← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 113

Sashe 23

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai yi mamaki ba tunda a lokacin ba ta zama ruwan dare irin yanzu ba, ko iyayenta ma Sumayya ce ta sayo musu don ta ri'ka gaisawa da su tun da ita ba mazauniyar gari ba ce. Ita kuma ta gaje ta Inna.

Halima ta ce "Ba Inna na da waya ba?"

Shiru ta yi da alamun dai ba ta son ba da lambar ne, shi kuma sai ya ce "Yawwa 'kawarmu a taimaka a ba ni lambar Innarmu!"

Haka Halima ta bude wayarta ta karanto masa lambar Inna saboda ta ga alamun za su sami kudi a tare da mutumin.

Duk kokarinsa na son sai ya kai Sa'adah har kofar gidansu, amma hakan bai samu ba, saboda ta kafe akan idan aka gan ta cikin motar da ba a san mutumin ba, za ta fuskanci tashin hankali, wannan kalaman ya sake jin son ta sosai, ya san daga dukkan alamu da ga Babban gida ta fito ma'ana gidan tarbiyya.

Kan dole ya kai su gidan su Halima wanda ita ko dar ba ta ji ba, hakan ya sa yake ganin anya iyayen Sa'adah ba tufka suke wannan 'kawar tana musu warwarba? A dan haduwar nan tasu ya lura da kamewar Sa'adah, ya kuma gane rawar kan Halima, a ransa yana rayawa da zarar ya sami Sa'adah zai raba ta da wannan kawar da idan kawancesu ya ci gaba da wanzuwa, zai ta ba tarbiyar Sa'adatu.

Halima ta shige gida ta bar su, bai wani jima ba shi ma ya ce zai tafi don ya lura da Sa'adah kamar a tsorace take, kudi ya dauko har kimanin dubu talatin ya ba ta ya ce ta bawa kawarta goma a ciki. Ta tattaro dukkan kunya ta yaba a fuskarta tare da cewa, "Ka bar su ba zan karba ba!"

Shi kuma ya na ta fadin "Idan ba ki karba ba, ba zan ji dadi ba Sa'adatu."

Da kyar tasa hannu ta karba ta yi godiya bayan ya karbi address din gidansu, wanda kai tsaye address din gidansu Zainab Ma'aji ta bayar.

Jiki na rawa ta shige gidan su Halima ta tarar da ita a falo da kaninta suna kallo kasancewar mamansu tana wurin aikinta, haka suka shige dakinta, kudin ta ciro ta nuna mata suka hau ihun murna! Halima na cewa "Ai tunda na gan shi na san akwai rodina tare da shi sannan ba matsolo ba ne."

Dariya Sa'adah ta yi tare da cewa, "Kin ga kuwa takanas ya ba da naki sakon."

Dadi ya cika zuciyar Halima da ta ji yawan kudaden da ya ba ta, haka ta sake jan Sa'adah zuwa Country Mall wanda a lokacin aka bude shi, suka kashe kudin nan tas a wurin siyan kayan kwalliya, da takalmi da jaka. daga Country Mall suka rabu kowa ya yi gidansu, Sa'adah zuciyarta sai wasiwasi take yi mai za ta cewa Inna akan wadannan kayan?

Ta tabbatar uwarta ba sakaryar uwa ba ce! Duk wani motsinta akan idonta ne, wa za ta ce ya ba ta wadannan kayan? A ina ta zubar da nasihar da kullum take yi mata idan za ta fita na kar ta tsaya da saurayi a hanya, ko dazu kafin ta fita sai da ta jaddada mata duk mai son ta ya zo gidansu ya same ta, kar ta yarda a tsayar da ita a hanya.

Ta gama tunaninta kaf ba ta sami kalaman da zai shiga zuciyar mahaifiyarta, ta fahimce ta ba, don haka kai tsaye gidan su Zainab ta sauka, ta ba ta ajiyar kayan tare da ce mata khalil ne ya ba ta, ba ta son a gani a gida, don ta san idan ta fada wa Zainab gaskiyar magana sai ta iya zuwa ta fada wa Inna tunda ta tsani abotarsu da Halima, kullum sai tace mata, "Sa'adah ki kiyayi kawance da Halima Mu'az ba wayewarku daya ba, ba kuma irin tarbiyarku daya ba"

Da kyar Zainab ta karbi kayan bayan ta gama mata mitar ita a rayuwa ba ta son shiga shirgin rashin gaskiya, ban da rashin gaskiya ina ke ina sauraran wasu mazan tunda dai kin san namiji daya za ki aura! Kuma kin tsayar da wanda kika aminta da shi.

Sa'adah da yake mafita ta ke nema sai ta yi mukus ta kasa tanka wa Zainab tamkar ba ita ce mafadaciyar nan ba.

Tana isa gida ta tarar da Baffa ya dawo daga Gogel, ta yi farincikin dawowarsa amma a gefe takaicin yadda za a ci gaba da yin tuwo ba kakkautawa take yi.

A kwanakin da baya nan hilatar Inna ta ke yi ba sa yin tuwo amma yanzu kam ba hilar da za ta mata ta yarda, tunda tafi girmama ra'ayin Baffa fiye da komai, sannan kuma ba za ta bari ta yi nata girkin ba, ce mata ta ke yi nan ba gidanki ba ne, ki bari idan kin yi naki gidan sai ki yi yadda kike so.

