Sashe 93
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce "A a Sa'adah kin so ki yi rikici ne kawai, yaushe zaki dake shi da wannan uwar wayar da alamun ta suka nuna ta A.c ce. Zo ki ga yadda za'ayi".
Bata san ya akayi ba, shauki ya kwashe ta, ta isa kusa da su, domin ganin da ta yi Jawad na rungume da shi, sai ta ji tamkar ta tabbata tana ganin su a haka, sune cikon farin cikin ta, ta yarda.
Mk ya rungume Jawad sosai ya ce "Dan yi masa dundu amma ba wadda ya zarta 'kwarin 'kashinsa ba, duka duka ma yaushe kika haifo mana shine?"
Ai kuwa kamar sokuwa ta yar da bulalar ta yi masa dundu har uku, za ta yi na hudu ya ce " oh sorry ya isa haka nan, ni ma zan yi masa fa'da ai".
Ta koma gefe tana harara tamkar idon zai fa'do.
Mk ya saki Jawad da suka kankame juna tamkar zasu zama halitta guda, ya ce " shiga ciki muna zuwa".
Ai kuwa ya tafi da gudu ya na dariya. Abin da ya sake kular da Sa'adah.
Ya kalleta ya ce "wannan ka'dai ya isa ki gane shima yana dandanar azabar da nake sha idan na ganki da wani".
Ta tabe baki ta ce "Allah ya bawa wadanda aka 'ki su, ake zaune da makiyansu ha'kuri".
Ya kasa cewa komai.
Ya saki maganar da cewa "ina son azo nema mini auren ki, jiya Baffa ya ce mini wai Gogel za'a je domin Yayansa dan wan Babansa ya ce wannan karon can za'a je".
Ta murmusa sosai ta ce "Ashe duk wasa ka dauki maganata? Wallahi bana fatan zaman aure ya sake hadamu, na riga da na yarda kaddarar haihuwar Jawad da kanwarsa ya sanya na yi muku kutse cikin soyayyarka da Yar mutanen Yemen".
A sanyaye Mk ya ce"Amma ai na sha fa'da miki sunan kanwar Jawad Aisha ko? Tunda ta zo da ranta, ko bata zo da rai ba matu'kar yaro ya yi motsi a ciki to a sanya musu suna saboda zasu tashi da sunan su ranar Gobe, dan haka sunan Hajiya Babba ta ci, Nana Aisha ce ina fatan ta zame mana sanadin shiga aljannah babu Hisabi".
Sa'a ta amsa da Amin a zuciyar ta.
Ya nisa ya ce "ke yanzu da gaske kike yi ba kya so na?"
Yana rufe baki ta ce "Wallahi ina sonka Mukhtar! amma bana sonka da aure, ina neman tsari da kaddarar da zata sake hadamu. Ka sani sarai, ina da kishi, idan na dawo ma ba abin da zan tarar sai bacin rai, na ro'ke ka mu rufe wannan maganar tun da sauran mutunci a tsakanin mu".
Ya matsa sosai kusa da ita murya a dakushe ya ce "Na miki tanadin farin ciki marar yankewa, kin sani Ina son ki, son da ya zarce kwatance, kin sani har zuciyarki ban zalunce ki ba, ke ce kika musguna mini, amma ina tabbatar miki Sa'adah zan sake ninka miki soyayya akan wadda na miki ta baya, zan sake tausaya miki, zan kuma yi iyakacin kokarina ban yi abin da zai yawaita motsa miki kishi ba, na dade ina roka miki sau'kin kishi a wurin ubangijin da yake sarrafa zuciya. Ko baki dawo dan ni ba, ki dawo dan Jawad, ki dawo ko ubangiji zai azurta mu, da sama masa yan'uwa".
Jikinta ya yi sanyi sosai da kalamansa, wadanda ta tabbatar babu yaudara ko da'din baki a cikin su.
Amma sai ta waske da cewa "Ina yiwa Jawad fatan samun yan'uwa ta bangaren Farida. Domin kuwa ni dai ba da kai zan samar masa ba".
Wani irin abu ya soki Mk tunda ga kan kansa har kan yantsunsa .
Ya dinga jin kansa na yi masa nauyi, ganinsa ya koma dususu, jiri ya fara katantanwa da shi.
Cikin hikimar ubangiji sai kawai ya zauna dabas angurin, farin yadinsa na tissue original din, ya debi 'kura da ciyayi amma baima sani ba.
Yana zaune sai zufa ke karyo masa, take kuma hakoransa suka dinga kadawa tabbacin zazzabi ya kawo gudunmawa a tashin hankalin da yake ciki.
Da kyar ya ciro wayarsa ya mika mata ya ce "Taimaka ki lalubo mini Abbas".
Jikinta a matu'kar sanyaye har bari take yi saboda halin da yau ta ga Mk a ciki ya matu'kar kidima ta.
Bugu daya Abbas ya dauka. Cikin karfin hali Mk ya ce taimake ni ka zo ka dauke ni, ina nan gandu gidan nan na layin Madugu, ba zan iya tuki bane".
Ya kashe wayar ya kalleta idonsa ya ka'da sosai ya ce "kin manta duk rayuwar da kika yi ta jin da'di a hannuna, kin manta alheri na, kin manta duk kalolin soyayyar da nake gwada miki, kin dora kuskurena akan dukkan wadannan abubuawan".
