← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 113

Sashe 64

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta sake sa salati tana tafa hannu, tare da cewa "yanzu idon ku, idon tsohon nan ku iya fa'da masa kun mayar masa da 'ya Bazawara? kaico na taya ku jin kunya".

"Yanzu ku tashi ku kaini gurin Alh Isa".

Sai da Mahmoud ya taimakawa Mk sannan ya mike.
Fada sosai Mk ya sha a gurin Alh Isa, sai daga karshe ya sassauta ya ce " Ka yi kyan kai da ka yi saki 'daya tal, fatana ka janye ka mayar da matarka, kowa hakuri ya ke yi da abokin zamansa ,ta ci darajar mahaifinta".

Kan Mk na kasa baice komai ba sai da Baban ya kammala sannan cikin ladabi ya ce "A mini afuwa Baba, a yi hakuri, a sani cikin addu'a ina cikin ru'dani mai yawa, ina rantsuwa da ubangiji ina cikin ru'danin da nake jin inama ajalina ya riske ni a yau saboda tsananin asarar da nake jin na tafka, ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi 'karfina"

Dukkansu jikinsu ya yi sanyi mussaman yadda yake maganar cikin rawar murya tamkar ba Mukhtar ba, namiji mai karfin zuciya.

"Allah ya daidaita ya kawo mafita " cewar Alh Isa da ya rasa mai zaice, dan ya lura Mukhtar na cikin rashin nutsuwa da firgici, ya tabbatar kuma yana da gaskiya, sannan mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo.

Dukkansu suka amsa da "Ameen, ya yin da Hajiya ba haka ta so ba, so ta yi ya wula'kanta mata shi, ya kuma tirsasa masa ya mayar da matarsa ko ba ya so.

Har da Alh Isa suka 'dunguma zuwa gidan su Sa'a, Hajiya ce kawai ta ce ba zata je ba, bata san da idon da za ta kalle su ba.

A tsakar gidan Baffa ya jagorancin zaman, Alh Isa ne ya yi karfin halin bayyana mutuwar auren wadda ya matu'kar dukan zuciyar iyayen na Sa'adah, juyin duniya ba wadda ba'a yi musu ba, amma sun 'ki bayyana menene dalilin da ya haifar da wannan tashin hankalin, kukan da Sa'a ke yi tamkar za ta shi'de ya sake 'daga hankalinsu.

A hankali Mk ya ce "Baffa Ina rokon ka, kar yanke mini kauna, ka yafe mini, kaddarar muce ta zo da hakan, har wayewar garin YAU bamu san zamu tsinci kanmu a cikin wannan mawuyacin HALIN da muke ciki ba, ina kuma fatan itama ka yafe mata, ba laifinta bane Baffah".

Gurin ya yi tsit sai shshshekar kukanta kawai ake ji, Mahmoud ya kamu da ciwon tausayin masoyan biyu, mussaman Sa'a kallo daya za ka mata kasan tana cikin tsaka mai wuya.

Baffa ya nisa ya ce "Ba aurenta ne ya hadamu ba Mutari, ba kuma zai zama dalilin rabuwarmu ba, nasan halin girma irin naka, tsiyar a gunta take, yanzu kuma zata gane tsiyar har wasali gareta, domin na tabbatar laifin nata ne, ba zata 'ki zaman aure ta yi tunanin zata zauna a gabana ba".

Ga mamakin Mk sai ya ji kalaman Baffa sun sake girgiza masa zuciya.
Da sauri ya mi'ke ya koma kusa da shi ya ce "Baffa Dan Allah dan Annabi ka yi ha'kuri, idan ka yi haka bazan yafewa kaina ba, ka yiwa Allah ka barta ta ji da tashin hankalin da na jefata, ba laifin ta bane, nawa ne, Ni za ka hukunta ba ita ba".

Ido kawai Baffah ya zubawa Mk da yake gurfane a gabansa yana rokonsa idansa jawur, ga wata irin rama da ya yi ta farat daya.
A ransa fadi yake Iyah kin tafka asara, kubucewar miji irin Mutari abin ki shimfi'da tabarma azo a miki jaje ne.

Ya tabbatar laifin na Iyah ne, amma ya 'boye laifinta, ya kuma tsaya kai da fata wurin nema mata sassauci da aminci a gurinsu.

Baffa ya dafa kan Mk ya ce " Madallah da mutanan kirki irin ka, madallah da mutane masu irin dabi'ar ka, madallah da zuciya mai adalci irin ta ka! Saboda kai zan bar Iyah ta zauna a gidan nan, ban taba jin takaicin rashin ya'ya da yawa ba sai yau, da ace Ina da wata 'yar! da wallahi taron nan bazai watse ba sai na musanya maka da ita".

Kwalla ta 'kwacewa Mk ya na jin kunya da tausayin Baffa na sake masa rubdugu, wacce irin kauna ya ke masa haka, anya bai yi rashin kirki da ya kasa yin ha'kuri da 'yarsa ba?"

Ba zato suka ji Mk na cewa "Baffa me yasa ba zaka ba ni umarni na mayar da ita ba, sai ka yi fatan ka bani yar'uwarta idan hakan ya yiyu ka haramta mini ita gaba'daya fa?".

Ba ki 'daya jikinsu ya dan yi karfi saboda kalaman Mk, wadda suke bushara da zai iya daidaitawa da matarsa, yanzu ko anjima.

Inna ta ce "Tunda baka da wata da za ka bashi, ai sai ka mayar masa da wadda ka ke da itan".

Cikin kuka sosai Sa'adah ta ce " Na gode Innah".

