Sashe 20
Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ilai kuwa a tsakar gidan ta tarar da ita sai safa da marwa take yi, jin sallamar ta yasa ta tsaya cak, tare da zuba mata ido, amma ganin ta futu-futu kuma idanuwanta a kumbure sai ta sami sau'kin tashin
hankalin da ta shiga, don ta tabbatar Iyah ba za ta iya biyawa wani wajen a haka dukun-dukun ba, amma duk da hakan sai da ta ce "A ina kika tsaya har zuwa wannan lokacin?"
Fuska daure ta ce "kwanakin da na yi ban je makarantar ba shine suka ci zalina."
Ajiyar zuciya Innar ta sauke sai kuma ta ce "Madalla da wannan cin zalin."
Sannan ta dauki buta ta zaga ban'daki.
Sa'adah daki ta yi tana tube kayanta, zuciyar ta fes ,tana tuno hirar su da MK da ya mantar da ita takaicin da ya kunsa mata a safiyar yau.
Tana idar da sallah ta wanke uniform din da ya baci da 'kura sannan ta zuba abinci, kai tsaye falonsu ta shiga wanda ba komai sai leda a shimfide da labulaye, sai yar karamar talabijin kirar (sharp) a kan dan karamin tebur, kusa da mahaifiyarta ta zauna da ta ke kulla bushasshiyar kubewa.
Ganin Innar ba ta 'daga kai ta kalle ta ba yasa ta fadin, "Inna ko ki tambaye ni, ko na ji ciwo a cin zalin da aka mini?"
Cike da rashin kulawa ta ce "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, tunda kin yi girman da za ki zabawa kanki abin da ya dace da ke ai magana ta 'kare"
Jikinta ya mutu ta ce "Inna kin ce magana ta wuce, amma kina ta share ni kina nuna ko oho da ni" Ta ture abincin tare da fashewa da kuka.
Da farko share ta ta yi, amma jin yadda take ta sauke ajiyar zuciya, ga kuma hawaye nata tsere a fuskarta, sai ji ta yi raunin da bata son ta nuna mata ya kubce mata cike da tarin soyayya irin ta uwa ta tausasa murya ta ce "Share hawayen kin san dai ba na son kukan ki ko?"
Ta tura baki cike da shagwaba ta ce "Inna ai da ne ba kya son kukan nawa, yanzu sau nawa za ki ga ina kuka amma ko ki nuna kin gani bare ki rarrashe ni?"
Murmushi ta yi ta ajiye ledar da take hannunta ta zuba mata ido sannan ta ce "Iya bawai kukan naki bai dame ni ba ne. Ni kadai na san yadda zuciyata ke zafi idan na gan ki cikin rashin sukuni, halayen da nake gani a tare da ke ne ba su mini ba, ina matu'kar kaduwa da yadda kike kokarin jefa kanki a rayuwar da ba za ta bulle da ke ba"
Sa'adah da jikinta ya yi laushi amma sai ta yi karfin halin cewa, "Don Allah Inna wai mene ne nake yi wadda bai miki ba?".
Muskutawa ta yi sannan ta ce "Iyah kin san dai ke din nan ba 'yar kowa ba ce, mu iyayenki ba wasu ba ne illa masu neman abin da asirinmu zai rufu, amma ke kina daukar ra'ayin ya'yan masu wadata, ba kya duba idan ba yawan gashinku daya ba, yawan kitson ku ba zai daidaita ba! Watanni kadan ya rage ki kammala makarantarki, kin san kuma aure za a miki amma duk saurayin da zai zo gidan nan da maganar aure za ki yi tsalle ki ce bai miki ba, amma kina son abin hannunsu saboda kawai kin 'dorawa kanki sai kin daura abin da kike gani a jikin yaran da 'karfin iyayenku ba 'daya ba"
Ta nisa tana jiran ko Sa'adah za ta yi magana sai taji sabanin hakan, duk da dai ta lura jikinta ya sake yin laushi fiye da 'dazu, don haka sai ta sake cewa, "Ki ajiye wannan dabi'ar, sannu a hankali idan kina da rabon yin arzikin za ki yi shi ne. Yanzu dai babban misalin da zan miki da yayarki ne, duk da cewa lokacin da aka aurar da ita ba ki da wayon da za ki gane komai, mijinta ko mashin din da kika raina mai hawansa ba shi da shi, amma a yau mene ne bai mallaka ba? A saninki 'kasashe nawa ya debi iyalinsa suka fita? Wace irin hidima da karamci ne ba ya mana ke ma shaida ce tunda dai ko wannan makarantar da kike yi ba don shi ba, da ba ki yi ta ba, da ace farko ta raina matsayinsa da yanzu ta cim ma wannan jin dadin da kowa ke mata kallon tana ciki? Tsakanin ki da Allah ba don ta sau'ka'ka buri ba ta kai wannan matsayin?"
Kai Sa'adah ta girgiza wa mahaifiyarta don kuwa harshenta ya mata nauyi, amma a ranta tana raya in dai akan zaben miji ne an wuce wannan babin, zuciyarta ta riga da ta aminta da MK Bichi kuma shi ma ai talaka ne tunda ko mota ba shi da ita. Jin da'di da son kayan 'kawa kuwa ba mahalukin da ba ya so sai idan bai samu ba, ita a jininta ne son gayu ba wai fariya ko 'karya ta sa a ranta ba. 😀 Don haka ba ta dauki maganar ajiye dogon buri da aka mata nasiha da wani muhimmanci ba.