Ta kasa magana, ya sake kallon ta soasai fuskarsa duk gumi tamkar ya yi alwala ya ce "ki manta dukkan dadin da nake raba dare ina jiyar da ke, kin ri'ke sharri na guda daya. Har yau din nan ban ji a jikina na zalunce ki ba, na san dai babban laifi na auren da na yi ne, aure kuwa ko muna tare idan bu'katar yinsa ta zo ba zaluntarki na yi ba. Amma duk da hakan na yi ta baki ha'kuri, na fada miki kaddara ta ce auren nan da na yi. Amma ubangiji shine shaidata akan ba abin da ya ragu na daga son da nake miki, bana jin kuma a cikin wannan duniyar akwai abin da zan so ya zarta ki".
Ya nisa ya ce "Amma duk kin yi fatali da komai, kin dage sai kin yi ramuwar gayya. Abin da baki sani ba, shine ba ni da karfin guiwar juriya akan kishin ki, amma tunda kin dage shikenan, kawai ina jiye miki fargar jaji ne, ina jiye miki ki maida 'danki maraya. Shiga gida na gode sosai".
Ya yi shiru, zufa na sake karyo masa ta ko ina.
Kafin ta yi magana Abbas ya iso a adaidaita sahu.
Ya gaisheta, tare da tambayar ahalin gidansu.
Mk ya mika masa hannu, shikuma ya mikar da shi.
Suka doshi mota ba tare da Mk ya sake cewa komai ba.
Abbas ya dinga jin tausayin wadannan masoya, a ransa ya dinga musu addu'ar samun daidaito ko hankalinsu ya kwanta.
Kwanan Mk biyu a kwance Farida na jinyarsa domin a wnanan karon har ruwa aka kara masa, a gida.
Mahmoud ya damu sosai ya sake komawa wurin Sa'a Amma ta kafe ita fa ta riga ta ha'kura da Mk.
Haka da Baffa ya tambayeta ta ce ita kam bata sonsa, abin ya farantawa Inna rai, ba irin kabalin da Baffa bai yi ba ta ce ita kam ta riga da ta shafe babinsa. Lamarin da ya farantawa Inna rai ba ka'dan ba.
Da ta ga da gaske Baffa zai mata fin karfi ta shirya suka tafi Gogel ita da Sumayya, ta kai korafi wurin Yayan Baffah da ya ce a Gogel din za'a daura aurenta wannan karon.
Baffah bai san da gaske Iyah take ba, sai da ya ji kokenta akan a roke shi ya barta ta auri wadda zata nutsu da shi.
Ya dawo gida a sanyaye, ya tarar da su duk suna gidan har Sumayya.
Ya zauna a cikinsu, suka gaisa.
Ya kasa daurewa ya ce " Iyah na ji sakon ki, na san wannan hukuncin da kika yanke a iya fatar bakin ki ne, amma tunda kin yarda da shawarwarin makusantan ki, kin tauyewa zuciyar ki, da 'danki fari ciki shikenan. Ai dama ke ce kike da hakkin zabawa kanki miji domin kin girma hankali ya ratsa ki".
Ya daga kai sama ya ce "Allah ka zame mini shaida, na yi iyakacin kokarina, na mikata inda zata sami nutsuwa amma basu fahimce ni ba, Allah ka sani ban yi fishi ba, Ina dai roka mata sassauci kar abarta da zabinta, a bata mafi alheri."
Ya sauake idonsa a akanta da duk jikinta ya mutu, kunyar 'karar da ta kai shi na kamata, ba ita kadai ba har Sumayya, Innace kawai take kan ba'kanta gara da suka yi hakan.
Ya nisa ya ce" ki cewa wadda kuka aminta da shi, ya tura iyayensa Gogel wajen Babanku Ayuba, ni ba sai sun zo mini ba".
Ya mike ya barsu da sanyin jiki.
Yana fita kuwa, ya kira Mahmoud ya zo ya same shi.
Ya kalli'Karfi ya ce "Mahmouda Ina ba'kin cikin sanar da kai cewa duk yadda nake ganin Zan shawo kan Iyah akan al'amarin ta da Mutari abin ya ci tura, na rasa inda zansa kaina kunyar yaron nake ji. Yau din nan sun je can gida sun fa'dawa Yayana Akan na matsa sai ta auri Wanda ba shi take so ba, na samu umarnin akan lalle na barta ta tura musu iyayen wanda take so".
Takaici ya kama Baffa ya kasa cigabada maganarsa.
Sai ya nisa ya ce "Bazan iya fa'dawa Mutari wannan maganar ba, domin ya riga da ya gamsu na isa da ita, to gashi sun hade min kai, sun nuna mini *HALIN YAU* na rashin girmama ra'ayin magabata. Dan haka ka fa'da masa ya yi hakuri dan Allah, yau ma zan sake maimatawa da ina da wata yarinyar da na bashi, in fatan ubangiji ya albarkaci Jawad da ya ratsa a tsakanin mu".
Jikin 'Karfi ya mutu kwarai da gaske! Kenan biyu babu zasu yi? Mk ka'dai zai iya sadaukarwa da Sa'adah, amma matu'kar ba Mk ba kuwa zai shiga ya fafata da kowanne mahalu'ki dan ya tabbatar ya hana shi daukarta, a yanzun ma abin da zuciyarsa take kissima masa kenan indai yana raye bai kamata ya bari ta subucewa Mk din ba.
Ya riga da ya hakura da ita, badan ya daina sonta ba, sai dan ya san ubangiji ya dubi girman hakurinsa ya bashi mace ta gari, matar da ako ina zai bugi kirji ya ce ta gari ce, matar da take sonsa da dukkan zuciyarta, take mutuntunta shi, take hakuri da dukkan matsalolinsa, ya sani ba iyawarsa ba ce, horewar ubangiji ce.
Ya nisa ya ce "Baffah mu bamu sare ba, har sai ranar da muka ga an daura mata aure".