Sashe 51
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idan ta kawo musu pure water, sai sunce ruwan warin nama ko karnin kifi yake yi, suna fadin freezer da zai siya ta nama da kayan miyane yake ganin asara, gara yaje ya rabawa yanmata a waje.
Tun bata yarda, har maganganun suka shigeta, mussaman da ta ga falon amaryar Mahmoud, sai ta sake rikicewa, ba tare da ta yi nazarin kayan da suke rainawa, ita ba'a Mata kamar su ba.
Ta fara rikice masa, ya kasa gane kanta, ya zauna yana rarrashin ta, har ya samu tace ita tibin bango take so ya siya mata.
Ya rikota cikin kwantar da murya yace "ki yi hakuri zan siya, amma ba yanzu ba, kinsan dai yanzu ba cikakken kudi nake samu ba, amma da zarar naci karfin biyansu, zan siyo miki, ba sai na kammala biya gaba'daya ba, ya kara da fadin wacce kamfanin kike so?"
"Sumsung"
"To ki daina bata ranki akan maganar tv, mecece talabijin kuma?"
Ya lallaba ta da maganar tv. sai kuma wayar Black berry ta shigo, kullum su Halima hirar BB chart, Safina kam tuni ansiya mata, yayin da Halima take fatan saurayin ta ya siyo mata.
A ranar da saurayin Halima ya kawo mata wayar, suka je gidan Sa'adah suka nuna mata, Halima na fadin " kina ganin saurayi ma, da bana daga masa kafafuwa, ya fidda kudi ya siyo mini, bare ke da kullum yake hakar ki".
BB chart din nan ya matu'kar gigita Sa'adah mussaman da aka tabbatar mata, sai masu irin wayar ne suke yi.
Kullum mitar ya siya mata waya take, rannan da ya gaji, ya zaunar da ita yace "kinsan za ki dame ni mai yasa za ki sani karban filaye biyu? bani da kudin siya miki wayar da kike magana akanta, Ni kaina ban ri'ke ta ba".
Ai kuwa zamansu ya dawo wani iri, saboda ta kudire a ranta da gaske yanmatan banzan yake yiwa hidima, ita ya barta ko oho, mussaman da ya ki yarda ya kaita ta ga filayen nasa.
Ranar wata juma'ah sai ga shi da sabuwar plasma TV 32 inch, ga mamakinsa ba ta yi wani murna ba, lamarin da ya bata ransa sosai.
Haka ya daure, ya kira mai gyara ya hada mata har da satellite.
Kallonta kawai yake yi, a zatonsa siyan tv zaisa zamansu ya dawo normal, amma sai ya ga sabanin haka, saboda ta riga ta yi nisa a son Black berry, ta samu shedanun kawaye na mata famfo.
Haka suke ta gungurawa, yau fari gobe tsumma, mussaman da ya tsaya akan ra'ayinsa na ba zai siyi waya ta makudan kudade ba. haka jarrabawar jamb ta fito, a lokacin da F.C.E. ta fidda jerin daliban da suka sami gurbin karatu har da ita, inda zata karanta primary care education jiran lokacin fara daukan darasi take yi nan da yan wattanni. Hakan bai sa ta sauko ba, saboda ita B.U.K. take so, Safina sai cewa take "mijinki is very smart
Ya rantse ba zai kai ki makarantar da yake ba, dan kar agane yana da mata".
Yau da gobe akace ta fi karfin wasa, ya gaji da zaman rashin walwalarsu, ya kukuta ya siyo musu Android shi da ita, a lokacin bata jima da fitowa ba, dan haka itama mai tsada ce, ga mamakinsa ko Na gode ta gagareta fa'da wadda ko kadan ba halayyar ta bace, ko abu bai yi mata ba zata yi godiya ko a gajarce ne.
Amma wannan ajiyewa ta yi a inda ya bata ba tare da ta duba ba, ransa ya baci da ita, irin wadda bai taba ji ba.
Ganin idan ya cigaba da zama kusa da ita, komai na iya faruwa a tsakaninsu na rashin jin dadi, yasa ya mike ya fita zuwa shagon sa, bai dawo ba, sai shadaya da ashirin da bakwai 11:27pm.
Ya sake tarar da wani 'bacin rai fiye da na farko, wato rufe masa gida, bugu ka'dan ya yi, ya hakura dan kar makwabta su fahimci abin da ke faruwa, ya dinga kiran wayarta ba kakkautawa, tana shiga amma taki dauka, karshe ma sai ta kashe wayar gaba'daya.
Haka ya kwana a gate a cikin mota, ya yi kwanan zafi, da sauro, barcin kansa rabi rabi ne, wannan daren yana cikin jerin dare masu tsayi da ya fuskanta a rayuwar sa.
Duk juyin da zai yi, tunanin irin hukuncin da zai mata yake yi, ya gaji da wannan bala'in, zai nuna mata, neman zaman lafiya ba shine lasisin da zata dinga wulakanta shi ba.
Koda asuba kin bude masa ta yi, dan iskanci kuma ta kunna wayar amma taki 'dagawa. Ya Mata text yafi sau goma, har kurarin zai fadawa Baffa ya yi, amma ko gezau.
Har taran safiya, yana harabar gidan. Takaicin sa daya, ba ya ajiye kaya a mota. Mahmoud ya kira ya fada masa halin da yake ciki.
Da kyar Mahmoud ya shawo kanta ta bude masa, domin kuwa cewa ta yi, ya koma ya dauwama a gurin Farida.
