← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 113

Sashe 100

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dinga yi mata maganganu masu da'di, Wanda wasu ta tabbatar ya fa'da ne dan hankalinta ya kwanta amma dai ta ji da'di kwarai da gaske, ta samu sau'kin daurewar da kirjinta ya yi.

Ya kalli agogo ya ga har sha'dayan dare ta gota ya mike da ita cak tamkar yar jinjira ya shige daki da ita ya dire kan gado ya ce"Ashe ma fafaloloce ba nauyi"

Ta dan murmusa kadan ba tare da ta ce komai ba.
A haka ya dinga hilatarta sai da ya raya daren da ita cikin wata irin soyayya mai tsayawa a zuciyar mace.

Har ranar daurin aure ta zo ba wani jituwa tsakanin Mk da Sa'adah.

Ranar juma'ah 15/7 aka sake daura auren Mukhtar Kabir Bichi da Sa'adatu Bashir Gogel akaro na biyu akan sadaki Mai darajah.

Sai yamma suka baro Gogel, duk yadda Mahmoud ya so suje gun amarya Amma Mk ya ce ba inda za shi.

Dr 'Karfi ya kalli Dr Mk da ya yi kicin kicin da fuska ya ja tsaki ya ce "aikin kawai duk wani cin magananinka na 'karya ne, wato yanzu ka sami kwanciyar hankali shine zaka hau wani fiffika, to dan ma dai tsiyar Sa'adah ta fi taka, yanzun nan zata sumar da kai, farfadowa sai a gadon asibiti".

Fuska a daure Mk ya ce 'Tunda ba a lahira zan ji ni ba, ai da sau'ki, ka takura ni fa ".

Da dariya 'Karfi ya ce wallahi ka bini a hankali ka san ina da dorinar da idan na zuba maka sau uku, amarcin da kake rawar jikin zaka sabunta shi ba zai yiwu ba".

Dariya ta kwace musu dukkansu Mk ya guntse ya ce "Na rantse kuwa da ba zan yarda ba".

Har suka rabu caccaka Mk yake sha a wurin Mahmoud.

Washagari da hantsi Mk ya yiwa Sa'adah siyayyar komai na amfani, karon farko da shi a karan kansa ya siya ba wai Jawad ya saka shi akan dole ba, ya tuno sadda take cewa idan ya sake yi mata wani abu na alheri ba zai gama da Hajiya lafiya ba.

Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya yana ayyana banda zuciya ba a ganinta bare a hukunta ta ai bai kamata zuciyar tasa ta zarme akan soyayyarta haka ba.

Ya nisa a fili ya ce "Albarka cin Baffah na yafe wannan maganar".

Amma haushin ganinta da Khalil da kuma tariyar da ta ce ba zata yi yanzu ba, ya matu'kar bata masa rai, shiyasa kullum ya yi sallah sai ya roki ya samu dalilin da itace zata nemi ta tare da bakinta.

Ya cika mota da kayayyakin ya nufi gidan su Sa'adah.
Domin ya kai mata ,tunda yanzu ta rataya a wuyansa, duk da ita bata da niyyar sauke nasa hakkin da ya rataya a wuyanta.

Surayya Dahiru
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

*NA*

*SURAYYA DAHIRU*.

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

*GAISUWA GA*.
*Haj Zulaihatu Sani Kagara*
*Haj Maimuna Beli*.
*Hassana 'Danlarabawa*.
*Ku Dade, ku yi 'karko irin na Dabino*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

107-108.

Sannu a hankali yake yin tuki, har ya isa gidansu Sa'a.

A zauren kofar gidan, ya tsaya, ya fito da wayarsa, ya dinga 'kiran layin Sa'adah amma tana gani ta yi mirisisi, yana tsaye Baffah ya shigo, suka gaisa ya ce "Ya ka tsaya shigo mana".

Tare suka shiga cikin gidan, Inna ce a Zaune tana kwadon zogale.

Mk ya zauna a gefen tabarmar da Baffah yake kai, ya gaida Inna! ta amsa ba yabo ba fallasa.

Cikin nutsuwa Mk ya ce "Inna ina neman afuwarki, na sani ni mai laifi ne, amma tunda ubangiji ya sake hadamu ina rokon ayi mini hakuri, bana jin da'din yadda kuke mini ke da Hajiyar Bichi".

Kunya ta matu'kar kamata, ta dinga jin wani iri, da kyar ta yi kundubalar cewa "Ni ba fishi nake yi ba, Allah ya kiyaye gaba, yasa albarka a aurenku".

Da'di ya yi matu'kar kama Mk, ya yi ta godiya.

Baffah ya ce "Idan ka zo, ka dinga shigowa, ai yanzu ba maganar tsayawa a zaure, Ina fatan ku kammala shirin ku da sauri ta tare hankalin kowa ya kwanta".

Innah da ta gama 'kwadon ta zubawa Mk, ta kai na Baffa dakinsa sai ta yi shigewarta daki, yayin da Baffah shima ya fita yana cewa Mk "shiga tana ciki, bakam ta yi".

Ya shiga dakin ya sameta a zaune cikin kwalliya tamkar ya yi mata waya zai zo, ta yi masa kwalliyar.

Ya zauna yana shakar kamshin turarenta, ya kalleta, ya na tuna sadda ta zo wankan haihuwar Jawad irin soyayyar da suke fakar idon Innah suke yi a dakin, amma yanzu ba wani farin-ciki a tare da ita, asalima tunda ta amsa sallamarsa bata sake yin magana ba.

Ya daure ya hadiye komai ya ce "Barka da lokaci"
A hankali ta ce "Barkan mu dai".

