← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 113

Sashe 31

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Sa'adah ya yi sanyi kalau, ta yi shiru amma hawaye bai daina zubo mata ba, tana jin tsanar Khalil sosai a ranta duk shi ya janyo mata wannan tashin hankalin, da ya ajiye ta a hanya ai da ba wanda ya ganta, ga fushin Uncle MK, ga fishin Baffa duk da dai shi mai yawan yi mata afuwa ne. Amma yau har zane ta Inna ta yi, ba za ta iya tuna yaushe rabon da Inna ta dake ta irin haka ba.

A darare ta shigo ta shige dakinta, ta fito da shirin wanka, sai da ta fito ta shirya, sannan ta je ta tambayi abincinta, ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ban yi dake ba tabbatacciya! Kina kwance na tashi na yi komai saboda zuciyarki ba imani balle tausayi, amma har ki iya cewa ina abincinki? Saboda ga baiwa kin ajiye, to ga tuwo can da kika raina sai ki hada wuta ki 'dumama, idan kuma kin fi nan sai ki zo ki dora abincin rana idan kin gama sai ki ci."
Tana kaiwa aya ta ja bakinta ta tsuke.

Cikin rawar murya ta ce, "Me zan dora?"

Kamar ba za ta kula ta ba sai kuma ta ce, " Dambu!"

Hawayen da ta ke matsewa ya balle tasa gefen dan'kwalinta ta goge, sannan ta ce, "To!"

Haka ta hau aikin sarrafa dambu tana goge hawayen da ya'ki yankewa ta san dan a musguna mata yasa aka 'kir'kiri yin abincin da zata jima bai kammala ba. Ba ta sami kanta a hannun Inna ba sai wajen karfe uku, saboda yadda ta'ki sa mata hannu, ada idan za su yi dambu kusan Inna ke jagorantar yi, kawai sai dai Sa'adah ta sa ido tana lura tare da gyara gyada ko zogale.

Amma na yau komai sakar mata ta yi, ta kuma kara yawansa a cewar ta za ta aika wa makwabta, ita dai Sa'a ba bakin musu saboda a tsorace take da ita don ba karamin duka ta mata ba.

Faranti guda ta cika da danbun ta debi ruwa a randa mai sanyi ta sami inuwar bishiyar dake tsakar gidan, ta fara ci hannu baka hannu kwarya tamkar ba Sa'adah mai cin abincin a gayance ba.😁

Inna na kallon ta a ranta ta ce, "Ja'ira yau kin gane yunwa ba kanwar uwa ba ce."

Sai da ta share abincin nan tas ta yi gyatsa gumi ya karyo mata, ta yi Hamdala. Ta jima a zaune a gun, sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan ta cika bokiti da ruwa, ta jira Inna ta fito a bandakin sannan ta shiga wanka.

Sai da ta yi sallah sannan ta shirya, kana kallon ta kasan zuciyarta ba walwala, tana zaune waya a hannu tana ta kiran MK amma ya ki dauka, lamarin da ya sake dugunzuma damuwar da take ciki, a fili ta ce, "Me yasa nake son mutumin nan ne?" Ta sunkuyar da kai tana tunano adadin yadda take shiga damuwa saboda shi.

Haka ta ci gaba da kira ba kakkautawa har ta gaji. Sai kuma ta koma tura text din ban hakuri da maganganun soyayya masu taushi. Amma ko sau daya ba ta ga amsa ba duk kuwa da sun nuna mata sun yi delivered, (Watau sun je).

Wasa-wasa sai da aka shafe sati biyu ba ta ji daga MK ba idan kuma za ta yini tana kira ba zai dauka ba.

Abin ya yi matu'kar tayar mata da hankali tun tana boyewa har abin ya fara fin karfinta, ta zama wata iri, ko abinci ba kasafai take iya ci ba. Ga Inna ba sakar mata fuska take yi ba, abin ya hade mata biyu, ta fara ramewa a tsaye.

***

Bangaren Mk kuwa ba karamin zafi ya dauka da Sa'adah ba, kwana biyu ya yi a kwance yana fama da ciwon kai da wani irin zafi a cikin kirjinsa. Idan ya tuna yadda Sa'adah ta fito a gaban motar Khalil jikinta a dame sai ya ji tamkar ya shide, haushin ta yake ji ba ka'dan ba, gara ya gan ta da Alhaji Mamman akan wannan dan iskan yaron, so yake ya hakura da Sa'adah amma kunyar mahaifinta yake ji musamman yadda ya girmama lamarinsa.

Sannan ya san ko giyar wake yake sha bai isa ya tunkari iyayensa maza da maganar ya fasa auren ta ba, ya rasa inda zai tsoma ransa. Yana ganin yadda kiran ta yake shigowa wayarsa ba adadi. To me za ta ce masa? Ta je su karata da wanda ta zaba.

Kwanaki na ta shudewa, damuwar da Sa'adah ke ciki na sake karfafa, tsawon kwanaki ashirin ke nan MK bai dauki kiranta ba, balle kuma shi ya kira.

Ranar wata Laraba da daddare suna zaune da Inna a tsakar gida amma kowa na gefensa, Yan NEPA suka kawo wuta, daidai inda Sa'adah ke zaune hasken ya fi karfi, Inna ta zuba mata ido tana kallon yadda ta lalace ta birkice. Nan da nan tausayin ta ya kama ta, sai dai ba ta nuna mata ba, amma ta kudiri aniyar yi mata sassauci.

