← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 113

Sashe 108

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fa'da hawaye na zubowa.
Da sauri ya matsa ya rungumeta, yana jin tamkar an yaye masa wata katuwar masifa a rayuwarsa, yana jin wata irin salama tana mamaye dukkan zuciyarsa.
Ashe wannan 'daaurin da 'kirjinsa ya yi, ashe wannan fargabar da yake tsintar kansa a ciki, duk saboda rashin samun aminci ne daga wajen Sa'a?

A yanzu da ta yarda zasu zauna lafiya sai ya ji tamkar anyi masa bushara da gidan aljannah ne.

A fili ya dinga fa'din "Alhamdulillah! Allah kasa karshen tashin hankalin da zamu fuskanta kenan, Allah ka sanya wannan shine karshen jarrabawar mu".

Sau uku tana yun'kurin yin magana sai ta kasa, da ya lura da hakan sai ya ce "fill free, fa'da mini abin da ke ranki".

Ta tura baki gaba ta ce "Amma dai ka yi mini al'kawarin ba zaka ha'da ni zama da wata matarka ba, kuma yanzu na tabbatar waccan part din na Amaryarka ne".

Ya sake ru'ko ta sosai ya ce "Ban manta al'kawarin ba, amma sai nake ganin a waccan gidan da kika tsara yadda za'a gina shi, na miki wannan al'kawarin, yanzu kuma ai bashi bane".

Da rawar murya ta ce"kar ka hadani zama da ita, kar ka bari na dinga ganin mua'amalarku, zaka iya rasa ni a dalilin ciwon zuciya ko hawan jinin farat 'daya".

"Ina son ki koyi jarumta Sa'adah! Ina son hankali na ya tsaya a wuri daya, a yanzu da nake matu'kar mararinki, idan na rabaku zan halaka ne, Ina tabbatar miki zan tare ne a inda zuciyata tafi so, shi kuma adalci wajibi ne ka yiwa kowa.
Addinin musulunci! Addinin adalci ne, ubangiji ya sani namiji ba zai iya raba soyayyar matansa ta zama daidai a zuciyarsa ba, sai akace an masa uzziri anan, ma'ana bai yi laifi ba dan ya so wata sama da wata ba.
Har ilah yau Sharia bata ce dole abin da ka yi da wannan, idan ka koma wajen wannan ma sai ka yi mata irin wannan ba, domin ansan ba zamu iya ba.
Amma duk da hakan sai da Annabi ya yi ta wasiyyar kar mu jingine mace, mu ratayeta ita ba sakakkiyar mace ba, ita ba matar aure ba, dole a rabon kwana, muhalli, abinci da sutura ya zama daidai (eqaul).
Shari'ar musulunci ta yiwa mata gata da adalci, ta yadda ko ba ke aka fi so ba, to kuwa indai ana kan tsarin sharia din ba za'a ki wulakanta ba".

Ya numfasa sannan ya ce "ki min hakuri zaki koma wanccan gidan amma ba yanzu ba, ki bari nima na koyi jarumtar da zan kiyaye ka'idojin shari'a".

A hankali ta ce"To" ba dan tana so ba, sai dan kar ta cigaba da yi masa gardama yana ganin Farida ce mai biyayya kawai.

Ya tsura mata ido yana kallonta, sonta sai huda dukkan sassan jikinsa yake yi, cikin kasalalliyar murya ya ce "har yanzu baki huce da ni ba, har yau baki yafe mini ba?"

Murya ba amo ta ce "me yasa ka ce haka?"

"Har yanzu ban ji kin kira suna na ba, Na sani kuwa idan kina fishi ne kike gatsa sunana dan ki nuna mini iyakata. Idan kuma ba kya son shiga shirgina sai ki yi maganar ki ba tare da kin kama sunan ba"

Ta zuba masa wani irin kallon da yake kidima shi, tana murmushin da wurshiryarta ta bayyana, hawaye kuma ya zubo mata Ta ce "Malam".

Farin-ciki ya dirar masa fiye da wadda yake ciki, rabon da ya ji ta ambaci Malam a bakinta, tun ranar da suka hadu a gidan 'Karfi kafin komai ya tabarbare musu.

Ya sa baki yana lashe dukkan hawayenta da yake zubowa.

Ya yi gyaran murya ya ce "nan da kwanaki shida zaki tare, Ranar juma'ah mai zuwa.
Yanzu mu je ki za'bi funtures din da kike so, masu harkar 'kawata gida, za su zo su shirya miki".

A hankali ta ce "Na gode sosai! Amma ka barsu, domin yanzu ina da kishiya idan ta gane haka na zo, zata samu dama akaina".

Ya kalleta ido cikin ido tsawon lokaci sannan ya ce "Na ta'ba rokon ki a shekarun baya ina so ki ji a ranki nima tamkar Sumayya nake a wurin ki, ashe baki dauke ni hakan ba?"
Ta kasa bashi amsa.
Ya ce "Wallahi Sa'adah ko wani kika aura ni zan miki komai da uba yake yiwa yarsa domin Baffah zan yiwa, lokaci ya yi da zai huta, a yanzu abin da nake ji game da shi ba wai kallon mahaifinki nake masa ba, kallon nawa uban nake masa, domin ya mini abin da na tabbatar uba ne kawai zai yi wa 'dansa.
Na yarda da maganar da ake cewa ko baka haihu ba, idan ka yi alheri ga marayu da masu rauni, ka zauna da mutane lafiya, ka yi hakuri da cutarwarsu, to ubangiji sai ya turo maka wadda zai yi maka abin da ko 'danka ba zai maka ba, haka nan idan kana da zuri'a ubangiji zai baka wadda zai jibanci lamarinsu ko da baka numfashi".
Baffah uba na ne, da ubangiji ya bashi, komai zan yiwa jinisa a duniya ban biya shi ba, dan haka ki yarda da ni, ko ba aure a tsakaninmu Ni din mai yi miki komai ne, mai kuma tsaya miki ne a ko Ina".

