← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 113

Sashe 34

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffa dai bai ce komai ba, da'di ya cika zuciyarsa, Allah Ya kai Iyarsa cikin ahalin da suka san mutunci suke kuma rama shi da alheri.

Bai ce komai ba sai da suka mike, ya kalli Mukhtar ya ce, "Ban baka aure ba sai da na tabbatar kana da nagarta, ina kuma zaton kai din adali ne saboda ka siffantu da kyawawan dabi'u don haka ni ba na shakku a kanka. Sai dai kar ka bari jan kunnen da ake ta faman yi maka na ka kyautata mata, ya yi dalilin da za ka bari ta yi abin da ta ga dama, ka bude kunne ka ji ni sosai. Duk 'kawa ko makwabciyar da ka ga dabi'arta ba ta yi maka ba, ka shata wa matarka layin mu'amala da ita, idan ka bari ta fi karfinka to kai ne za ka sha wahalarta".

Su Baba umaru suka hada Baki wurin cewa, "Ba ma za ta bijire masa ba, ai barewa ba za ta yi gudu d'anta ya yi rarrafe ba, In sha Allah, irin halin gidansu na girma za ta yi ba *HALIN YAU* ba".

Aka rufe maganar da doguwar addu'ar zaman lafiya da neman tsari daga sharrin shaidan, da shaidanun mutane. Suka tafi MK ya bisu a baya, yana ta musu godiya tare da fadin duk abin da suka fada zai kiyaye, bai juyo ba sai da motarsu ta bace wa ganinsa. Sannan ya bi bayansu zuwa bakin titi ya karbo gasassun kajin da tun yamma Mahmoud ya yi masa booking, ya hado da yougurt din L & Z da kuma lemon 5alive, yana tafe yana ayyana bai taba ganin nisan bakin titi zuwa gidan nasa ba sai yau. yana isa ya rufe gidan.

Kamar a guje ya fada falon! ya tarar da ita zaune a inda suka bar ta, tana rufe ruf cikin lafaya.

Gefe daya ya ajiye ledojin hannunsa, ya isa kusa da ita ya tsaya, a zuciyarsa yake ta fadin Alhamdulillah! sannan ya sunkuya ya 'dago ta tare da fadin , "Assalamu alaiki! Barka da zuwa gidanki, ina miki murnar wannan rana mai cike da farinciki".

Ta yi shiru, ta kasa amsawa saboda yadda zuciyarta, take a cunkushe da alhinin barin gida.

Ya ri'ke hannun ta yana janta zuwa cikin 'dakin da shi ne mallakinta, a bakin gadon ya zaunar da ita tare da fadin, "Haka na ga ana yiwa amare." Yana warware mata laffayar zuwa kafadarta, fuskar ta masa kyau duk da ta kode saboda kukan da ta ke yi. Kusa da ita ya zauna sosai har jikinsu na gogayya da juna ya dan ri'ko ta ya ce, "Kukan na mene ne tamkar ba gidanki za a kawo ki ba, ke da kika yi sa'a a gari za ki zauna duk lokacin da kika so zuwa gida, zuwa za ki yi to menene abin kuka sai ka ce ba gidana kika dawo ba".

Tissue ya dauko a kan madubi ya shiga goge mata fuska, yana ta fadin maganganu masu taushi.

Ya kalli agogo ya ga tara saura,ya mi'ke ya dauko ledar kajin da ya bar su a falo, sai da ya shimfida musu abin zama sannan ya janyo ta ta sau'ko 'kasa, ya bude ledar ya tura mata gabanta yana cewa, "Nasan tun safe ba komai a cikinki. Taimake ni ki ci"
Ya zabura ya nufi kicin ya samo 'yar roba ya wanke hannu sannan ya zubo ruwa a ciki ya dawo, da rarrashi da hikima ya sa ta cin kazar nan, har ta manta ita ba'kuwa ce, dama kuma azabar yunwa ce a cikinta. ya sake lallabawa ya tura mata yougurt, sai da ya ga ta nutsu sosai sannan ya kalle ta ya ce, "Ga toilet nan ki shiga ki yo brush ki dauro alwala"
Ya mike yana fa'din ni ma bari na yi alwalar.

'Kirjinta ya buga fargaba ta kama ta yau gata a daren farko da ta ke karantawa a cikin littafai ko ya ya nata daren zai kasance?

Har ya dawo tana zaune a inda take.

"Kin yi alwalar kuwa?"

Shiru ta masa ya tabbatar ba ta yi ba sai ya ce, 'Tashi mana!" Ya sa hannu ya 'dago ta, sai da ya raka ta har kofar bayin da ke cikin dakin sannan ya dawo yana tattare kayan da suka yi amfani da su, ya shimfi'da musu sallaya ya koma gefen gadon ya kishingi'da yana jin matsanancin bege na ratsa shi.

A bandakin ta tarar da sabon brush da makilin, sai da ta wanke bakin sannan ta 'dora alwalar sai kuma ta tsaya a bakin 'kofar ta kasa fita. Wata irin fargaba ce ke haniniya da ita.

MK da ya ga shirun ya yi yawa, sai ya tashi ya tura kofar ganin ta a tsaye, yasa shi yin turus, bai ce komai ba ya ru'ko hannunta yana fadin, "Ba na son ba'kon yanayin nan da nake gani tare da ke a yau".

Laffayar ya mi'ka mata ta fara kokarin na'de jikinta, ya kalle ta ya ce, "kin ga ba sai kin yi wannan na'din ba, kawai ninka ki yafa".

Ba ta musa ba saboda yadda bakinta da jikinta suka yi mata nauyi ainun.

