adah Masallaci ya nufa da 'kyar ya karasa saboda yadda zuciyarsa ta daure, ba abin da yake bukata sai kadaici. Ya Jima a zaune yana ta ambaton Allah har ya sami sassauci sannan ya dauki Qur'ani ya fara karatu a fili, a hankali, duk kiran da Sa'adah ke yi masa yana gani, duk da a silent ya mayar da wayar.

Bai bar massalacin ba sai da aka yi Magariba zuwa wannan lokacin ya samu saukin daurewar da zuciyarsa ta yi a dalilin kishi, ya fito daga Massalacin ke nan kiran ta ya ci gaba da shigowa ba kakkautawa.

Gefe sosai ya samu ya zauna ya fito da wayar ya katse kiran nata sannan ya kira ta.

Jikinta har rawa yake yi wurin amsa kiran wanda ta dade ba ta ji zakuwa da dokin amsa kiran sa ba kamar a wannan lokaci.

Muryarsa ba amo sosai ya mata sallama tare da cewa, " Sorry Sa'adatu! Kin kira na bar wayar a caji ne tun dazu sai yanzu na ga tarin missed calls."

Wani nauyin jiki ya kara kama Sa'adah, ta rasa kalmar da za ta furta saboda abubuwa biyu, na farko bai nuna ta masa laifi ba tunda da ban ha'kuri ya bude maganarsa bugu da kari ma katse kiran ta ya yi, ya Kira ta.

Na biyu ya ambace ta da Sa'adatu rabon da ya kira ta da hakan tun lokacin suna yar tsama, ita kam ya binneta, ha'kuri za ta ba shi ko kawai sharewa za ta yi kamar yadda ya yi?

Da kyar ta bude baki ta ce "Ai na dauka kana sane ka 'ki amsawa."

Tana rufe baki ya ce
"Ko daya to mai kika mini?"

Ta san sarai a cikin fishi yake, don haka sai ta lankwashe harshe ta ce "Ka yi ha'kuri don Allah!"

Da sauri ya cafe da cewa
"Ni fa ba ki mini komai ba, laifina ne da na zo kai tsaye ban sanar da ke ba, sannan ai yaudarar kai ne na yi tsammanin ni kadai kike kulawa, ke allura ce a cikin ruwa don haka feel free you did nothing."

Ta kasa gane inda ya dosa shin gatse ya ke mata ko kuwa da gaske hakan yake nufi a zuciyarsa?

Don haka sai ta ce "To ka dawo na ganka dama ai na kwana biyu ban gan ka ba"

Kai tsaye ya ce, "Ai ba na zuwa zance da daddaare"

Shiru ta yi sannan ta ce "To gobe za ka zo?"

Tana rufe baki ya ce "Ina da schedules masu muhimmamanci a gobe."

Kawai sai ji ta yi kuka ya zo mata, cikin rawar murya ta ce "Har sun fi ni muhimmamanci?"

Cike da rashin kulawa ya furta "Wadancan tabbas ne, ke kuwa gaibu ce."

Ta yi shiru amma kuka take yi, yana jin yadda ta ke jan majina da shassheka, amma ya yi burus da ita, yana fatan ta ji a ranta cewar ita ba wata tsiya ba ce a gunsa.

Cikin kuka ta ce "Ni ka ke kwatantawa da gaibu?"

Ko dar bai ji ba wurin ba ta amsa da cewa, "E!" A gajar ce.

Bai sani ba ko kishin dake cin zuciyarsa ne, ya sa bai ji kukanta ya taba shi sosai ba.

Yayin da ita kuma bakin cikin yadda yake nuna mata rashin kulawa yake dada addabar ta.

Duk da hakan sai ta daure ta ce "Jibi Juma'ar za ka zo?"

"Zan zo idan ina cikin masu rai da lafiya idan kuma uzuri ya taso ban sami zuwa ba, to sai satin sama."

Ta yi shiru tana jin ta rabu da wannan mutumin da yake nuna mata ita ba komai ba ce a idonsa, sanin ya gan ta da wani ta san dole zai ji ba dadi yasa ta ajiye komai ta neme shi.

Har ha'kuri ta ba shi amma shi ya nuna ma ba laifi ba ne bai yi fishi ba, anya kuwa yana son ta, anya ba ita ke bankaura akansa ba?

Jin ta yi shiru ya sa ya magantu da cewa, "Sai yadda ta yiwu." Ya katse wayar! Bakin ciki ya kama ta sai kawai ta kife kai a kan filo tana kuka.

Shi kuma ya mike ya mayar da wayar aljihunsa, yana sake jin sau'kin radadin da zuciyarsa ke yi masa, tunda dai ya tabbatar ita ma ta shaki takaici.

Washegari tun safe Sa'adah ke zuba idon kiran MK har aka yi sallar Isha bai kira ba, a lokacin ha'kurinta ya gaza, ta dauko wayar Inna ta shiga kiran sa, sai da ta gama ringing bai dauka ba, tana shirin sake kira sai ga kiransa ya shigo. Ba ta tsaya jan aji ba ta dauka da sauri sai kuma ta yi shiru ta ki yin magana.

Sai da ya yi sallama har sau biyu sannan ta amsa ciki-ciki, mamakin ta ya kama shi amma ya waske ya ce, "Mura ki ke yi ne?"

Nan ma ta yi shiru ya nisa ya ce, "Yau yini guda ban zauna ba, ina ta yunkurin kiran ki, sai wani al'amarin ya mantar da ni.
Chapter 24 · 0% Book details