← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 113

Sashe 70

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta fada jkin Inna tana cewa "na gode Inna dan Allah ki dinga mini addua, ki mini adduar dangana ji nake zan mutu, Ina cikin kunci da ba'kin ciki mai yawa".

A tausashe Inna ta ce kin bar Allah ne, shiyasa ya bar ki, ki yawaita addu'a, ki lazimci istigifari, duk tsaurin damuwa istigifari na wanketa. ki daure zuciyarki,ki daina rokon Muutar akan ya zauna da ke a dole, fadawa Allah damuwar ki yana jin ki".

Da kuka sosai ta ce " To Inna".
sai kuma ta dinga fadin Astagafirillah da karfin gaske hadi da salatin Annabi.

"A hankali za ki yi Iyah, ko a zuci kike yi Ubangijinki ya ji ki"

Bata daina ba, haka bata rage ba, ganin da Inna ta yi tamkar ba a cikin hayyacinta take ba yasa ta fita ta 'kyaleta, tun tana jinta har ta daina ji, ta leka ta ga barci ne ya mata shigar sauri, a fili Inna ta ce Allah ka dawo wa da yarinyar nan nutsuwar ta, Allah ka tausaya mata".

Kwana biyu kullum Inna ke tausarta, hakan kuma ya taimaka gurin rage kaso mai yawa na damuwar ta, dama kuma ganin da Farida ta mata, tana tsugunne gaban Mk ne ya susuta ta, sannan ta sa a ranta soyayya yake da ita.

A 'ko'karin Inna na son ta 'kara nesanta Iyah daga tunanin Mk yasa ta roki Baffa akan ya barta ta tafi Gombe ta yi ko wata 'daya ne, ko hankalin ta ya 'dan kwanta idan tana tare da yar'uwarta.

Ai kuwa Baffa na bude baki yace "Eh ita ta'ki zaman aure sai kuma taje ta zauna gidan SUMAYYA, arasa gane wacece matar gidan a tsakanin su, wata'kila kuma idan ba sa'a aka yi ba, ta koyawa Sumayyan iyashege tunda tana ganin ita wayayyiya ce kuma me ilimi ce, sa'banin Sumayya da tasa Allah da Ma'aiki a gabanta! Ba inda za ta je nan ne dolenta, ba gidan Sumayya ba".

Da 'kyar Sumayya ta roki Baffah ya amince Iyah ta je Gombe amma da sharadin sati biyu zata yi.

Zuwan ta Gombe ya sake sa mata hakurin rashin Jawad da Babansa, duk da dai kullum dare sai ta ji'ka filonta da hawayen takaici da kewa mai yawa.

Daga sati biyu sai da ta shafe wata uku a Gombe, wadda yayi dai-dai da wattanni bakwai da mutuwar aurenta.

Ranar wata lahadi Mk da Mahmoud suka je wurin Baffa, suka gabatar masa da takardar admission din da Mk ya samowa Sa'adah A Aminu Kano college of legal studies (LEGAL KANO). Inda zata yi diploma a fannin Sharia tsawon shekaru biyu.

Kai tsaye Baffah ya ce "Mutari ba zai yiwu ba, ka sani tun tana 'karamarta ban barta ta tafi babbar makaranta ba, aurar da ita na yi, sannan kaima tsawon shekaru bakwai ba ka'dan da ta yi a hannun ka, ba ka sata a makaranta ba sai yanzu?"
Ya girgiza kansa alamun bai amince ba.

Mk ya yi kasa da kai ya ce "Allah shine shaida tuntuni na so ta fara, to makarantar da take so bata samu ba, sai na mata sha'awar F.C.E KANO. Ashe mun makara sai muka bari sai bana, to ga yadda banan ta zo mana ba yadda muke zato ba. Dan Allah Baffah ka mini wannan alfarmar, ka barta taje ta yi ilimi ai yanzu ta yi hankali ba kamar da bane da kake jin tsoro".

"Mutari ka bar wannan maganar dan kuwa bata shiga kunne ba, ba kuma zata shiga ba".

Sai lokacin Mahmoud ya ce " Hakuri zaka yi Baffah! Idan ka gamsu da gaske Mukhtar bai rabu da Sa'a da nufin tozarci ba, to ka bashi dama ta shiga makarantar nan, yadda ya dauke ka, wallahi ko aure bai gitta a tsakanin su ba, shi me yin alheri ne ga ahalinka.

Sosai su Mk suka matsawa Baffa da roko har suka shawo kansa ya amince, zata yi karatun amma da zarar mijin da ya cacanta ya fito neman aurenta to zai katse karatun, domin kuwa yafi bu'katar auren akan karatun. Jikin Mk ya yi sanyi tubus adalilin kalaman Baffah, na farko da Baffa yace ya fi bu'katar auren sai ya ji tamkar gugar zana ya masa, sai kuma kishin da ya ce idan ta sami miji zai yi aurenta.

A satin ta dawo kasancewar har fara karatu a makarantar, ba ta yi wani murna ba, amma dai ta gamsu ta fara karatun shine yafi mata alheri, zuwa wannan lokacin ta fara ha'kura da Mk! duk da zuciyar ta tafi son ta koma masa, ha'kurin na dole ne mussaman yadda Inna da Sumayya suke ta yi mata nasihar hakuri da karbar kaddara.

Ana jibi zai tafi Uk, inda ya samu gurbi a Jami'ar Bhirmingham zai yi digirin digir gir (P H.D). duk akan harshen turanci.

