Sashe 74
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonta kawai ya ke da tsananin mamaki, can ya nisa ya ce " Ashe kaifin harshen ki yana nan, ashe rashin arzikin ki na nan fal a zuciyar ki? No wonder na kasa yarda da gaske kin canja, yanzu na tabbatar da na mayar da ke din ma kina wartsakewa zaki 'dora da dibar albarkar da kika saba".
Yana rufe baki ta ce "Ni Iyah Basiru Ado Gogel idan ka mayar da ni ban yafe maka ba, ko da gwal aka yi ka na barka, ai da tun farko nasan kallon fasi'ka kake mini, da ka yi tsararo na bika, wallahi Mukhtar ko zaman mota bana fatan ya sake hadamu balle zaman aure! Idan har ni diyar Malam Basiru da Malama Salamatu ce na barka. Koda kai ne autan maza, idan kuma ban aikiata abin da ka jefe ni da shi ba, to na yafe maka, idan kuma na aikata ubangiji ya bayyana ni, na kunyata na kuma tozarta a idon duniya".
Ta juya ta tafi sai da taje ba'kin kofar barin falon ta juyo, suka hada ido tunda kallonta kawai yake yi, ta ce "ka manta ka sanni domin kuwa daga yau nima na rufe shafinka, sannan hidimar da kake yi da ni ta makaranta ka dakatar bana so, ban bu'katar komai daga gareka, idan kuma har na ji alert din kudi zan mayar wa da Mahmoud, turowar kuma na nufin in sha Allah baza ka rabu da Hajiya lafiya ba".
Ta juya da saurin gaske ta fita, ta bar shi a tsaye cikin mugun mamakin kalaman da ta jefa masa, mafi tayar da hankalin a ciki shine alakanta Jawad da datti, ko makaho ya shafa ya san Jawad jininsa ne, domin komai na jikin Jawad nasa ne, hatta tawadar Allah da Mk yake da ita akan lebansa Jawad na da ita.
Bugu da kari da ta masa fatan mugun alkaba'i na rashin gamawa da duniya lafiya, to ai mahaifiyar ka itace duniyar ka.
Da kyar ya ja kafarsa ya isa kan kujera ya fadi yaraf yana jin tamkar kansa ba a jikinsa yake ba tsabar nauyin da ya masa.
Zuciyarsa ta kuntata sosai, gumi ya dinga karyo masa, fargabar auren da zai yi gobe ta sake nunkuwa, fishin da ya gani a tare da Sa'adah ya sake kassara shi, Anya haka kawai Sa'a ta bar shi kuwa, wanne irin so yake mata haka? Ya dinga tambayar kansa, a cikin wannan yanayin 'Karfi ya dawo ya tarar da shi.
Cike da tausayawa ya ce "Bichi ka dawo da Sa'a itace matsalar ka, Ina jin fargaba kar hawan jininka ya sababa maka ciwon zuciya".
A shake sosai Mk ya ce "Dan Allah 'Karfi ya zanyi ne, ban son auren nan da zan yi, ka taimake ni ka 'boye Ni".
Ido kawai 'KARRFI ya zuba masa amma zuciyarsa sai harbawa take fiye da 'kima saboda yadda maganar Mk take nuni da rashin nutsuwar da mai yin ta yake ciki. Amma ya san ganin Sa'adatu ne ya gigitashi haka, da kansa Mahmoud ya dinga jinjinawa kansa, ya tabbatar Mk na mutuwar son Sa'a amma ya tabbatar bai fi shi sonta ba, kawai girman aminci ke hakurkurtar da shi, sau tari zuciyarsa da tunaninsa na fa'da masa ba haramun bane, ya gwada Sa'arsa kawai, amma da ya tuna girman Mk da tarin sadaukarwar da ya masa a baya, sai ya ji a ransa ana barin halak dan kunya!
A fili Mahmoud ya ce " Ashe dai ni jarumi ne na gaske, Allah ka samu a cikin masu yin soyayya da abota saboda Kai".
Mk da yake fama da zafin da Sa'a ta hada masa, bai fahimci 'Karfi ba bare ya nemi fashin ba'ki kan kalamansa.
Hannuwan Mk ya ru'ko ya ce "ka yi hakuri nasan yadda kake ji, auren Nan na cikin kaddarar ka, ka karbe shi da zuciya daya, ubangiji zai buda maka kirjinka in sha Allah! Fatana dai ka dawo da Ummu Jawad, ka sau'ka'ka muku wannan dambarwar tura ta fara kaiwa bango, bana son a kai matakin da zata janye nadamarta tunda ka ki bata damar da zata gyara kuskuren ta, wallahi yarinyar nan ta gane kurenta, komin sharrin zuciya da mahassadi ansan dai ta nutsu ta fahimci rayuwa yanzu".
Ido jawur Mk ya ce "mumunar karyace baka ga Tijarar da ta mini ba yanzu, sosai ta wulakanta ni tare da yi mini mugun fata, ashe so yana zama tsiya?"
Mahmoud ya fahimci Mk yana cikin tension sosai sai ya kyale shi, ya rasa gane wannan masifar ta Mk, Yana son abu yana cutar kansa, yana cutar Yar mutane, haushin yadda Mk yake wulakanta Iyah yana neman samun muhalli a zuciyarsa.
****
Ikon Allah kawai ya kaita gida lafiya, domin daga gidan Mahmoud ba tasan ya aka yi ta isa titi ba. Haka nan tunda ta hau abin hawa, bata sake sanin inda take ba, sai da Mai adaidaita ya ce "Malama mun iso fa, ta daga kai ta ganta jikin shagon da suke kwatance da shi, a sukwane ta fice yana ta Kiran ta tsaya ta karbi canjinta amma ina, ba ta tsaya din ba, ta dai samu sukunin daga masa hannu alamun ta bar masa.
