← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 113

Sashe 48

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusa da ita ya zauna yana sauraron kira'arta mai dadi, sai da ta kai Aya. sannan ta ajiye kura'anin ta mike tace "sannu da dawowa".

Ya amsa da "yauwa! Na gaji yau dinan sosai, na sha zirga zirga, ba tare da kalle shi ba, tace " wata'kila har wanka ya hau kanka".

Zuciyarsa daya ya ce "gaskiya kam idan na yi zanfi wartsake wa", ya kalli agogo ya ce bari na yi sauri na watsa ruwan kafin a kira sallah".

Ya mike ya yi dakinsa, ita kuma ta bishi da kallon tuhuma, da takaici mai yawa.

Da ya dawo bai nemi abinci ba, ta kara gasgata su Halima, ya taba jikin Jawad da yake kwance yana fama da zazzabin hakorin fi'ka, ya kalleta yace a kwance ya yini ne?"

Kai kawai ta daga masa, ya riga da ya saba da halinta na rashin bashi amsa da baki wani lokacin, dan haka bai damu ba.

Wani ikon Allah yau da wuri ya dawo, kamar yasan anshirya masa ya kwana a waje, haka suka kwana bai gane kan gimbiyar ba, ya daure, shima ya 'kyale ta.

Washagari suka tashi Jawad yana ta suma! ga wasu irin abu sun feso masa kamar borin jini, asibiti suka kai shi, aka bashi magaunguna bayan anmasa allurai, sunje siyan magani, suka tarar da Farida a pharmacy din, da azama ta zo gunsu ta karbi Jawad da yake hannun sa ta dudduba jikinsa tana fadin "Abban Jawad wannan ai 'kyanda ce(measles)".

Da kanta ta hado maganin da aka rubuta musu, har ta kara musu da wani sabulu da zai taimaka wurin baje fatar.

Lokacin da take yiwa Mk bayanin maganin da yadda za'ayi amfani da su, Allah kadai yasan yadda zuciyar Sa'adah ta ke tafasa, ko da Farida ta karaso fuskar Sa'adah a daure ta gaisa da ita, har Mk yaji kunyar yadda ta mata a gaban jama'a.

Ya mika kudin Farida ta ce "A a Uncle ka barshi, da dai na Gogel ne sai na barka ka biya! Amma ai Jawad 'dana ne nima", ta fa'da da sigar tsokana da wasa.

Ya yi godiya ta rakasu har mota, ya karbi Jawad a hannun ta, ya mika ma Sa'adah ta hakince a gaban mota, suka tafi.

Suna Isa gida bata jira ya gama daidaita parking ba, ta dauki ledar maganin da Jawad ta fice.

Tana kwantar da Jawad da yake ta barci tunda aka masa allura, ta samo biro, ta yiwa magaungunan nan shaida ta yadda ita kadai zata gane, ta daure ta ajiye su.

Ya shigo ya zauna, yana son yi mata magana amma ganin yadda ta 'daure fuska tamkar wadda ya zagi iyayenta, yasa ya mi'ke yana cewa " na tafi! Dan Allah kar kiyi wasa da bashi magani".

Ci kanka ba ta ce ba, ya gaji da tsayuwursa ya fita, yunwar da yake ji dole ya fita da abarsa, dan yasan tunda take wannan fishin ba yi zata yi ba, yasan ganin Farida ne ya sake tunzuro ta, tunda tun jiya take ta faman 'kunci, a ransa yana ayyana da jiya kuma ta ganshi yana taimaka wa kanwarta da ta samu admission zata karanta economics fa? Farida ba tasan komai a new side ba, tunda ita a old side take karatunta, shikuma sai ya rakasu a kokarinsa na kyautata mata kamar yadda take girmama shi a matsayin malamin ta.

Shi bai san har anzo anfesa mata ba.😄

Da yamma ya dawo, ya ya tarar da ita goye da Jawad, kayan da ya barta da su ya dawo ya same ta da su. kallo daya ya mata, ya gane bata ci komai ba, sannan bata yi wanka ba.

Ya rasa gane wannan masifar da ta 'dorawa ranta, da 'kyar ta bude baki ta ce "Sannu" ya amsa da yauwa ya isa bayanta yana duba Jawad da yake ta Nishi, shi dai ta masa wanka fes yake, sai dai jikinsa kamar wuta.

"Kin bashi maganin kuwa? na ga jikin, har yanzu bai sauka ba".

Ko kala ba ta ce ba, ya isa inda ledar maganin take ya bude ya ga ba wadda aka taba, bare a sha.
Ransa ya baci matu'ka da gaske, ya nunata da yatsa ya ce " Wai ke wacce irin yarinya ce marar mutunci?"

Ta yi 'kasa da kanta tamkar wadda ta saduda, yaci gaba da fadin "kin fara kaini bango Sa'adatu, kullum a cikin zullumi nake zaune da ke, masifar yau daban, ta gobe daban, haka ta jibi".

"Ai kaci moriyar ganga, sai ka kawo karshen zaman zullumi Mk" ta fada kanta tsaye.

A razane ya zuba mata ido, yana kallon ta, itama ta kafe shi da idon da suka cika da 'kwalla ba alamun tsoro ko shakka a cikinsu.

Ya kasa cewa komai, dan kuwa a yadda yake jin bacin rai zai iya na'da mata dukan tsiya, abin da baya fatan ya aikata kenan, dukan matar aurensa.

Ya mika hannun yana fadin "bani yaron, kai tsaye ta ce "idan kai ka haifar min, ba sai ka 'kwata ba".

Ya yi kanta yana fadin "Me kika sha ne? Bari na sauke miki iskancin da kike fama da shi".

