← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 113

Sashe 40

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yinin da na yi, ba tare da kai ba, a daddafe na yi, sai yanzu na gane, ko kace na kwanan ma ashe ba zan iya ba."

Da'di ya kama shi ya ce "Har na dawo masaukinmu amma bari na zo".

Sosai suka huta, zuwan su Jos sai ya zama tamkar Honey Moon a gurinsu. Son juna ya karu a zukatansu.

Wani irin so da zazzafan kishin MK, ya cika zuciyar Sa'adah, zuwa yanzu ta tabbatar ya iya soyayya, irin wadda ma ba ta yi zaton akwai irin ta ba.

Alkalamin *SURAYYA DAHIRU*
✍🏼✍🏼.
[6/7, 11:54] Aminan Ibrahim: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*

55-56

Kwanan su uku da dawowa, jikin Sa'adah ya rikice da wani irin zazzabi da amai.

Ganin kullum ciwon gaba ya ke yi ba baya ba, yasa ya kaita asibiti, test aka ba su, tunda kan Taifod, malaria, da ciki (P.T).

Sakamakon na fitowa komai Negative, illa na cikin da ya kasance positive.

Maganin tsayar da amai da karin jini aka ba ta. Sai Panadol, tare da fadin sai a hankali za ta sami lafiya tunda jikinta na samun sauyin yanayi.

Sosai MK ya ji dadi, sai fadin Alhamdulillah yake yi har suka dawo gida.

Sannu kuwa har gajiya da amsawa take yi, motsi kadan zaicce sannu, tamkar mai nakuda.

Kwana biyu ta warware ta shiga harkokinta ba wata matsalar komai, lafiyayyen ciki ta samu komai ci take yi, ko sau nawa MK zai neme ta ba ta gajiya, wani lokacin ma ita take yin dalilin da za su hadun.

Mamakin yadda ta zama expert a wannan harkar take yi ba gajiya, har Allah-Allah take yi idan ya fita ya dawo, ko kuma dare ya yi.
Ta san mabukaciyace ita, amma ko kusa ba kamar yanzu ba. Tunda ta sami ciki, ba ta sake hadiyar Viagra, bare ta ce ko shi ne yake sababa mata yawan son sex.

Daga dukkan alama cikin ne ya zo mata da wannan salon, wadda take fatan kar ya zame mata dabi'a ta dindin, MK da'din hakan yake ji ba kadan ba, kullum a cikin fadin "Madalla da Babyn nan yake."

Cike da zumudi suke goyon cikin, wani irin kyau Sa'adah ta yi, fatarta ta sake yin laushi, ta goge ta yi tas, MK baya gajiya da kallon ta musamman yadda kirjinta ya cika dam, kugunta ya bude sosai.

Shi kansa MK ya murje farinsa ya karu sosai, kallon su kawai za a yi a san suna cikin kwanciyar hankali, da mutunta juna.

*BAYAN WATA SHIDA*

Zaune take a tsakar gida tana waya da Inna, "Inna har yau ba za ki zo kiga inda nake ba?".

Daga can bangaren ta amsa da cewa " To Baffanku ne ya hana ni, wai mai zan zo na yi miki".

"Cikin shagwaba ta ce "Na san da kin karfafa Inna da tuni kin zo, haka na sha jinya har na warke ba ki zo ba, da Anty Sumayya ce a garin nan take rashin lafiya da kin je kin ganta, amma ai ni ma Baffa ya zo ya ganni." Ta fada a sanyaye.

Dariya ta yi tana cewa "Iyah ashe dai har yanzu da saura, na dauka kin yi hankali sosai, musamman da na ga kina zaune lafiya da mijinki kuma kin tsare kanki ba kya yawo".

"To Inna yanzu na kai wata biyar ban zo gidan nan ba, tunda na ji fa'danku, ba na yawo na tsare kafata, ba sai ki dinga zagayowa kina gani na ba".

"E gaskiyar ki, to ki kwantar da hankalinki, ina tafe tunda ga Baffanku ma yana jin ki da kunnensa".

Da haka suka yi sallama ta kashe wayar, da kyar ta samu ta tashi saboda yadda cikin ya mata nauyi sosai tamkar ba cikin fari ba. Watansa bakwai, amma sai a yi zaton a watan nan za ta haihu, duk da cewar watansu takwas da aure.

A fili ta ce "Gara ki zo ki gan ni, ki ga yadda na zama".

Washegari kuwa bayan azahar sai ga Inna da yar rakiyarta Zainab Ma'aji.

Mamaki ya yi matu'kar kama Inna ko kadan ba ta san cikin har ya tsufa haka ba, ta san dai tana zargin ko da cikin tunda rabon da ta sa Iyah a idonta an kai wata biyar koma ya zarce hakan.

Ta zauna tana mamakin yadda ta aune ta zama babbar mace komai nata ya bude, da kyar take zama da tashi.

Kallon Zainab Inna ta yi ta ce 'Ashe kin kusa zama uwa amma ba labari?"

Dariya sosai Zainab ta yi tare da fadin "Inna Ina zan iya hirar haihuwarmu ta fari".

Yayin da Sa'adah ta sunkuyar da kai kasa alamun kunya.

Zainab ce ta shiga kicin ta hado ruwa da lemo ta kawowa Inna, ta sake komawa ta dauko tiren da ta gani an shirya kayan abinci a kai.