Ya nisa ya ce"Tsakanin ki da Allah ya kamata ace anan kika wayi gari? Komai mutum zai yi ya auna abin nan a mizanin hankali da sharia, saboda kawai ki kuntata mini kika cewa Baban Na'ibawa sai kin shirya zaki tare dan Allah ba ki ji kunya ba?"

Ta yi masa banza, abin da ta san ba ya so.
Bai yi fishi ba, ya sake cewa wanne shirin zaki yi? Ki tashi kawai mu yi tafiyar mu, ke kanki nake so ba wani shiri ko kwaskwarima ba, har yau ina kallon ki a little Sa'adah dalibar FGC Kano".

Ta tura baki gaba amma ba ta tanka ba.

Ya sake yin kasa da murya, ya ce " Kin amince na kira Baban Na'ibawa a waya ki fa'da masa kin yarda zaki tare yau? kawai sai mu yi tafiyar mu da waccar katifar da kike ta ajiye da ita. Zan dai siyo miki wata, tunda naga har yau din nan tana cikin abubuwanki masu daraja".

Ta hango katifar da take saman wadirof a 'daure wadda ya siyo mata ne tun shigar ta FGC a lokacin ma basu san juna ba, amma ta ki yarda a bayar da ita, ta kafe tana son abarta.

Ya taya ta kallon katifar da ba abin da ta yi, tunda ta da ce mai aminci.

Ya ce "ya kamata mu tafi da ita, ko akanta ubangiji zai sai a samowa Jawad kani ko kanwa".

Ta dauke idonta daga kallon katifar ba tare da ta ce 'kala ba.

Ya matsa kusa da ita ya ce "pls Sa'a zuge mini zip din rigar nan, ina son ganin kirjin ki, just gani zan yi, I won't touch it" .

Ta mike ta koma kan wata kujera da take dakin, ta juya masa ba, tabbacin ba zata yi ba kenan, zuciyarta sai hango mata take Allah 'dai ya san me ya yi da wata matar kafin ya zo nan, yana mata maganganu na rainin wayo da dasa ciwo a zuciya.

Ya nisa ya ce da alama, dukkan hardship din nan da muka yi going through bai zame miki iznah ba. saboda kawai kina da masu daure miki gindi ana dannata, abin da baki sani ba, indai har kika ce zaki cigaba da yi mini taurin kai wallahi zan yi dealing din ki with iron hand".

Ta ce "Ai daman na san ba abinda da zan kwasa a hannunka sai ba'kin ciki, na ce bana sonka, bani da burin aurenka amma an matsa mini".

Kuka ya kwace sosai.

Cikin kuka sosai ta ce"Idan ina sha'awar auren mai mata Allah ya tsine mini. Amma saboda ka fini a wurin Baffah ya mini fin 'karfi, ni an cuce ni, gaskiya angama da ni".

Jikinsa ya yi mugun sanyi, amma ya waske da cewa "Da gaske ba kya sona? To Ki yi hakuri son da nake miki ya isa ya ri'ke mana auranmu".

Bata tanka ba, haka bata daina kukan da take yi ba.

Ya ce zo muje ki raka ni unguwa, daga nan mu biya, mu yi lunch a restaurant din Royal Tropicana, mu tuno moment din mu na baya".

Ta 'kara sautin kukanta ta ce "sai dai ka je ka dauki Farida kuje Tahir sai ka fi shaukin tuna bayan. Ni kuwa me zaka yi mini na ga haskenka? ai babu shi, iya tozarci ba wadda ba ka mini ba, ina cikin bala'i amma ka iya daukar wata macen ka tare da ita a hotel, sannan har ka iya ce mini wai sai ka tuno ni kake gamsuwa".

Ya matu'kar firgita da kalamanta, ashe. duk motsinsa ta sani? Ya kalleta a kidime ya ce "waya fa'da miki wannan maganar?"

A hassale sosai ta ce "wadanda suka ganku, masu son na kalli yadda ka tattara ka yi wurgi da ni da dukkan al'amarina. Masu son na cireka a raina, na daina ganin idan babu kai ba zan iya rayuwa ba, domin kana can kana more rayuwarka da wata macen, ahalin ni ina shirin zaucewa adalilin ka".

Ta yi shiru tana shesshekar kuka mai ha'de da gunji mai cin rai.

Tausayinta ya maye gurbin takaicinta da yake ji, ya dinga jin komai ya narke na laifukanta a zuciyarsa, ya sani ita din mai tsanani kishi ce akansa, tamkar yadda yake tsananin kishinta.

Ya sani kishin Farida ne yake yagalgalata mussaman da bata samu damar amayarwa a lokacin auren ba, ta bar abin a zuciyarta yana cinta.

Ya numfasa yana jin sonta da ya makale a kasan zuciyar sa yana ta tunkubowa yana mamaye kowanne gurbi da sako na cikinta, sai shine yake ta kokawa cikin jarumta kar son nata ya mamaye har inda Farida take makale.

Ya sassauta ya ce "mu yafewa juna hakanan, zukatan mu sun wahala, gangar jikinmu sun yi kewa ba ka'dan ba, pls My dear Sa'adah let gone be by gone".

Har ranta ta ji da'di, dan haka ta sassauta kukan ta sa hannu ta dauko, tissue ta fara goge fuskar ta.

Ganin ta rage kukan, ya nisa ya ce "muje ki yi shopping din kayan kwalliya".

Ta girgiza kai tare da cewa "ina da su".

"To muje ki raka ni, na gaida Aunti Sumayya, na bata ha'kuri ta daina watsi da al'amarina, tunda mun shirya ta yafe mini".

"Ba zani gidanta ba, sai ta neme ni".
Chapter 100 · 0% Book details