"Kullum addu'a ta Allah ya ba ki miji nagari wanda zai kula da ke da amana, ke ma irin adduar da za ki rike ke nan. Dauki abinci maza ki ci kar ya gama hucewa, Allah ya miki albarka."
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Amin na gode?" Sannan ta ja abincin ta hau ci, danwaken fulawa ne da yaji mai da'din gaske, tana ci tana yaba yadda Innarsu ta iya sarrafa abincin gargajiya masu da'di, kawai dai abincin zamani ne ba ta yin su ko kuma don za su ja kudi ne?
Sai ta tsinci kanta da cewa "Allah Inna na kusa daina cin abinci mai nauyi."
Cike da mamaki ta ce "Me za ki dinga ci to?"
Murmushi ta yi, ta ce "Chips, chicken, sai dangin su pizza, da indomie da kwai, sai na bi bayansu da ababen ruwa irin su juices da yougurt ko hadadden shayi hadin kauri."
Salatin da Inna ta 'dauka ne ya sa ta dakatawa tare da tunanin ta yi subutar baki.
"Ashe duk togaciyar da na gama yi miki bai shiga kunnenki ba? A gidan uwarki kika san wadannan kayan, wadda ba ta alfahari da abin da ta bude ido ta gani a gidansu, sai hangen kayan wani da ba ya rufa maka asiri!
Nasan kina nufin idan kin je gidan miji ne kike tunanin wannan rayuwar za ki yi"
Ta kafe ta da ido tana mata kallo mai tsanani sannan ta ci gaba da cewa, "To saurare ni da kyau aure ya wuce wasa tun wuri ki cire wannan tunanin a ranki, gabadaya aure ibada ne, duk abin da akace ibada ne, to ba son ranka za ka yi ko zaka gani ba, sannan ba abin da ke ri'ke da aure gabadaya sai ha'kuri don haka ki cire wannan tunanin a ranki. ki yi fatan Allah ya ba ki miji nagari, da hankalinki zai kwanta, domin komai za ki samu idan ba kwanciyar hankali ina tabbatar miki ba za ki ji dadinsa ba Allah ya shirye ki, adduar da zan dinga miki ke nan."
Ta fada da iyakacin gaskiyarta, domin ta lura addu'a ce kawai za ta canja mata Iyah ba hantara ko nuna fishi ba.
***
MK yana isa gida ya tarar da Hajiyar Bichi ta zo, a falo ya tarar da su ita da Hajiya Babba suna cin makani wanda ba ya tantamar daga Bichi ta taho da shi, da murna ya hau fadin,
"Hajiya ashe da gaske kike da wuri za ki dawo?"
Dariya ta yi ta ce "Allah Ya yarda ban dade ba".
Suka ci gaba da hirarsu har su Abbas da Ahamad suka dawo aka ci gaba da hirar da su, Maghriba ce ta dakatar da su.
Bayan sallar Isha MK ya tarar da Hajiya Babba a dakinta, ya gama kame-kame da soshe-soshen 'keya, sannan ya ce "Hajiya so nake aje a tambayar mini izinin magana da wata yarinya a wajen mahaifinta."
Dadi ya kama ta, ta shiga fadin "Alhamdulillah! Allah Ya sa abokiyar arziki ce, ina ne gidan nasu?"
Sake kasa ya yi da kansa da kyar ya ce "A babban layin Unguwa Uku suke mahaifinta mai karamin karfi ne amma mutumin kirki ne, na san shi tun kafin nasan yarinyar."
Farin ciki ya bayyana a fuskar Hajiiya Babba ta ce, "Yanzun nan za mu tattauna da Hajiyar Bichi tunda Allah ya sa ta zo garin, gobe In Sha Allah zan je har gidan Babanku Alhaji Isa (Aminin mahaifinsu ne) na shaida masa. Sai ya je ya tambayar maka, tunda ka kammala karatun kuma ka iya harkar kasuwanci ba za mu ji tsoron aurenka ba, bare da ikon Allah da wuri za ka sami aikin yi ka ci gaba da rike mu gabadaya."
Koda ta sami Hajiyar Bichi da maganar fatan alheri kawai ta yi tare da cewa, "Hajiya Babba ai ke ce uwarsa, ni 'yar addua ce!"
Wannan biyayyar da tun fil'azal Hajiyar Bichi ke yi wa Hajiya Babba ta taimaka kwarai wurin samun zaman lafiya a tsakaninsu, tare da saukaka kishin junansu matu'ka da gaske.
A satin aka tambayo masa izinin magana da Sa'adah, a take kuma Baffa ya ce ya bashi damar ya nemi yardarta ba don yana jin tsoron halin dan yau ba, da a take zai ce ya ba shi ita, to tsoron kar ta ce ba ta sonsa ta kunya ta shi yasa ya ce idan har sun daidai ta kansu to ya ba shi, aka yi murna aka rabu ana addu'ar Allah Ya sa hadin Allah ne.