← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 113

Sashe 10

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ta yi tana kuma godiya amma ta ci alwashin bashi ya ci, dole sai an baje maganar nan ai ya san tun farko ta zabe su tabar Alhaji Mamman din da dukkan abin da yake da shi.

Tun a mota yake 'kiran lambar MK amma bai dauka ba, har ya gaji ya mayar da wayarshi caji a jikin motar. Mintuna kusan ashirin har ya shiga layin gidansa yaji 'karan wayar shi, ganin sunan MK yasa shi dauka da sauri, tare da cewa, "Wai ina ka shiga ne?"

Daga can ya amsa mishi da cewa, "Wallahi ina tare da Farida ne ba zan so ka yi mini maganar Sa'adah a gabanta ba"

Shiru Dr Mahmoud ya yi yana jin shi kam bai san wani namiji da ke gudun 'bata wa matarshi da gangan irin MK ba, ya tuna lokaci da dama da yake zaunar dashi yana caccakar shi akan tsoron Sa'adah ya ke yi, ashe ba tsoro ba ne tunda ga Farida ma hakan ya ke mata.

Mutum ne mai martaba abin da yake so, ko wadda yake son sa, ya sake tuna ko a abotarsu, MK ke ha'kuri da shi, shi ke masa hidima ba tare da tunanin ai yasan yawan albashinsu 'daya ba, samun irin Mukhtar Kabir Bichi zai yi wuya a wannan lokacin.

Amma duk da hakan sai da ya tsokane shi da cewa, "Dadi na da kai mijin ta ce ne kai, ni ban san me ya sa kake jin tsoron mata ba, ai na 'dauka Sa'adah ce kawai dodon taka, ashe wa lnnan alankosar ma murza ka take yi".

Shi ma cikin 'kosawa da shakiyancin da ba ya gajiya da mishi ya ce, "Kai ai ba za ka gane karatun ba ne ni kadai na san mai suke jiyar da ni, ka ga kuwa ai dole na yi tattalin farincikinsu, kar ni ma a hana ni nawa farin cikin"

Dariya sosai 'Karfi yake yi yana cewa, "Ashe haka karatun yake ganewa ne ban yi ba? amma da dukkan alamu karatun naka na daban ne"

"Idan kagama iya shegen naka, ina sauraranka don waje na fito, idan kuma ba ka gama ba, to zan koma, ma hadu gobe"

'Karfi ya gintse dariyarsa hadi da cewa, "Kai MK wallahi da alama 'yar darun taka, ta shiryawa daru kala-kala, amma dai na san kishi ke 'dawainiya da ita, ka san tunda ka yi auren nan bata bude baki ta ce 'kala ba, yana ta cin ranta, na ga soyayyarka mai yawa a idanuwanta duk da bakinta na 'kirarin rashin son"

Shiru MK ya yi har Mahmoud ya yi tsammanin ko wayar ce ta katse. Amma da ya ce,
"Kana ji na kuwa?"

MK ya amsa da cewa
"Ina jin ka. Mamakin ta ne ya ke ta kama ni".

"Ai ba mamaki a lamarin mace." A cewar 'Karfi.

"Ka shirya gobe muje mu same ta, kada Hajiya ta tambaya ta ji ba ka fara kafa tubalin kome ba ta yi fishi"
Ya 'karasa maganar cikin zolaya.

"Hmmm!" Kawai MK ya yi tare da cewa "Na gode sosai sai mun hadu gobe idan Allah yaso"

*

Sa'adah tana shiga a dakin mahaifiyarta ta ci burki, "Inna na dawo"

"Zo ki zauna magana zamu yi"

Ba ta musa ba ta shiga ta zauna daf da ita,"Waye ya zo?"

"Ba wani daban ba ne Baban Dadi ne"

Tabe baki ta yi tare da cewa "Waye hakan, kar ki ce mini Mahmoud abokin Muutar?
Cikin shagwaba ta rungumo uwar tata ta ce "Shi fa mene ne Inna?"

Ture ta ta yi tana cewa
"Ashe baki daina bibiyar yaron nan ba ko? 'dazu amsar da ki ka bani na komai ya kusan 'karewa akan maganar aure, ashe kina nan kina zawarcin Muutar ne? Wannan shi ne al'kawarin da ki ka mini?
Tunda kin zabi son ranki sama da nawa to ki je ki ta yi,
amma ki sani ba da yawuna ba, ba kuma da son raina ba, sai don kin fi 'karfina, don kin san zaki samu goyon bayan mahaifin ki ne"

Ta nisa sannan ta ci gaba da cewa, "Tunda na ga kina ta hanzarin shiryawa tare da 'doki na tabbatar ba kowa kike wa wannan rawan jikin ba sai shi"

"Inna ba fa yadda kike zaton lamarin ba ne wallahi ban karya al'kawarinmu ba, amma don Allah ki yi hakuri ki gafarce ni ba na son kina damun kan ki akan wannan maganar"

"Ai dole na damu tunda na gane ke da Baffanku, ba ku da burin da ya wuce ki koma gidan Muutar, ni kadai na san ba'kin ciki da wahalar da na sha kafin na samo ki a dalilinsa. kuma yanzu da komai ya wuce sai ya lallabo ya sake dama miki lissafi, saboda ya mai da ke marar zuciya, wacce ba ta san ciwon kanta ba"

Cike da tausasa murya Sa'adah ta ce, "In sha Allah Inna ba zan sake shiga halin da kike jin tsoro ba, ni ma nasan abin da kike guje mini, tuni na cire shi a raina."