Ya yi shiru! Sai kuma ya cigaba da cewa "wanccan gidan da kike magana akai tun ranar da kika ce mini filin ki Baffah ya siyar ya bani ku'di, zuciyata take ta bugu akan na baki shi kyauta, sai dai bani da halin bawa Farida irinsa, dan haka na bawa Jawad shi, na je an canja takardun, sunan Jawad ne akai.
Idan na gamsu sosai zan iya ware miki gida, shikenan sai ki koma gidan d'anki kafin na samu damar da zan sake yi muku wasu gidajen a jere amma ko haraba ba zan ha'da ku ba".

Karon farko da tasa hannu da kanta ta rungume shi tana kuka 'kasa-'kasa. Ta tabbatar da gaske Malam din nata ne har yau.

Ta ce" na gode sosai ubangiji ya fini yabawa.
Zan iya kokarina ban tayar da hankalinka ba, ba zan cuci matarka ta hanyar asiri, ko sharri ko zagon kasa ba, lafiyarta da mutuncinta har ma da dukiyarta amanace a gare ni, na yi maka al'kawarin ba zan tsokaneta ba, ba zan taba mutuncinta ba, ba zan yi shirka dan na farraqa tsakaninku ba, na yarda 'kaddararka ce itama.
Amma abin da nake so ka yi mini dalci a ciki shine ni ban iya munafunci ba, am straight forward, ka ja mata kunne akan tsokanar da take fakar idon mutane tana yi mini, ba zan yi gaba da ita ba, amma kuma babu aminci a tsakaninmu da zamu zama so close, kowa ta yi harkar gabanta".

Jiki na rawa ya dinga fa'din"thank you! Thank you so much my love".

Saboda ba 'karamin nutsuwa ya samu na saukowar ta botsarar tasa ba,😅 ya dinga neman tsari da abin da zaisa ta sake mur'dewa. Ya tabbatar har zuciyarsa tsoron fishinta yake yi, tsoron ta birkice yake yi, 'karfin hali kawai yake gwada mata, idan yana bagarar da ita ko yana nuna mata iyakarta.

Bai nemi ya sake ta'ba ta ba, duk da yana bu'katar hakan. A waya ta zabi furniture's din da take so, amma Mk ya canja mata da masu tsadar gaske, ta dinga jin tausayinsa, shikuma so yake ya wanke mata zuciya, ya sani dan ta kwantar masa da hankali ne, da kuma son ya fahimci ita yanzu ba luxury life a gabanta yasa ta zabi masu sau'kin kudi, shikuma sai ya daure ya siya mata masu daraja sosai tunda ya yi 'karfi yanzu, business dinsa yana garawa 'kwarai da gaske.

Ya mayar da ita gida, suka rabu cikin shau'ki tamkar wani abin bai ta'ba gittawa a tsakaninsu ba.

Kai-tsaye gida ya wuce tunda biyar ta yi, ya samu Farida a falo ta yi kwalliya ta sha kyau, ga abinci a dining, yana jiransa, ya dinga jin kunyar me zai ce mata kuma yau?
Tunda yake fita da Sa'a baya cin abincin rana a gida, saboda tare yake ci da Sa'adah.

Ya daure ya bita zuwa dinning din, ta zuba masa brown sphagetti da ta ji kayan lambu, sai papper fish a gefe.

Ya dan ci ka'dan ya ture domin ya riga ya shafa'a ya ci a waje.

Takaici ya 'kume Farida, idonta ya ciko da 'kwalla.

Ya kalleta ya ce "menene yake damunki?"

Da rawar murya ta ce "yau kusan kwanaki goma baka cin abinci na, jiyan nan ka gama yi mini al'kawarin yau zaka dawo mu yini tare, kai ka ce na yi maka wannan nau'in abincin, na yi kuma ka bar mini abina".

"Yi ha'kuri my ferial! ba haka bane, ai dai kinsan duk safiyar duniya da abincin ki nake karin kumallo, idan na yi aiki na gaji ne, yunwa ta kamani sai na kasa daurewa na je capteria na ci, amma yi hakuri zan dinga jurewa".

Yana rufe baki ta ce duk zamana da kai ban san kana zuwa capetaria kullum ba, sai yanzu dai da ka yi Kome!
Na san abin da nake yi, Ina sawa abin da nake so ido fiye da kaina, kullum ka cire kayanka scent din Gogel nake ji, ban yi magana bane saboda na sani matarkace kuma cike kake da 'dokin sake dawowar ku abu guda, amma kuma shikenan sai abin ya zama ba waiwaye tun yanzu kake son sai dukkan rauni na ya bayyana? Ka yini a wajenta, ka dawo mini gida a gajiye da ka kwanta sai barci".
Ta fa'da muryar ta na rawa.

Sanin da ya yi ita din ba mai 'korafi ba ce, sai ya gano lallai bango ya nemi kaita, ya sani kuma da gaske ne ya watsar da ita a wannan tsukun.

Dan haka ya sassauta murya ya ce "very sorry my dear! Ko ka'dan ba abin da kike nufi bane, amma tunda na bata miki, ki yi hakuri ki sake yi mini afuwa da uzziri. Ubangiji ya miki albarka, ke mai hakuri ce, mai kuma fahimta ce."

Da haka ya lallaba ya jata bedroom, second round din da bai yi da Sa'a ba, ita ya yi da ita.
Chapter 108 · 0% Book details