Yana jin lokacin da ta zare sakata, amma ba'kin ciki ya hana shi tashi, ya jima yana addu'ar samun sau'kin zuciya kafin ya samu sassauci. ya shiga gidan kai tsaye dakinsa ya shiga, ya yi wanka, ya fito ya shiga kicin, ya hadawa kansa Abu mai sauki, ya koma dakinsa ya rufe, yini guda bai fita ba, domin ramuwar barcin da bai samu ya yi ba.
Itakuma tana zaune cikin shirin ko ta kwana, har sun yi waya da Halima ta fada mata abin da ta yi masa jiya, tace mata da kyau, gobe idan ya sake har gate din za ki rufe.
Sai azahar ya tashi, ya fito da shirin fita masallaci, Jawad ya biyo shi, ya ri'ke hannun sa, suka tafi bayan ya masa alwala, suna dawowa, Jawad ya dinga Jan hannunsa, Yana cewa" Mami falo". Ya daka masa tsawa ya shige dakinsa ya daga murya yace "je ka wurinta kai, domin ita da babu duk daya ne a gurina" Jawad ya fashe da kuka saboda tsawar da bai saba da ita ba.
Abin ya yiwa Sa'adah ciwo, a fili tace "Allah yasa yau ka sake yin dare, zaka san Ni da babu daya muke".
Tsawon kwanaki biyu, zaman nasu ya sake yin tsami, domin shima fishi ya dauka sosai, ya dauke sabuwar wayar da ta bar masa a gurin, sannan ya karbe wadda take amfani da ita.
Lamarin da yasa rikicin ya sake ta'azzara a tsakanin su.
Ta dayan bangaren kuma sai shirin tafiya Abuja yake yi, saboda za su yi wata jarrabawar scholarship da gwamnatin tarayya zata tura malaman jami'oi karo ilimi a kasashen Birtaniya, Canada da kuma Rasha.
Bai fada mata zai yi tafiya ba, har sai da ya kammala shirinsa, da zai tafi, ya tsaya daga bakin kofar falon yace " Zan yi tafiya, sai Allah ya dawo da Ni, ya bawa Jawad dubu uku yace "kai mata".
Mamaki yasa ta kasa bude baki ta yi magana, ya juya ya tafi, Jawad na kukan zai bishi.
A tunanin ta kwana daya zai yi ko biyu, amma sai da ya shafe kwanaki biyar ba shi ba alamun sa, a kwana na shida ne, idonta ya fara raina fata, mussaman da ta tabbatar da Mahmoud suka yi tafiyar, Amma shi ya dawo kwana biyu kawai ya yi.
Kuka ta dinga yi, tamkar shine mafita, ga rashin waya dake addabar ta, ga rashin sa.
Sai da yayi sati guda ya dawo, kallo daya ya mata yasan ta ji jiki, sakonsa ya daketa sosai, amma saboda Halinta na taurin rai, ko kallo bai isheta ba.
Washagari da ya fita, sai da ya kai 11pm kafin ya dawo, domin ya jarrabata ya gani. A bangaren ta tana son rufe masa gida amma ta kasa, kwanakin da ya yi baya gida, sune mafi tsauri a dukkan rayuwar ta, tunda suka yi aure bai ta'ba yin tafiyar da ya kwana ba tare da ita ba. tasan rufe masa gidan da ta yi ne, yasa yayi tafiya mai tsayi ba tare da ita ba, ba magana mai dadi, ko na zai yi missing dinta.
Ya dawo ya tarar da gida a bude, ya yi murmushi, yauma 'dakinsa ya zarce, wannan abin ya dameta, amma bata ji zata bashi ha'kuri ba, tunda ai ita ya zalunta.
Washagari yana shirin fita, ta fito ta tsaya a tsakar gida, sai da ya fito sannan tace " Ina son zanje gida".
Ba tare da ya kalleta ba, yace " Ba za ki je ba".
Ya sa kai zai fita, taja tsakin da yasa shi juyowa da sauri, kafin yayi magana tace "dama idan mutum na cin amanar matarsa, sai ya yi ta boyeta a cikin gida, mai za'a yi da auren likitan mata, da mai koyarwa a Jami'a, aiki ne na yan iskan maza, masu juyawa matansu baya idan sun sami biyan bu'katar su"
Ya zuba mata ido yana jin wani iri Abu mai kama da tsanar ta na son yiwa zuciyar sa dirar mikiya.
Ya nuna kansa da yatsansa, yace "Ni ki ka zaga?"
Idonsa ya kada ya yi jawur, ya rasa inda zaisa ransa ya sami sau'kin zafin da zuciyar sa ke yi.
Ya girgiza kai yace " Na gode, amma U will pay for it Sa'adatu".ya juya ya fice da sauri.
Ganin yanayinsa yasa ta jin nadama na dan shigarta mussaman yadda ya nuna kansa yana tambayar shi ta zaga? tasan bai taba zaton zata iya zaginsa ba, ita kuma ba'kin cikinsa ne yake neman kashe ta a tsaye, sannan ma a ina ta zage shi?
Fishi ya dauka sosai, sun kai sati a haka, abin ya fara fin 'karfin ta, rama take yi a tsaye, ko uffan baya cemata, Idan yana gida Jawad na manne da shi yana bashi labarin yaci abu kaza da iri kaza, ko yace su Anty Safina sun kawo masa abu kaza.
Hankalin ta bai tashi sosai ba, sai da yayi shopping, taga iya abin da ya zama dole ya siyo, wadda ya saba siya na kyautatawa duk bai siyo ba, duk wani tarkacen kayan kwa'dayi babu a siyayyar nan, hatta kayan miya da yake zuwa janguza ya lodo musu, wannan karan ko guda daya bai siyo ba.