← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 113

Sashe 37

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kin budewa ta yi, sai Sumayya ce ta bude ta fito da su, daya a cikin wata yar roba yake mai kyau an rubuta Women's Formula.
"Kinga wannan na robar Multivitamin ne 100 pieces ne kullum daya za ki sha"
Sai wannan ta nuna na kwalin shi ba kullum ba sai ranar da kika so. Ki kula da shi mai tsada ne sosai, daurewa na yi na siyo miki package dinsa, kafin ya kare dai na san za'a dade sosai".

Ba tare da ta kalli fuskar Sumayya ba ta ce "Na gane, na gode." Ta mayar da su ledar. ganyin wata takarda a ciki yasa ta janyo ashe recit din kudin ne, ganin yawan kudin da maganin suka lashe musamman na kwalin ya matu'kar ba wa Sa'adah mamaki.
Ta fito dana kwalin tana dudduba mene ne special a tare da shi da ya yi wannan darajar haka?

"Viagra"

Ta furta sunansa a fili, a kunyace ta sake cewa "Na gode sosai Anty".
Sumayya ta muskuta ta tsare Sa'adah da kallo mai tsanani sannan ta ce "Ina rokon ki Iyah kar ki jefa kanki a hallakar da MATAN YAU suka jefa kansu na shaye-shayen magunguna barkatai marasa fa'ida da inganci, da sunan mallakar miji. Kar ki yarda da wannan bankaurar wallahi ba a mallakar miji da wannan sai dai ki ta asarar kudaden ki, karshe ki hadu da ciwon da zai raba ki da mijin gaba'daya".

Cike da wauta Sa'adah ta ce "Fada mini abin da zan yi na mallake shi kamar yadda kika mallaki mijinki".

Dariya sosai Sumayya ta dinga yi har da kwanciya akan gado, lamarin da ya fusata Sa'adah, kawai sai ta fashe da kuka, da kyar Sumayya ta hadiye dariyar ta shiga rarrashinta.

"Yanzu mene ne abin kuka Iyah?"

"To akan me za ki mini dariya kamar mahaukaciya?".

"Tambayar ki ce ta ba ni dariya, amma nutsu ki ji mai zance miki. Mace tana kama mijinta da girki mai da'di, da kuma ba shi kulawa ta musamman a shimfida, da kuma tsaftar jiki da ta muhalli. Amma wadannan kadai, ba zai sa ta mallake shi ba, sai ta yi ha'kuri ta bi ra'ayin sa akan komai, ko da kuwa ita ba hakan take so ba, ya zama ba ta da ra'ayin kanta sai na mijinta, ta iya ladabi da biyayya, ta kiyaye harshenta akansa. Ina tabbatar miki idan kika hada wadannan abubuwan sai kin mallake shi fiye da yadda kike so".

Tura baki gaba ta yi tana goge hawayen idonta, ta sake cewa "To idan ina son ya zama mijin ta ce fa?"

Mamaki da tsoro ya kama Sumayya, wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar auren jiya, ita ce ke son ta mallake miji, bayan mallakar kuma ta mayar da shi mijin ta ce. Wane irin son zuciya ne ya shigo wa matan wannan zamanin haka?

Sumayya tsintar kanta ta yi da ri'ko hannun kanwarta ta kalle ta da tarin kauna sannan ta ce, "Abubuwan da na fada su ne za su miki jagora akan komai, sai kuma ki hada da addu'ar Allah ya zaunar da ku lafiya cikin aminci da tausayi. Amma karki yarda da kawayen da za su ba ki maganin mata ko a saki a hanyar zuwa wurin malamai wallahi ba za ki samu yadda kike so ba, ba komai a wannan hanyar sai bata da lalacewa".

Ta dan tsahirta kafin ta zarce da fadin "Ki ba shi dama ya zama sarki a gidansa, ke kuma ki zama baiwa kuma bafadiyarsa, duk abin da kika san yana so, ki masa tun kafin ya bu'kata haka nan ki guji abin da baya so kafin ya ankarar da ke, ina tabbatar miki idan kin yin hakan bayan mallakar da za ki masa zai ya zame miki mijin kan ta ce ma, matu'kar yana rayuwa kan tsarin ilimi da shari'a ne.
Ga turaren wuta nan Inna ta ce a kawo miki sai dazu suka iso, ni ma na diba na ga masu kyau ne, har da na tsugunno".

Ta mike tana fadin, "Kin ga an dade da idar da sallah bari mu tafi".

Da za su tafi rungume juna suka yi kuka kowacce ta ke yi tamkar ba za su sake haduwa ba. A dole suka rabu Sumayya na mata fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka.

Ba su jima da tafiya ba ta zuba gawayi a kasko ta zuba kalanzir tare da kyasta ashana, ta barshi a tsakar gida, ta share falon inda su Khalifa suka bata. Sannan ta shiga wanka, sai da ta yi sallar Isha, sannan ta duba ta ga wutar ta kama, ta dauko ta zuba turaren. Kan ka ce kwabo gida ya cika da kamshi, sai kallon agogo take yi,har tara na shirin yi bai dawo ba.

Daidai lokacin ya dawo, waya ya kira, ta fita ta bude masa, kamar dazu ba mayafi a tare da ita.

Suna tafe yana fadin "idan za ki fito ki dinga saka hijab, ban son wani ya hango ki a haka".

Ta amsa da tom.

