← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 113

Sashe 60

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska ba walwala ta ce "idan har kana so na huce, hankalina ya kwanta, to ka zauna lafiya da matarka, na lura itace bata da gaskiya, amma abin da zaka lura ko a lahira wani na cin albarkacin wani, ka manta komai ta yi maka, ka mata afuwa, ba hankalinku daya ba".

Ya nisa ya ce "Allah Hajiya ban so ki ka shigar mata ba, so nake kawai ta
banbance tsakanin zaman lafiya da kuma zaman tashin hankali, ta fitine ni wallahi".

"Kaine Babba hakuri za ka yi! sonka take yi, shiyasa ta ke kishin ka, tunda ka fahimci matsalolinta sai ka kiyaye abin da zai tunzura ta, har hankali ya shigeta, wata rana ko ance ta yi wani abin ba zata yi ba".

"Shikenan na ha'kura saboda ke, amma wallahi ki dinga mata fa'da Hajiya! tana sake yin mini yadda ta ga dama ne saboda kina bin bayanta, kwalbar ha'kuri na ta kusa fashewa akan lamarinta".

"Kai kuma haka za ka yi? mahaifinka mai ha'kuri ne akan sabgogin mata, kafin muga fishinsa mukan
'dade, duk yadda zan bata masa rai kuwa da zarar nace yi hakuri to maganar ta kare".

Shiru ya yi! A ransa kuma sai cewa yake yi ba za ki gane mai yarinyar nan take mini ba ne, inda a iya kishin ne ai da sauki.

A fili kuma ya ce "shikenan Hajiya ta ci albarkacin ki magana ta kwanta".

" So nake ta mutu murus, ba wai ta kwanta ba".

Ya yi dairya ya ce "ki mata fa'da, idan ta kwantar da hankalinta, magana ta wuce, amma idan tana tayar min da hankali ai dole laifin baya ya dinga tasowa, yana zama sabo".

"Zan ja kunnenta sosai, amma ka ri'ke a ranka na kashe wannan matsalar, kaima ka kashe ta a ranka, sannan kar ka kuma zuwa cin abinci gurina idan kun yi fa'da, bana so! bana so".

Ya amsa da "to sannan ya mata sallama ya tafi, yau har zaure ta taka shi tana cewa "ka zarce gida kai tsaye ka nuna mata na isa da kai."
Ya amsa da fadin "To In sha Allah".

Madallah da uwar miji irin Hajiyar Bichi, masu maida surukansu tamkar ya'yan su, suke musu adalci irin wadda ko wacce uwa take so ayiwa 'yarta.

Gidan kuwa ya zarce, ya sameta a inda suka barta har lokacin kuma kukan ta ke yi, sai dai alamun sun nuna ta yi wankan duk da ba kwalliya ta yi ba.

Ya tsaya a bakin 'kofar falon ya zuba mata ido yana jin takaicinta na kama shi sosai.

A kausashe ya ce "Rashin mutuncin ki kullum 'kara tunbatsa take yi, ki mini cin mutunci, ki raina arzikina ki nuna mini bariki ya fi aurena, sannan ki zame ki kai 'karata, saboda kin koyi munafunci?"

Ta kasa magana sai kukanta da ya 'karu.

Shi kuwa ya zarce da fadin "Tunda kin zama macijiya ki sare ni, ki koma ki baibaye uwata da kalolin alherinki na makirci da tuggu, to Ina tabbatar miki nima daga yanzu kome kika mini sai na fadawa Baffa, su dinga raba 'bacin ran tare da Hajiya".

Ya ja tsaki ya shige dakinsa.
Ta jima tana zaune cikin rashin sanin abin yi, sannan ta tashi ta bi bayansa, cikin sa'a bai rufe 'dakin ba, yana zaune a bakin gado iskar fanka na kada shi.

Akan gadon ta zauna kafadunsu na gogaiya da juna, ta ri'ko hannunsa tare da jingina kanta a kafadarsa murya ba amo tace"Am sorry Malam! Wallahi zuciyata ba za ta iya 'daukan fishinka irin haka ba, ka yafe mini' ka manta dan girman Allah".

Ta karasa cikin kuka na sosai.

"A hankali yace "Na ha'kura, amma mantawa sai a hankali, idan kin kiyaye, kin kuma rufe 'kofofin da zan dinga tunawa din! ki sani ba dan Hajiya ba, da ban san ranar da zan miki afuwa ba, saboda kin riga kin shayar da ni mamaki da ba'kin ciki mai yawa".

"Na yarda na yi ba dai dai ba, dan Allah kar ka yanke mini kauna, ka sake bani dama".

Ita da kanta ta yi dalilin da sai da suka hadu a lokacin, tun Mk na basarwa, har ya kasa cigaba da jarumtar ya ru'ko ta suka sami nutsuwa, haka nan sai da haduwar ta yi awon gaba da kaso hamsin na bacin ran da ke zuciyarsa.

Tun a wannan rikicin Sa'adah ta fahimci ta rasa damammaki a gurin Mk, ya matu'kar rage rawar jiki akanta, ya daina tattauna halin da yake ciki da ita, haka nan baya zama ya shiririce mata da hirarrki kamar da, za su yi hirar amma a gajarce, sannan mafi yawan hirar sai dai ita ta kawo.

Haka suke wannan zama har Jawad ya dawo daga gidan Samira, so take ya barta ta je Gombe amma tsoron tambayar ta ke yi, har mamakin kanta take yi, yadda take tsoron su yi rikici yanzu.

Washagari alhamis da safe ta tura Jawad ya tambayo musu za su je su gaida Maman Gombe da ganin Baby boy, tunda sai satin sama hutun su zai 'kare.