Ga mamakinsa ko motsi ba ta yi ba, sa'banin da, idan ya mata irin haka take kwasa a guje ta 'buya.

Ya isa kusa da ita ya kama kafadunta ya girgiza da karfi har sai da Jawad ya motsa, ya ce " fada min me yake faruwa, me na miki har ya shafi wannan yaron da bai san komai ba?".

Tsaki ta ja, tare da fizgewa, ta koma gefe tana sake 'daure goyonta sosai.

" What! Ni Kika yiwa tsaki Sa'adatu? abin da kinfi kowa sanin na tsani a mini?"

Ai kuwa ta sake jan wani fiye da na farko, sannan tace " ka kashe ni! an maka tsaki Mukhtar".

Wani irin shock ya kama shi, a farko da tace Mk gatsal mamaki ta bashi, amma a yanzu da ta ambaci cikakken sunan sai ya gane ashe Mk din a mutunce ta fa'da.

" Allah ya tsare ni da kisan kai, duk bala'in da kike nufi na da shi, in sha Allah ba zai same ni ba".

"Tunda abin har ya kaimu ga haka, to shikenan! ki yi harkar ki na yi tawa, sauko shi na bashi maganin, sai ki mayar da shi".

"Baka ji mai nace tun farko ba? ka 'kwata' a shirye nake da mu karya yaron nan! idan har ni na tsugunna na haife shi wallahi ba zai sha wannan maganin ba".

"Ya zuba mata ido, yana jin haushin ta na samu gurin zama a zuciyarsa, ya ce "idan na siyo masa wasu zai Sha?"

"Idan na tabbatar da sahihancin su ba".

Ya dauki ledar maganin ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba".

Bai wani jima ba, ya dawo da su, a wata ledar mai tambarin lamco pharmacy.

Ya mika mata, tare da cewa "gashi" ya juya ya fice.

Ta dudduba ta tarar da su dinne, illah ledar da ya canja, ta yi 'kwafa ta dankwarar da su.

Ana idar da Isha ya dawo, ya tarar da maganinsa akan kujera ita kuma ta shige 'daki ta rufe kofar, Jawad sai kuka yake yi.

Ya duba maganin ya tabbatar ba'a bashi ba, ya hau dukan kofar, amma banda kukan yaron ba ya jin komai.

Ya kirata ya fi sau hamsin amma tamkar bata gidan.

Ya hassalo sosai ya ce "wallahi idan yaron nan ya mutu, ke kika kashe shi, da hannuna zan mika ki wurin hukuma".

Sai lokacin ta ce "yi sauri kar 'kuda ya riga ka, wato ka maida ni bagidajiya, ka fita da magani kamar gaske, ka sake dawo min dashi, idona tar yake, bazan bashi ba".

A fili ya dinga fadin "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un".

Ya fice zuwa dakinsa, yana karfafawa kansa guiwar ya rabu da ita, ai ta fishi son yaron.

Karfe shadayan dare ya dinga jin kukan yaron, da farko ya yi biris, amma da ya dinga jin 'ka'karinsa baisan yadda akayi ba sai ganin kansa ya yi a jikin kofar dakin Sa'adah yana bugawa, yana cewa "ki dubi girman Allah ki bude min kofar nan, komai na yi miki, na yarda kimin komai, amma banda yaron nan, ki ji tausayinsa, ki ji tsoron hakkinsa".

Har ya gama bilayinsa bata tanka ba, tana jin ta shirya faruwar komai ciki har da rabuwarsu.

Cikin ikon Allah, sai Jawad ya sami barci adalilin ta bashi tea, ta bashi maganin zazzabin sa da yake da shi.

Da asuba kukan Jawad ya sake tayar da hankalin Mk, ya rasa inda zai tsoma ransa, a take ya kira Hajiyar Bichi a waya, bai fa'da mata komai ba, ya ce dai kwana suka yi Jawad bai yi barci ba.

Ba bata lokaci, ta taho,har da garin kunun ko zai dinga sha, tare suka shiga falon, ya dinga kiran Sa'adah amma ta 'ki budewa, sai da taji muryar Hajiya tana cewa"Sa'a, menene yake faruwa ne?"

Da sauri ta bude 'kofar, ta fito idonta, yayi luhu luhu, yayi ja tsabar kuka.

Ta mi'ka mata Jawad ta zauna a gefe tana kuka tamkar wadda aka yi wa mutuwa.

Hajiya ta kalleta, taga ta fita a hayyacinta, ta rame farat daya, ta maida kallonta ga Mk taga shima a firgice yake.

Tace ciwon Jawad ne ya susuta ku haka, ko kuwa wata matsalar ce?"

Ya dauko maganin ya mi'ka ma Hajiya ya ce "Dan Allah ki bashi maganin nan", ta karba, ai kuwa Sa'adah ta saka uban kuka tana cewa "Kar ki bashi Hajiya".

Hajiya ta rasa maganar wa zata dauka a tsakanin su, ta dubi Sa'adah tace "Yi shirunki bazan ba shi ba, fada min me ya faru?"

Ta kasa magana sai kukan da take yi mai dauke da shesshekar ajiyar zuciya.

Ganin hakan yasa Hajiya ta rufe Mk da fa'da, ta inda ta shiga, ba tanan take fita ba, tana jaddadawa laifinsa ne, tunda Sa'a ba me fitina bace.

Ya yi shiru ya dauki laifin da bai yi ba.
da lallashi, Hajiya ta samu Sa'adah ta fada mata dalilin da bata son maganin alhalin ba expired suka yi ba.

Da rawar murya ta ce " Budurwarsa ce ta siyi maganin, akan idona suka yi zance ta siya ta bayar".
Ta karasa cikin gunjin kuka.
Chapter 48 · 0% Book details