Tunda ga tsakar gida yake jin daddadan kamshi, suna shiga falon ya rikota yana cewa "Madalla da Antyn mu, irin wannan kamshi haka".

Ita dai ba ta ce komai ba, sai da suka zauna ta ce "Sannu da dawowa" Ya amsa mata cike da walwala.

"Shi ne ka tafi ka bar ni ni kadai har tsoro ya fara kamani".

Ta fada cike da shagwaba.

"Ai kuwa dai gara ki cire tsoro, kin san har sha dayan dare ina kaiwa a shago".

Murmushi ta yi kawai ba ta ce komai ba, amma a zuciyarta tana raya ba za ta yarda da wannan dogon zaman a waje ba, tana gida ita kadai.

Haka suka ci gaba da cin amarci ba kakkautawa cike da soyayya da kulawa, tun Sa'adah na jin zafi da tsoron haduwarsu har ta saba ta fara fahimtar dadi da nutsuwar dake cikin haduwar.

```Alkalamin
*Surayya Dee*.
``✍🏼✍🏼

[6/5, 14:08] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*Fatan alheri ga Amare*
*Hafsa Sani Abubakar*
*Halima Sani Abubakar*
_Ubangiji ya albarkaci auren ku, ya Baku zuri'a mai albarka_.

53-54.

*BAYAN SATI SHIDA*

Zuwa wannan lokacin, sabo da shakuwa mai karfi sun shiga tsakanin ma'auratan biyu, soyayya da aminci sun sami wajen zama a gidansu, kowa kokarin kyautatawa dan uwansa yake yi.

MK ya dauki soyayyar duniya ya dora akan Sa'adah da da hali kirjinsa zai bude ya cusa ta, saboda yadda ya ke jin ta a zuciyarsa, musamman yadda ba ta gajiya da bukatunsa. Duk da dai ya gane ita ma mabukaciyar ce ta gaske ga tsafta ga iya sarrafa girkin gargajiya, saboda ire-iren su aka fi yi a gidansu.

Babban abin da ya ke gigita shi a kanta, shagwaba da iya kwalliya, kullum sabuwa take zama a idonsa, kullum da sabon abin da zai gani a tare da ita, babban abin birgewa ta kama dukkan ahalinsa ta ri'ke da hannu biyu, ta zama yar gida a gidansu, akai-akai take kiran Hajiya Babba da Hajiyar Bichi tana gaishe su. Sun zo sau daya sun ga gida, da amarya.

Tana kokari sosai wurin yin abinci akai gidan su Mk mussaman masar Bauchi da miyar ganye, da kuma Dambu. Kasancewar mahaifiyar ta daga Bauchin take, sosai ta iya masar Bauchi.

Kullum yana gida, hatta FGC Kano ma ya daina zuwa, shago kuma sai Azahar yake fita, da zarar karfe biyar ta yi zai juyo ya bar su Abbas da kula da wurin, Mahmoud ya masa tsiya ya gaji.

Shi kansa Mahmoud din tunda ya je ya ci girkin amarya, dambun shinkafa ta yi musu da ferfesun naman rago, sai kunun aya bai sake yi wa MK tsiyar ya zama bita-zai-zai ba, musamman yadda kamshin turaren gafgaf da kajiji ya kama gidan gaba'daya, dole idan mutum ya yi katarin samun irin su Sa'adatu ya manne musu ya kasa fita ko ina.

A wannan tsukun ASUU ta janye yajin aikin da ta ke yi, a kuma lokacin aka tabbatar da MK da Mahmoud da sauran da suka yi sa'ar samun koyarwa a Jami'ar Bayero takarda shedar fara aiki.

Ranar da ya fara fita aikin dukkansu sun galaibaita, sati shida kullum suna manne da juna, ko fita ya yi Allah-Allah yake ya dawo. Don haka yanzu ma da zarar ya ga yana da tazarar lokaci, sai ya dawo gida ya ci abinci, ya yi abin da zai yi, sai kuma ya yi wanka ya koma, idan kuma ba shi da sauran darasi shike nan sai ya yi zamansa gurin amaryar sa.

Watannin su biyu da aure Sa'adah ta tsiri fushin da babu dalili, share shi take yi, ta daina hira da shi daga eh sai um um, ta rage walwala idan yana gidan, idan tana falo ya zauna, sai ta san yadda ta yi ta bar falon, haka nan daki.
Ba ta gudunsa, amma shi kadai zai yi kidansa yayi rawarsa, babu gudunmawa daga gare ta.

Wannan canjin ya matu'kar 'daga masa hankali ya yi tambayar duniya tace ba komai, kuma lafiyar ta 'kalau.

Rannan da daddare ya dawo da ga Masallaci, jikinsa a sanyaye ya zauna kusa da sallayar da ta ke sallah ya jira ta idar.
Tana ganinsa ta yi kamar ba ta gan shi ba ta fara kokarin tashi a gurin ya kira sunanta a kaurare.

"Sa'adah zauna magana za mu yi".

Ba ta 'ki ba, ta koma ta zauna amma fuskar nan a 'daure, sannan ta juyar da kanta gefe, ta ki kallon inda ya ke.

"Na tambaye ki mene ne yake faruwa kin ce mini ba komai amma kuma kin canja mini, kin tayar mini da hankali, wallahi da kinsan yadda nake ji a zuciyata da kin tausaya mini cikin kwanakin ukun nan.
Chapter 37 · 0% Book details