Kallo daya Inna ta mata ta gano rashin gaskiya a tare da ita, ba ta mata magana ba, sai da ta gama da hidimar Baffa ya fita waje. Sannan ta iske ta a daki tana game a waya, ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta ta ce, "Iya na ga sauyi a tare da ke mai kike ciki ne da har ban cancanci na sani ba?"

Duk da yadda Sa'adah ta maze akan ita ba komai, bai gamsar da Innar ba, amma sai ta ce, shike nan Iyah! Ki sani tun kafin ki san kanki na san ki, tun kafin ki yi dabarar boye mini halin da ki ke ciki nake tattalin ki, don haka komai za ki yi, zan gane. Ki sani idan har mu ba mu san mai kika yi ba, Ubangiji ya sani! Shi ne kuma zai kama ki saboda ha'intar da kike kokarin yi Mana."

Ta fada tana kallon ta irin kallon nan mai tsanani.

Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai musamman kallon da uwar take mata mai kama da ban yarda da ke ba, sai ta ce,
"Ni fa Inna ban je ko ina ba."

"Iyah ai ban ce kin je wani gun ba amma fada mini ina kuka biya daga asibitin sannan bayan Zainab da wa ku ka hadu a tafiyar?"

"Yan makarantar mu ne kawai Inna"

"To wa ye kuma ya ce yana son Zainab?"

"Babu!"

Ta sake ri'ko hannun ta sosai sannan ta ce "Waye ya tsayar da Iyah?"

Kai tsaye ta ce "Kai Inna ni fa ban kula shi ba, wani mutum ne tsoho ne fa!"

"To tsohon ba namiji ba ne?"

Idan har nagari ne kuma kina son sa ai magana ta kare! Ba za mu miki dole ba, don haka ko waye ya tsayar da ke idan kin ga ya miki ki turo shi wurin mahaifinki, laifin da za ki mana shine ki yaudare mu, ki yi abin da kika san ba za ki iya yi akan idon mu ba, ina abin da ya ba ki?"

Dariya ta kwace wa Sa'a ta ce
" Ban karba ba Inna"

Ita ma Innar dariyar ta yi tare da cewa "Ban yarda ba Iyah! Na san ki da martaba kalmar nan ta ba kyau mayar da hannun kyauta baya, amma na san Iyah ba za ta boye mini duk wata kyauta da za ta samu ba.
Don ta san ba zan ki ta da alheri ba, sai dai na kiyaye ta daga fada wa hatsarin MAZAN YAU musamman da ba gidansu aka biyo ta ba."

Tana fadin haka sai ta mike ta fice ta bar Sa'adah da sanyin jiki da kunya iri-iri suna saukar mata a lokaci guda.
A ranta kuma fadi take, "Ko yara nawa ne irinta suka dace da samun tsayayyiyar uwa mai sa ido akan duk wani motsin 'ya'yanta?" A fili kuma ta furta "Madalla da uwa irin Inna!"

Tana Jin komai za ta yi In Sha Allah ba za ta tozarta tarbiyar da Inna ke yi a kanta ba gajiyawa ba, amma kuma ba ta jin, za ta ki karbar duk wata kyauta da za a mata kawai dai boyewa ne ba za ta sake yi ba. don haka da kanta ta fada wa Alhaji Mamman gaskiya cewa gidansu na gaba kadan da wancan da ta fada masa da farko, haka nan hatta Khalil ta ba shi damar zuwa, ta gaji da boye-boye tunda wanda take yi domin sa ba fin su son ta ya yi ba, ita ce dai tafi son sa.

Yawan wayar da Alhaji Mamman yake mata ba kakkautawa, sau tari ma gajiya take yi da amsa kiran nasa, ya sake sa ta raina kulawar MK, tunda dai yanzu ai ta gama karatun tunda ada uzurin kar ya raba mata hankali a karatu ya gabatar.
Amma har yau ya ki canjawa idan ya kira ta da safe ba zai kara kira ba sai da daddaare shi ma a ya dade su yi maganar mintina uku, sabanin Khalil da Alhaji Mamman sai su shafe fin awa akan waya suna neman saye zuciyarta tamkar ba kati suke sawa ba.

Tana yawan tambayar kanta shin Uncle MK soyayya ne bai iya ba, ko kuwa matsayinta ne a zuciyarsa bai kai ya mata yadda su Khalil ke mata ba?

Zuwan ma bai canja ba sau daya a sati, duk da kullum sai ya zo unguwar, sannan ba ya mata kyautar bajinta kololuwar kyautar sa dubu biyu, sai dai karshen wata ya kan hado mata shopping din kayan kwalliya masu matsakaicin kudi da tarkacen alawowi masu dadi da biscuit, wanda ba sa dadata da kasa saboda yadda Alhaji Mamman da khalil mai sato kudin iyayensa suke mata barin kudi.

Wani zuwa da Alhaji Mamman ya yi ya fa'da mata matansa biyu, da yara bakwai, bai boye mata shi dan majalisar jaha ba ne mai wakiltar karamar hukumar Gezawa, uwargidansa na can Gezawa yayin da amarya ke nan cikin Kano a kwatas din 'Yan Majalisu na Farawa.

Da daddare Sa'adah na kwance a daki tana hira da Khalil, cike da nishadi take amsa wayar don kuwa tabbas tana jin son Khalil, kawai sanin ba za a masa aure yanzu da kuma soyayyar MK da ta danne tasa ne! Amma tana son sa yana burge ta ya dace da tsarinta na Luxury Life.
Chapter 23 · 0% Book details