"To idan dai haka ne ki ba wa Alh Mamman ko yaron nan Anwar dama wani cikinsu ya fito, ki yi aurenki idan ba haka ba, hankalina ba zai kwanta ba."
Ta fada tana goge hawaye da hannun zaninta.

Jikin Sa'adah ya yi sanyi ashe dai da gaske Inna take akan ba za ta koma wa Malam ba? Ashe haka ta zafafa lamarin?

Wannan wacce irin ba'kar 'kaddara ce ke bibiyar ta ne? Bayan doguwar wahalar da ta sha akan komawarta 'dakinta, sai da abu ya zo a lokacin da ba ta yi tsammanin zuwansa ba, kuma mahaifiyarta ta yi bara'a da lamarin, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi.

*_Wai mene ne ke faruwa a tsakanin ma'auran biyu? Mene ne ainihin labarinsu? Mene ne ya raba su duk da matsananciyar soyayyar da ke tsakaninsu? Mu je ga mafari don jin wacce irin waina suka toya?_*

Al'kalamin
SURAYYA DAHIRU
✍🏼✍🏼

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

19-20.

*MAFARI*

Malam Basiru Ado Gogel, haifaffen garin Gogel ne, wani gari a 'karamar hukumar Warawa. Karatun Allo ne ya kawo shi cikin garin Kano, ya sa himma har Allah ya taimake shi, ya haddace al'kur'ani, sannu a hankali kuma ya fara sana'ar tura kura a kasuwar Singa

Da damina zai tafi gida yayi aikin gona gadan-gadan kasancewar al'ummar garin Gogel manoma ne, duk da ya ta so ba uba, domin ya na da 'karancin shekaru mahaifinsa ya rasu, dan haka ya yi birgimar ta shi fa'din rayuwa a tsakanin mahaifiyarshi da 'yan uwan mahaifinsa.

Da haka ya hada jarin sa ya bude 'yar tireda a cikin unguwar da ya ke hayar 'daki, a unguwa uku, a shekarar kuma aka masa aure da Salamatu 'diyar 'kanin mahaifiyarsa wadda asalin mahaifiyar ta shi 'Yar asalin gamawa ce ta jahar Bauchin Yakubu, aure da rabon haihuwar sa ne ya kawo ta Gogel, kenan Salamatu ma, da ga Gamawa aka ba shi ita.

Ya taho da ita cikin kano, suna zaune lafiya, cikin rufin asiri.

Yarinyar su ta farko da suka haifa bayan shekaru uku da aure, sunan ta Sumayya, ba sunan kowa taci ba, illa sunan Nana Sumayya, macen farko da ta yi shahada a musulunci. tare da fatan yarinyar ta sami albarkacin mai sunan.

Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin rufin asirin Allah, dukkansu sun da ce da juna, masu ha'kuri ne, masu kuma wadatar zuci ne.

Sai da Sumayya ta yi shekaru takwas sannan aka haifi Sa'adah wadda sunan mahaifiyarsa ta ci (Sa'adatu). Daga shi har Innar su Salamatu su ke kiran ta Iyah, kamar yadda ake kiran mai sunan nata. A shekarar kuma mahaifiyarshi ta rasu, shi yasa ya tattara ko mai da ya ke dashi a Gogel ya siyar illah gona 'daya da ya bari, wadda zai dinga noma wa, sai kuma 'dakin mahaifiyarsa da yake cikin gidansu ya rufe shi saboda idan ya je Yana da gurin zama. ya zo kano ya si yi madaidai cin gida anan cikin unguwar gidan akan titine a kuma babban layin na Unguwa Uku.

Haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya cikin ha'kuri da godiyar Allah, har Sumayya ta kammala 'Karamar sakandire manema suka mata ca kasancewar ta doguwar mace fara sol irin fulanin Gamawa.
Idris shi yafi kwanciya a ran Malam Basiru dan haka ya ce ya bashi, ba kuma ya bu'katar komai a gunsa sai sadaki da musulunci ya wajabta, komai zai ma ta idan ta je gidan shi sai ya yi.
Wannan karamcin da iyayen Idris suka ga ni ya faranta ransu ba ka'dan ba, suka girmama lamarin Sumayya da iyayen ta, kullum cikin jan kunnen shi su ke, akan ya ri'keta cikin aminci.

Haka aka yi auranta ba wani hidima, ya 'dauke ta zuwa ogshobo ta jihar osun inda yake aiki da babban bankin Nigeria (CBN) reshen jahar osun.

Dan haka Sa'adatu ita kadai ta taso a gidansu domin kuwa, ba ta wuce shekaru takwas ba, aka aurar da yayarta kasancewar mahaifinsu bai wani damu da karatun boko ba, muhimmi dai a gunshi a haddace alkur'ani.

Tun kuma akanta basu sake samun haihuwa ba, shi yasa sha'kuwa mai yawa ce tsakanin ta da iyayenta biyu har tana rasa gane waye yafi sonta a cikin su.

Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba, Iyah ta kammala 'karamar sakandire, amma ganin yadda ta k'wallafa rai a boko da kuma yadda ba ta sauraren ko wanne saurayi yasa Malam Basiru barin ta ta tafi babbar sakandire, kamar wasa aka zabe su, su biyar a makarantar su, ta GGC U/Uku, su rubuta jarrabawar shiga sakandire ta gwamnatin tarayya ta Kano (FGC KANO). jarrabawar na fitowa kuwa sunanta ya fito cikin mutum uku da suka yi nasara, ita kanta ta yi mamaki tunda duk ragowan da suka fa'di sun fita 'ko'kari.
Chapter 10 · 0% Book details