Baya so ya tafi bai yi sallama da Sa'a ba, haka kawai zuciyar sa ke ta azalzalar sai ya mata sallama, kunyar zuwa gidansu yake yi, ta yaya ya saketa, bai mayar da ita ba kuma ya je nemanta, me iyayenta za su dauke shi?.

Dabara ta fa'do masa, dan haka lokacin tashin Jawad a makaranta na yi ya bar koami ya 'dauko shi da kansa bai zame ko Ina ba sai legal. gefe ya samu kusa da masallaci a jikin wata bishiyar darbejiya ya yi fakin.

Ya jima a zaune a mota cikin rashin abin yi, tunda yanzu bata da waya, ko ta Inna ma bata sha'awar ri'kewa dama shi take nacin kira, zuwa yanzu kuma ta yi matu'kar rage 'kiran nasa, duk da dai idan abin ya juyo mata tana kiransa ko text me dauke da kalaman fatan alheri, da tuni akan girman ladan da me yin ha'kuri ke samu.

Ya yi zurfi, cikin tunani ya ji Jawad na cewa "Mami" da 'karfin gaske.

Ya zabura ai kuwa itace ta fito a masallaci sanye take cikin dogon hijab har kasa kalar albasa, ya sha guga, fuskarta dauke da farin glass, ba kwalliya ko ka'dan a fuskarta, sannan zuciyar ta ba sukuni amma sai ta yiwa Mk kyau.

Da sauri ta 'karaso yayin da Jawad ya balle motar ya fice ya nufeta da gudu, ta tsugunna ta bu'de masa dukkan hannuwanta ya fa'da, sakwanni goma suna haka sannan ta dago shi, ta ce "Halan biyo Malam ka yi akan dole, Na ganka da uniform?"

"A a dauko ni ya yi daga school ko gida bai kai ni ba! Ya zarce da cewa "Mami me yasa ba kya daga Ni sama irin yadda Malam ya ke mini?"

Da murmushi a fuskarta ta ce "saboda bani da 'karfi Jawad".

Maimakon ya yi shiru sai ya sake cewa "yau kin rungume ni, amma a gidan Inna ba kya yi mini haka".

"Oh Jawad! to kunya nake ji kar Inna ta ce ban da kunya".

Ya kalleta badan ya gane manufar ta ba.

Mk da ke jinsu ya bude motar ya fito, suka kalli juna, a nutse Sa'a ta gaishe shi.

Ya amsa yana cewa " ya karatun dai ?"
Ta amsa da fa'din Alhamdulillah".

Kai tsaye ta ce "wani abu zaka yi ne anan?"

kai ya girgiza ya ce "sallama na zo yi miki duk yadda nake cikin bacin rai ba zan iya tafiya ban miki sallama ba, jibi idan ubangiji ya nuna mana zan tafi ingilah, Ina fatan za ki yi karatun ki da kyau, Ina miki fatan dukkan alheri a rayuwar ki"
Da ga jin yadda ya ke magana kasan cikin rauni yake yinta.

Ita kuma tuni hawaye ya goce mata, ta yi 'kasa da kanta ta kasa furta ko da kalma guda.

Takaici ke cinta ta ko'ina, tafiyar da ya dinga cin burin dai ita da Jawad zai tafi, har ta yi karatu ta kuma haihu acan sai gashi tafiya ta zo amma ba ita. Kusan kullum sai ta ci karo da abin da ta rasa a dalilin rashin Mk.

Ya nisa ya ce " duk hidimar ki ta makaranta tana hannun Mahmoud, zaki bude account, fatana kar ki tambayi Baffah kome, ke kanwata ce, ko ba ma tare zan miki komai Dan rayuwar ki ta inganta, ina miki fatan alheri a rayuwar ki ta gaba, na yafe miki dukkan kurakuran da kika mini, fatan nima zaki yafe mini inda na musguna miki".

Ta 'dago idanuwanta cike taf da 'kwalla ta ce "Baka mini komai ba sai alheri, ban san wani abi da kai mini ba face mutunci da karramawa, nima ina maka fatan alheri, Allah ya bada sa'a ya tsareka a duk inda zaka samu kanka".

Sai kuma kuka sosai ya 'kwace mata, bai yi yun'kurin hanata ba, domin shi kansa da yake namiji ji yake tamkar ya yi ta zunduma ihu ko a fahimci Halin da yake ciki.
Idanuwansa sun yi jawur tabbacin yana cikin damuwa mai yawa.

Tsawon lokaci tana kuka kafin ya ce "it's okay ya isa haka zuwa yanzu ai kin dan samu relief, kukan ya isa haka share fuskar ki Jawad na kallon ki fa".

Ta dago ta sake kallonsa ta ce "Da gaske ka yafe mini Malam".

Da sauri ya'daga kansa yana fa'din har zuciyata".

Murmushi mai ha'de da hawaye ya subuce mata ta ce " zan yarda ka yafe mini ne, idan har ka mayar da Ni, zan gamsu da gaske ni 'kanwarka ce idan ka mini adalci irin yadda yaya zai yiwa 'kanwarsa na duk girman laifinta ba zai janye jinin da ya hada su ba. Ka mayar da ni zan jiraka ko da baza mu bika".

Ta yi shiru tana shanye kukan da yake son kwace mata.
Ta nisa ta ce "Har gaban abada ba zan ri'ke waya ba, ba zan sake mu'amala da su Halima ba, sai abin da kake da dama shi zaka yi mini Dan Allah kar ka tafi ka barni a haka".
Chapter 70 · 0% Book details