*Surayya Dee*
✍️

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_

*Gaisuwa da fatan alheri ga wadannan groups din*
*LAFAZEE FANS*
*DANDALIN MUM KHADY*
*HAFSAT SODANGI fans*
*DAGA DAJI 1&2 fans*
*PAID GROUP na BINTA ABBALE*
*DANDALIN SADA ZUMUNTA NA ANNURI.*
*JIDDA REAL FANS*
*FADILA LAMIDO FANS*
*SADNAF NOVELS GROUP*
*TASKAR AISHA MICHIKA*
_*Dama sauran wadanda ban ambato ba, mu hadu a shafin gaba, Kuna da yawa Allah ya bar kauna_*.
*MK, SA'A DA FARIDA NA GAISUWA*

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

79_80.

"Ba zan ba ka umarnin da na san kunya da nauyi ne zaisa ka yi shi ba.
Ba ni na maka umarni ka auri Iyah ba, ku ka hada kanku, ka aureta bisa ra'din kanka, ka zauna da ita cikin shekaru bakwai, Ni da mahaifiyarta shaida ne akan kyakkawan rikon da ka mata, haka nan, ka na girmama mu da dukkan zuciyarka, kana jin nauyi na tun kafin na baka aurenta, idan har za ka iya sakin Iyah, to ni kuwa bazan yi son zuciya ba, na tabbatar abin ne ya fi 'karfin ka".

Ya nisa ya cigaba da cewa
"Zan so kwarai ace na mutu na barta a hannun ka, domin Ina da yakinin ba za ta wulakanta ba, amma ya na iya da HALIN 'dan YAU mai yin aiki da son zuciya, daga baya kuma ya jinginawa tsautsayi da 'kaddara".

Alh Isa ya muskuta ya ce "Tun kafin mu zo nan, na umarceka da ka janye, ka mini gardama, amma yanzu kana cewa ya baka umarni ka mayar da ita, Ni baka jin nauyi na Mukhtar?"

Kunya iri iri ta sake rufarwa tashin hankalin da Mk ya ke ciki, a sanyaye ya ce " A a Baba bayan nauyin ka da nake ji, wallahi kallon uban da ya isa ya zartar da hukunci akai na na ke maka! Abin da yasa ban amsa ba, ina jin tsoron kada na mayar da ita a yanzu auren ya lalace gaba daya, saboda zuciyoyin mu cike suke da bacin rai mai ya.."

Cikin dimaucewa Sa'adah ta
katse shi da cewa "Ni zuciyata ba komai sai salama da nadamaar *HALIN* da nake ciki, na yi al'kawari zan jure duk wani kalar fishinka, ba zan yi abun da za mu kai ga lalata auren mu ba".

Tausayinta ya ratsa su dukkan su, gurin ya dauki shiru, sai fama suke da tausayin su, kowa ya lura laifin Sa'adah ne, amma Mk ya kafe laifin sa ne, su gafarce shi, haka aka tashi ana addu'ar, Allah ya daidaita su.

Bayan tafiyar su Mk, kukan Sa'adah ya karu, sosai ta ke rusa kuka, yayin da iyayen ta suke fadin ba ki ma fara kuka ba, domin sai nan gaba za ki gane asarar da ki ka yi ba 'yar 'karama bace.

Zazzabi mai zafi ya rufe ta, hakoronta suka dinga karo da juna, jikinta sai rawa yake tamkar mazari.

Da farko shareta suka yi, sai da suka ga abin na sake 'kamari sannan Inna ta kai mata 'dauki, tana sa hannu a jikinta ta ji zafi zau.
Har dare tana cikin wannan yanayin, kan dole Baffa ya 'kira wani jami'in lafiya, mai chemist a unguwar ya zo ya bata taimakon gaggawa.

Haka al'amarin ya kasance da Mk, bayan sunje sun sauke Baba Isa, yace da Mahmoud gidan Hajiyar Bichi zai maida shi, suna shiga falon nata ya yanke jiki ya fadi, alma'arin da ya matu'kar tayar da hankalin su, 'Karfi ya fita a gigice, ya yi sa'a ya tarar da Abbas na gida, ya 'Kira shi suka ciccibi Mk zuwa wani asibiti mai zaman kansa mafi kusa, dole aka kwantar da shi sakamakon jininsa da ya yi mugun hawa, baya ga haka yana cikin damuwa da ya ke bukatar hutu..

Abbas ne ya zauna da shi, sauran yan'uwansu kullum suna zarya a asibitin, haka nan Mahmoud kullum sau biyu yake zuwa duba shi.
Har zuwa wannan lokacin Jawad na gidan 'Karfi bai san me yake faruwa ba, takanas Mahmoudya je ya debo masa uniform da kayansa kullum da safe zai kai shi, idan anta shi kuwa mai aikin matar ke hawa adaidaita ta dauko shi, idan ya tambayi Mamin shi ko Malam sai ace sun yi tafiya ne, bai damu ba, tun tafiyarsu Abuja ya saba zama gidan Mahmoud Karfi.

Kwanansa uku aka sallame shi, tare da gargadin ya rage damuwa, ya kuma kula da shan maganinsa.

Haka ya tattare dakin Hajiya, tun tana ki, har ta ha'kura ta barshi, kan dole ta koma kwana a babban falon su, da suke zama ayi dab dabla lokacin Hajiya Babba.

Kwanansa biyu a dakinta yana warware wa, a cikon na uku ne ganin ya dan sami sauki har ya ci abinci, yasa ta bijiro da maganar Sa'adah.

"Matu'kar kana son mu shirya to ka dawo da matarka, rashinta ne duk ya susuta ka haka, idan kuwa ka 'ki jin maganata kar kuma takowa inda na ke, ko gaisuwar ka bana so".
Chapter 64 · 0% Book details