Hira suka yi, cikin walwala har Inna ta fahimci sauyin da Iyah ta yi, ta fara yin hankali.

Sai da suka zo tafiya, ta fashe da kuka, kamar wata sokuwa.

Cike da tarin kauna Inna ta sata a jikinta, tana fadin "Kukan na menene kuma Iyah? so kike ki tayar mini da hankali bayan cike nake da murnar ganin ki cikin nutsuwa da walwala, ko wani abin na damun ki ne?"

Cikin kukan ta ce "Ni so nake ki dinga zuwa".

Cikin rarrashi ta ce "Wani satin zan dawo, ai yanzu kam dole Baffanku ya bari na dinga zuwa akai akai".

Da haka ta lallaba ta suka rabu lafiya, ta raka su har gate bayan Inna ta shiga dakunan ta gani tare da sanya albarka.

Suna tafe Inna ta ce da Zainab "Ina murna Iyah ta yi hankali ashe dai da saura, indai ba so take na zama uwar zamani ba, ina ni ina zarya a gidanta?"

Dariya sosai Zainab ta dinga yi tana fadin "Mene ne a ciki Inna? Kin san Baffa ne ya hana mijinta barin ta zuwa gida, ke ba sai ki dinga zuwa ba".

"Ba ku da hankali"

Har gida Zainab ta raka Inna sannan ta tafi gidansu.

Allah- Allah Inna take yi Baffa ya dawo ta ba shi labarin Iyarsa ta kusa zama uwa.

Tunda su Inna suka tafi, ta debo kayansu da ya wanke jiya, ta zauna ta fara guga.

Ta kammala nasa tsab ta-ci karfin nata, ya dawo.

Ta fara kokarin tashi ta karbe shi, ya tsaya daga inda yake ya bude murya ya ce "Yi zamanki ki ji da kanki".

Ta koma ta zauna tare da cewa "Sannu da dawowa"

Bai amsa ba ya shiga kicin ya ajie ledar hannunsa, ya zubo abinci a plate, tare da cokula biyu.

Gefe kuma ya wanko guiba ya zubo a bowl.

Yana zama tun kafin ya yi magana ta sa hannu ta dauki gwaibar ta fara ci.

Ya kalleta ya ce
"Sau nawa zan ce miki ki daina gugar nan idan na sami dama zan yi?"

"To ina zaune haka ai bai fi motsa jiki ba, ni fa har wankin ma zan iya mana, kawai dai na bari ne saboda ka ce ba ka so.

Ya zuba musu abincin, yana fadin mun yi Ba'ki ne yau, ko kuma wani abin za mu yi da daddare?"

Tana murmushi ta ce "Yau babbar bakuwa muka yi baka nan"

Ya zuba mata ido cike da neman karin bayani.

"Inna yau dai Allah ya nufa ta zo"

Da sauri ya ce shine baki fada mini za ta zo ba?"

"Ni ma fa ban sani ba kawai ganin su na yi ita da Zainab".

"Ba ni labarin yadda ta kaya, kin saka hijabi kin boye cikin?"

Tana dariya ta ce "Ban saka ba, amma dai na ji kunya ba kadan ba, ita fa ba ta san ya girma haka ba".

Shi ma cikin dariyar ya ce "To me kika ba su da za su tafi?"

"Ban basu komai ba".

Ya rage fara'a ya ce "Kai Iyah don rowa?"

"To ai na ga farkon zuwa na na kai mata atamfa da sabulai, zuwan da na yi na karshe ma ka ba da kayayyaki na kai mata, yanzu ni kuma ba kudi ne da ni ba".

"Kudin da yake cikin durowa a dakina fa?" Ya tambayeta yana kallon ta.

"Uncle ai ban fada maka zan taba ba, sannan kuma cewa ka yi na sayayyar kayan Baby ne".

"Daga yau ban miki iyaka da komai nawa ba, akan su Hajiya da Inna, komai kika ba su ba zance don me ba?".

"Tom shike nan na gode zan gyara".

"Ina ta cin abinci baki sa hannu ba?".

"Ci abinka ni kunu zan sha, dazu Zainab ta taya ni muka yi".

"Kwana biyun nan ban san me yasa ba na son shinkafa ba".

Sai da ya kammala cin abincin ya tashi ya zubo mata kunun a katon mug, sannan ya jona gugar ya ci gaba da yi.

Suna zaune aka fara kiran Magariba, daidai lokacin kuma ya kammala musu gugar gabadaya.

Ya yi alwallah ya nufi Masallaci, ita ma ta tashi da kyar ta yi alwalar.

Kafin ya dawo ta shirya kayan su cikin durowa, ta tattare falon, ta kunna turaren tsinke na Touch Me.

Haka kwanaki suke ta shudewa har watan haihuwa ya kama, komai na Sa'adah ya sake canjawa, fuskarta, ta yi wani iri, hanci ya bude sosai, baki ya zama kato tamkar ba Sa'adah yar kwalisa ba.🤣

Ita da kanta ba ta son ganin fuskarta a madubi, MK idan ya kalle ta dariya take bashi, amma ba ya iya dariyar a gabanta, tun kwanaki da ya kalle ta ya fashe da dariya, ita kuma ta saka masa kuka mai tayar da hankali, da kyar ya shawo kanta, shike nan bai kara ba, sai idan ya fita ko ya shiga dakinsa ya yi mai isarsa.
Chapter 40 · 0% Book details