Ya ja su, suka yi sallar da Annabi ya kwa'daitar da sabbin ma'aurata su yi. Bayan sun idar ya ri'ke goshin ya yi addu'a sosai, tana amsawa da amin a cikin zuciyarta. Suna shafa adduar ya mike ya fita! bai jima ba ya dawo bayan ya rufe 'kofar falon tare da kashe fitila da fanka, kasancewar farkon damina ne yanayin zafi ne.

Yana shiga ta kalle shi da gefen idonta saboda yadda kamshin sa ya sake cika dakin da hancinta, ta ga ya sauya kayan jikinsa zuwa farar jallabiya sabuwa 'kal. Hannusa ri'ke da wasu kayan, kai tsaye ya isa kusa da ita ya m'ikar da ita ya cire mayafin ya wurgar da shi, ya zame dan'kwalinta!dogon gashinta da ya sha gyara na musamman ya bayyana, ya kasa cigaba da dauriya ya fizgo ta jikinsa ya sa hannunsa biyu ya rungume ta sosai tamkar zai mayar da su halitta guda.

Ba ita ba, shi kansa jikinsa 'bari ya ke yi, 'kamshin man gashinta da na jikinta da kuma nasa kamshin suka hadu guri 'daya suka sake rikita shi, hannunsa sai kai komo ya ke yi a bayanta cikin wani irin shau'ki mai rikitarwa.

Ta yi luf a 'kirjinsa jikinta sai 'bari ya ke yana sake rikicewa da sa'kon da ya ke kar'ba.

A kunne ya ke rada mata "please hold me Sa'adah, sa hannu ki ri'ke ni don Allah!"
Cikin wata irin murya da ba ta san shi da ita ba yake ro'kon.
Kunya da tsoro suka sa ta kasa koda 'kwak'kwaran motsi balle ta iya masa abin da ya ke ro'ko.

Da 'kyar ta samu ta zame daga jikinsa ta koma bakin gado ta zauna kunyar duniya ta rufe ta.

Murya a da'kushe sosai yace, "Ga rigar barci tashi ki saka".

Kai ta sunkuyar 'kasa tana kallon 'yar guntuwar rigar da ba ta da maraba da abin tatar koko, ta ya ya za ta iya sanya wannan rigar, ko a ina ya samo ta?

Ganin ba ta da niyyan tashi ya matsa kusa da ita ya 'dora mata akan cinyarta tare da fadin, "Tashi ki saka don Allah"
Ta 'daga taga lalacewar riga ta wuce ma yadda ta ke tunani, da sauri ta ajiye ta tana fadin "Ni ba zan iya sawa ba, ba na son ta".

"Ni ina so! kin san tun yaushe na siya miki na ajiye? Kullum addu'a nake Allah ya kawo mini ranar da zan gan ki a cikin ta.

Ta shagwabe fuska ta 'daga rigar da sauri ta mayar ta ajiye, ita rigar ma kawai kunyata take yi, balle kuma a ce ta saka, kanta a kasa ta ce "Ka yi hakuri ni ba zan iya sawa ba".

Nan da nan ya ci laya, "Wallahi sai kin saka na gani".

Ya fada a dake! gabanta ya yanke ya fa'di ta shiga bubbuga 'kafa, tana 'kananun kukan da babu hawaye, hakan da ta yi ya sake 'kawata masa ita, ya sake matsawa kusa da ita sosai, ya yi 'kasa da muryarsa ya ce, "Rufe idon ki ni sai na sa miki da kaina".

"Ni dai ka yi hakuri ka bari".

"Amma kin ji na rantse, so kike tun yanzu ki fara 'ba ta mini rai, ki fara kwasar zunubi?"

Kai ta girgiza, ya ce, "To ki bar ni na yi abin da nake so, tun yaushe nake ha'kurin ki zama halaliya ta".

Ya fara zuge zip din rigarta ta ri'ke da sauri, tana fadin "Ka kashe fitila to".

"Idan na kashe fitila me zan gani?"

Ta yi shiru tana jin tamkar kasa ta tsage ta shige. Ta kasa kallon sa a raunane ta ce, "Ka juya to, ya yi murmushi ya ce, "To" Ya juya mata baya.

Kan dole ta sanya rigar amma ta kasa cire kayan ciki! Ta kuma lullube jikin da mayafi.

Jin ta daina kiciniyar sanyawa ya sa shi cewa "Na juyo?" Jin ta yi shiru ya sa ya juyo gabadaya, sai dai ganin ta a lullu'be kuma a takure ya sa shi fa'din "mene ne haka kuma?"

Ya isa ya mikar da ita tsaye ya fara janye mayafin, ita kuma ta 'kan'kame 'kirjinta da dukka hannun ta biyu. Ya juya ta bayanta ya ga yadda rigar ta kama ta, shape din surarta ya fito sosai. Da 'kadan ta rufe mazaunanta 'yar guntuwa ce sosai, mai kuma kama jiki, rashin kirkin rigar ya kai 'kurewa.

Tsayawa kawai ya yi yana kallon ta yana fadin "Ma Sha Allah kin yi mini fiye da yadda nake so".

Jin yana 'kokarin 'daga rigar sama sai ta yi maza ta saki 'kirjin ta ruko kasan hakan ya ba shi damar juyo wa ya kalli 'kirjin ta. bai ce komai ba kawai ya ci gaba da tasbihi, ya jawo ta ya rungume ta sosai fiye da rungumar farko.

A haka ya dangana su da gado, ya sa hannu ya kashe fitila, hasken bandaki ya ragewa dakin duhu, ya cire rigar da ragowan kayan ya wurgar.
Chapter 34 · 0% Book details