Jawad bai jima da zuwa ba, ta ji Mk na 'kwalla mata 'kira, gabanta ya fadi sosai da hanzari ta shiga dakin tana cewa" Na'am".

Kallonta kawai ya yi, ta gane ba zai barta ba, ta tsugunna tana sauraronsa.
Sa'a an 'kara kwas na respect 😁

"Kin aiko Jawad za ku Gombe, inace dama ban hana ki ba tun farko?"

Ta yi sukuri tana jin fargaba na kamata, da 'kyar ta bude baki ta ce " ai kace ba zan ga alheri ba".

"To yanzu na ce ki ga alherin! Aje lafiya, adawo lafiya shikenan?"

Ta kalle shi ta ga yana daddana waya hankali kwance.

"To kwana nawa zamu yi?"

"Sai kin gaji da zama sannan ki dawo".

Ya fada hankalinsa na kan wayarsa.
Hawaye ya cika idonta tana jin tamkar ta sume.

Murya na rawa ta ce "Malam yanzu fa ban yi maka komai ba, Allah shine shaidata, na yadda na ke gudun na 'bata maka, amma kai kwata kwata ka yanke mini kauna, ka ki ka yafe mini, kana zaune da ni akan tilas.."

Kuka ya kwace mata sosai, cikin ko in kula ya ce "kin so yin kuka ne, kince za ki je Gombe, nace adawo lafiya, har da abin arzikin ki yi iya adadin kwanakin da kike so, shikenan kuma sai ki bare mini baki, to fada mini me kike so na ce miki?".

Ta dago da manyan idanuwanta da suka yi ja ta zuba masa akan fuskar sa, tsawon lokaci idanuwansu a sarke, chemistry na aiki akansu, a sanyaye Mk ya janye fuskar sa gefe daya, yana kokawa da abin da ya taso masa.

A hankali ta furta "so nake ka ce kwana kaza za ku yi".

"To sati hudu ya yi miki?"

Da mamaki ta kalle shi ta ce"ai zuwa wannan lokacin su Jawad sun '
dade da komawa school".

Kai tsaye ya ce "Ba da shi za ki tafi ba ai, ke 'kadai za ki yi tafiyar ki, ki je ki yi abin da ki ka ga dama".

Jikinta ya yi sanyi ta tabbatar ba barinta zai yi ba, sai kawai ta mike ta ce "Na gode".
Ta fita zuwa kicin, ta hau aikin abincin rana, ta na yi tana kuka, bata ta'ba sanin Mk na da ri'ko ba sai a wannan karon.

Haka tana ji tana gani har Inna ta dawo ba ta je ta gano su ba.

Ko zuwa ta yiwa gidansu dan ta yiwa Inna barka da dawowa, da 'kyar ya barta, shima sai da la'asr lis da zai tafi shago ya tafi da ita, kafin su Isa magariba ta yi, amma dan son ya musguna mata bata fi awa daya ba ya mata waya shi zai tafi, idan kuma bata gama ba, ta taho idan ta kammala, alhalin yana kaiwa fiye da goman dare.

Haka ta fito ta bishi yana ta cin magani, har suka iso ko uffan ba suce ba, wannan sabuwar rayuwar ta yiwa Sa'adah tsauri matu'ka da gaske mussaman da bata saba ba, ya riga ya sabar mata da wasa da raha, uwa uba kullum shine cikin rarrashinta da son ganin murmushi a fuskarta, shiyasa yanzu sauyin ya zo mata da tashin hankali.

Hatta Inna sai da ta yi 'kwalla da taga irin ramar da ta yi, sai dai fa'da sosai ta mata tana fadin tasan itace duk ta jànyowa kanta komai take ciki.
Cikin kuka ta ce "Ni damuwata 'daya yadda Anty zata ga rashin kirkin banje na gaishe ta ba".

Da sauri Inna ta ce "ba zata ga laifinki ba ai tasan aure ki ke yi, ba zaman kanki ba, kar ki damu ta warware sosai, Ba ki ga Anis ba ya yi 'bul'bul da shi, ki bi mijinki a hankali kin ji".

Haka suke rayuwar yau fari gobe tsumma, shi kansa Mk so yake ya manta komai amma maganganunta sun dasa masa wani irin ciwo a zuciyarsa, sun yi karfin da suka sababa masa hawan jinin da yake shan magani kullu yaumin, idan ya tuna sadda ta ke fada masa matan bariki na da daraja fiye da matan aure sai ya ji tamkar ya sume.

Ranan asabar da safe suna karyawa da wainar shinkafa da miyar ganye da ta ji tantakwashi, sammako ta yi ta shirya masa tare da kunun farar shinkafa da danyar gyada, tasan yana son wadannan abincin, sai da ta yi wanka ta ci kwalliya sosai sannan ta gabatar musu.

Suka kammala ta kwashe komai, ta zauna kusa da shi sosai, a ladabce ta ce "Malam ina son na je asibiti".

Ya kalleta ya ce,"me za ki yi?
Ta sunkuyar da kanta 'kasa ta ce " abin nan zan cire ".

Ya zuba mata ido yana jin tausayinta na neman kama shi, yasan so take ta yi abin da zai sa shi farin ciki, dan haka sai ya sassauta ya ce "Inace tun a Abuja na ce ki bari mu gani tukun, ko abin da nake fata zai kasance, idan ki ka haihu kun zama ku uku lissafi zai canja".

Ta dago idonta cike taf da hawaye ta kalle shi " Na dauka ka fasa tafiyar da ni, tunda yanzu ka canja mini akan komai".
Chapter 60 · 0% Book details