Tamkar an jefota haka Inna ta ganta ta fa'do, ta shige dakinta ta kwanta ta dinga gunjin kuka mai dafa zuciyar Dan Adam, kuka take yi na kaicon yadda rayuwa bata zuwa mata a yadda ta zace ta, kuka take yi akan kalaman Mk da suke nuni karara kallon mai cin amanar aure yake mata, wanne irin zalunci ne wannan?
A hanzarce Inna ta bita dakin ya zauna kusa da ita, ta dauki kanta ta dora a cinyarta, a tausashe ta ce "Iyah ki daina bibiyar Muutar, ba zai mayar da ke ba, ki fita harkar sa idan ba kina son ni na fita a harkar ki bane, ki fuskanci rayuwar ki, ki bawa wasu dama kafin ya dawo kasar kema ki yi aurenki".
Kuka kawai Sa'a ta ke yi na fitar hankali har da shidewa, sosai hankalin Inna ya tashi mussaman da taga yadda lebunan bakin yarta suka kubura tabbacin an musu dukan zalunci.
Kwalla ta cika idonta ta ce Muutar ne ya dake ki haka? Me kika mayar da kanki ne Iyah? To saurare ni da kyau, kinsan daukan kafafuwan da kike yi kina binsa ba komai bane face Ballagazanci, duk shashancin namiji kuwa bai son Ballagazar mace! Wallahi ba zai saurare ki a cikin wannan halin ba, ki fita a harkar sa, ki manta da shi, ki tattara shi ki watsar, ba shi kadai bane namijin kirki ba, Ina tabbatar miki Sa'adatu akwai wadda suke son ki kwatankwacin son da Muutar ya miki, ki kwantar da hankalin ki, zaki Sha mamaki".
Idonta dauke da hawaye ta kalli Inna da mamakin jin ta ambaci zahirin sunanta, Bata taba jin ta fa'di hakan ba, saboda riko da al'adar ba a fadar sunan uwar miji.
"So nake na manta shi Inna, amma na kasa! fada min me zanyi na huta da azabar da nake ji ta rashin sa"
Ta fa'da cikin rushewa da kuka sosai.
"Ki ji a ranki yanzu ba kece a gabansa ba, da yana sonki, da ya hadaku ku biyu ya aura, hakan ma wani nau'i ne na ladabtarwa tunda komai nasa zai raba muku biyu ne maimakon da, da bashi da komai a gabansa sai ke da 'dan ki, na sani ke kika jawowa kanki komai ya miki, amma ai ya ladabtar da ke, sannan kin yi nadama kin sauke girman Kai kin bada ha'kuri, ya kamata ya yi ha'kuri shekaru hudu yana jan ki a kasa, yanzu kuma zai yi aure tabbacin ya riga da ya sallama ki".
Zuciyar Sa'adatu ta dinga budewa tana fahimtar maganganun mahaifiyar ta, tana gasgata dukkan kalmomin ta, matsanancin kishi da miyagun kalmomin da Mk ya jefata da su sun taimaka wurin narkar da zazzafar soyayya da take masa, sun dakusar da kulafacin ta na son sake zama da shi by fire by force.
Inna ta Kai hannun ta kan leben Sa'a tana jin wani bacin rai na taso mata fiye da kowanne lokaci, akan me zai dukar mata 'ya alhalin ya ce ba ya yi da ita, dan mugunta har ya ya nemi canja mata fasali, sai dai ya makaro domin tana da yakinin ko hakori ya cire mata, ta zama mai wawulo ba zata rasa wadda zasu sota ba, da yawa ma kuwa.
Da karfin zuciya ta ce "In sha Allah Inna na miki al'kawarin bazan sake bibiyarsa ba, ba zan sake rokon ya zauna da ni akan dole ba, ba zan sake masa kallon idan ba shi rayuwa ta bata da amfani ba, na jingine shi, ki taga ni da addu'a Allah ya taimake ni"
Ta fa'da hawaye na gangarowa, da sauri Inna ta ce "da ikon Allah idan kika yi haka ba zaki wofinta ba".
Har dare Mk na murdadawa da bacin ran mugun fatan da Sa'a ta masa, da kyar ya lallaba ya isa gidan su Farida adalilin kiran da mahaifin ta ya masa.
A katafaren mahaifin Farida Mk zaune kan lallausan karfet na alfarma, kamshi na mussaman da sanyin AC ya sake maida falon aljannar duniya, duk juyin da Alh Nasir ya yi da Mk ya hau kujera ya 'ki hawa, hakan ya sake karawa Mk kima a idon dattijon.
Cikin 'kankanin lokaci aka baibaye gaban Mukhtar da nu'ikan abinci da na sha kala kala.
Cikin hikima yake jan Mk da hira har ya zo kan maganar da za su tattauna.
"Ka saurare ni da kyau Mukhtar! Na baka auren Farida ba dan ka nuna sha'awar ka ba, sai dan yadda ka ke da matsayi a wurinta, sannan nima da na ganka na gane tabbas kai din mutumin kirki ne! Amma na yi wani kuskure guda daya, da tun farko ban fa'da maka cewa ita din bata da koshin lafiya sosai ba, duk da lalurar bata hanata komai, amma dai tana tashi akai akai sannan hakkin ka ne a fa'da maka tunda dawainiya mai yawa ce zata sake hawa kanka".