Washegari kuwa da walwala ta amsa gaisuwar Sa'adah, ta daina daure mata fuska, idan ta mata magana cikin dadin rai take amsa mata, sab'anin lokutan baya da hantara ce a tsakaninsu.
Afuwar da Inna ta yi mata yasa ta samu sau'kin halin da take ciki, amma har yanzu ba ta da kuzari da walwala, Inna da kanta ta ce mata, "Idan ban manta ba na kai wata ban ji Muutar ya zo ba."

Sunkuyar da kai kawai Sa'adah ta yi ta kasa cewa komai! Amma idanuwan ta sun kawo 'kwalla.

Ganin yanayinta ya tabbatar mata akwai matsala a tsakaninsu ta ce, "Hala kin sallame shi saboda ba zai miki lefe ba?"

Da sauri ta ce, "Haba Inna! Ni wallahi ban sake tayar da maganar ba."

Cikin takaici sosai Inna ta ce, "To labarin abin da kika aikata ya same shi."

Ganin hawaye ya kwace ma Sa'adah ya sa ta hadiye fa'dan da za ta fara yi mata, sai ta bige da fadin, "Kadan ke nan a cikin sakamakon da mai yin 'karya ya ke fuskanta."

A ranta kuma tana raya dole su yi magana da Baffa akan rashin zuwan MK shirun ya yi yawa.

Washegari Zainab ta kawo mata ziyara, suna zaune kan katifarta, "Sa'adah me yake damun ki haka?" Zainab ta fada cike da mamakin ramar da ta ga Sa'adah ta yi.

Bata boye mata halin da take ciki ba, ta zayyane mata komai.

Cikin takaici Zainab ta ce, "Ai indai kina biye su Safina sai sun kai ki sun baro, ka'dan ke nan."

Tana kuka ta ce, "Ni yanzu ki nemo mini mafita don Allah!"

"E ai yanzu da yake ta kwabe miki za ki neme ni, amma lokacin da kika bi su ai ban sani ba."

Waya ta mi'ka wa Sa'adah tana fadin, "Saka lambar Uncle Mukhtar din mu kira shi da layina." Jikinta na rawa ta karba ta hau jera zababbun lambobinsa, tana fatan Allah ya sa ya dauka tunda har layinta da bai san da shi ba ta sha 'kiran ba ya 'dagawa.

Cikin Sa'a kuwa ya dauka! Zainab ta gaishe shi, ya tambayi wacece?
Ta amsa da gabatar da kanta, sai ta shiga ba shi ha'kuri a madadin Sa'adah, ya yi shiru har ta gama.

Ya yi murmushi mai sauti sannan ya ce, "Ba dan ina ganin hankalinki ba da ba zan saurare ki ba. Ki yi hakuri, ki cire kanki a cikin wannan maganar, ba zan iya da halin yarinyar nan ba, duk yadda nake zaton ta ta wuce nan". Yana fadin haka ya katse wayarsa.

Bugun da zuciyarta take yi ya sake tsananta, a rikice ta ce "Zainab mai yake nufi? Ya fasa yi da ni ke nan?"

Cikin son ta kwantar mata da hankali ta ce, "Ba fasawa zai yi da ke ba In Sha Allah! Kawai ya yi fishi ne sosai, ai kema kin san ba ki kyauta masa ba."

Ta dade tana kwantar mata da hankali, kafin ta mata sallama ta tafi da al'kawarin za ta sake tuntunbar sa.

Kwanaki biyu da zuwan Zainab, Anty Sumayya ta yi waya Sa'adah ta je ta karbo mata sa'ko a karkasara gidan kawarta.

Akan dole Inna ta barta ta fita bayan ta sha jan kunne da nasiha iri-iri akan kar ta biya ko ina, har kunya ta kama Sa'adah ta na jin ita ta janyo wa kanta rashin yarda a idon iyayenta.

Tana karbo sakon ta juyo, duk da yadda Anty Walida ta yi nacin ta zauna ta karasa yi mata yinin, ita kuma ganin biyu da rabi ta yi yasa ta gaggauta fitowa dan ta zartar da kudirinta na son ganin Mk a yau.

Kai tsaye FGC Kano ta sauka, sai dai ba makarantar ta shiga ba, gangare can gefe ta tsaya inda suka ta'ba tsayawa da shi, ta san kullum ta nan ya ke bi. Cikin sa'a kuwa ba ta dade tana jira ba ta hango shi, yana doso inda take, a kafa yake tafiya. Ta ce, "Ko ina ya baro dan mashin 'din?"

Sanye ya ke cikin 'kananun kaya yana rataye da jakar da yake zuba takardun shi, ya mata kyau sosai duk da ta ga ya dan zube kadan.

Sai da ya wuce ta sannan ta bi bayansa, jin ana ta bin bayansa yasa shi jiyowa, ba zato idanunsu suka sarke, ya hade girar sama da ta kasa tamkar bai ta'ba dariya ba, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa tamkar bai gan ta ba.

Sai lokacin ta yi magana "Uncle na yi kewar ka, idona sun yi kukan rashin ka!"

Ya ji ta sarai, bacin ransa ya dawo sabo, ya rasa wane matakin zai ajiye Sa'adah, duk inda ya ke ajiye ta, yau ya tabbatar masa ta kere gurin!har ta san ta bi saurayi gun aikinsa?

Ita kuma ganin bai kula ta ba har sun fara hango titi sai ta fara masa kukan da babu hawaye tana kuma fadin "Zuciyata ba za ta iya daukar fishinka ba, ka kalle ni ka ga yadda fishinka ya ramar da ni, ba na iya barci, ba na iya cin abinci, kamin afuwa, don Allah ba don halina ba!"

Ta fada cikin wani irin yanayi mai motsa ZUCIYA.
Chapter 31 · 0% Book details