← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 113

Sashe 47

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce "Duk kawayen na ki fa'da mini me kamar Jawad? fa'da mini mai miji irin naki da yake tsananin son ki".

Ta yi shiru tana jan hanci, sai kuma ta ce "su ai ba'a tauye su ba, ba a rufe su a gida ana shirin tsofar da su ba".

Ya yi shiru, yana nazarin maganganunta, da ya tabbatar kitsa mata aka yi.

Ya sake fadin yanzu zaman aure ne ya zama abin kashe wando da tauyewa a gurinki? duk yadda Allah ya miki ni'ima, kin raina?"

" Kawai ni son kanka ne ya dame ni"

Mai na yi miki na son kai a zamantakewar mu?"

"Gasu nan kala kala, ka sani haihuwa dole, sannan ka rufe ni a gida, kai kuma kullum kana ganin yanmata, wataran sai inji zaka w amarce da mai degree".

"Su Halima sun zo too nan ko?"
Ya fada ba tare da yasan a fili ya fada ba.

"Ba su zo ba".

"Hmmmm! kawai ya fa'da ya fara lalubarta a kokarinsa na son ya kawar da bacin ran dake neman taso masa.
Ai kuwa ta buge hannun sa tana cewa " Dan Allah ka bari, kullum aikin kenan, ka fitine ni da daddare, danka ya tsotse ni da rana, ga kuma wadda yake cikima bai barni ba, so haba da wanne zan ji".

Ai kuwa hakurinsa ya 'kwace ya ce "Duk ma wadda suka zo suka miki famfo, ke kuma kika yarda ina tabbatar miki kidahuma suka mayar da ke, sannan maganar karatun da kike ganin sun tsere miki da shi, su a gidajen iyayen su aka basu damar su yi".

Maganar ta mata ciwo ainun a harzuke ta ce "wato ni iyayena basu bani dama ba kenan?"

"Eh" kawai yace ya tsuke bakin sa, ai kuwa ta kara 'karfin kukanta, tana ta yunkurin tashi amma ya danneta ya'ki bata dama.

Sosai suka yi rikici, saboda ya ki amincewa da ra'ayin ta, na ta yi jamb a wannan shekarar.

Sai dai kan dole ya ajiye nasa fishin, Yana fadin ta yarda da shi, bazai taba juya mata baya ba, ita kanta yake so ba wani abu na kyan surarta ko zurfin ilimi ba.
indai zata biyewa maganganun wasu, ba abin da zata ci ribarsa a rayuwar ta, ko karatun take yi, wasu sai sunce ta 'ki aure da sauran maganganun marasa Da'di.

Sannan ba abin da yake ruguza Jin dadin zamantakewar aure irin ka bawa wasu dama su shigo cikin matsalar gidanka.

Tun a daren suka shirya, ya saukar da ita, daga famfon su Halima.

Haka rayuwar ta cigaba da gungurawa da su,har Allah ya sauki Sa'adah lafiya, ta haifi kyakkawar yarinya mai kama da ita kwabo da kwabo, sai dai yarinyar da lalura ta zo, ko kuka bata yi ba.

Aka ri'ke su a asibiti, ko numfashi sai da oxygen take zuka, kwanata biyu tace ga garinku nan.

fadin irin tashin hankalin da Sa'adah ta shiga ma, bata lokaci ne, domin tunda ta dora ido akan yarinyar nan, sonta ya shigeta fiye da na Jawad.
Ashe mai gajeran kwana ce.

Kan dole ta ha'kura, ba kunya ta karbi Jawad a hannun Inna ta cigaba da shayar da shi ba tare da an ro'ke ta ba.

Mk ya dinga tarairayarta da lallashi, da nuna soyayya har ta warware ta cigaba da jegonta cikin salama.

Da yardarsa da amincewarsa suka je asibiti aka aunata, aka dora ta kan maganin tsarin iyali da ya dace da jininta, duk dan ta samu ta huta ta gyagije, shima ya samu hutawa da ita, da sau'kin gorin da ta ke masa na ya maida ta akuya😃.

*SURAYYA DAHIRU*.
✍🏼✍🏼
25/03.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

63/64.

*Shekara daya a gaba*.

Zuwa lokacin shekarun su uku da aure, a shekarar Allah ya yiwa Hajiya Babba rasuwa, a dalilin ciwon siga da ya kamata, ba'a gane da wuri ba, har ya taba kodarta, kwananta uku a asibiti ta rasu! mutuwar da ta gigita dukkan yan gidan su Mk dama wadda yasan Hajiya, barin Hajiyar Bichi da akayi zaman makoki ita tana gadon asibiti.

Kwarai suka shiga alhinin rashinta, sai dai ita mutuwa duk yadda zaka yi, ba zata dawo da mutumin data dauka ba, dole aka ha'kura aka bita da addu'a.

Mafarin dawowar Hajiyar Bichi Kano gaba'daya kenan, kullum ta Allah sai ta yi kukan rashin Hajiya, ko na ido, ko na zuci, karshe sai ta musu addu'a tare da mijinsu, tana fatan itama ta riske su cikin aminci.

Mutuwar Hajiya Babba yasa Hajiyar Bichi ta gane abubuwan da Hajiyar ta kare , mussaman na rashin tasowar fitina a tsakanin yaran, tunda ta kwanta dama, yaran gidan kansu ya fara rabuwa mussaman manyan yaransu mata na 'dakin Hajiya Babba, da suke ganin dama kamar mallake musu uwa Hajiyar Bichi ta yi, kawai Samira a cikinsu bata biye musu to kuma itace karamar su.

Haka Hajiyar Bichi take ta ha'kuri da su tunda dai uwarsu ba abin da bata mata na alheri ba, duk yadda suke 'da'darewa da ita, yi take yi kamar bata gane manufar su ba, Abbas da Akil ne basa bata matsala, ko dan su maza ne?

Su Halima sun sami nasarar samun admission, dan haka ba sosai suke zuwa gidan Sa'adah ba, saboda sun koma new side.
Amma duk ranar da suka sami sararin zuwa gidanta sai Mk ya gane saboda yadda take daukan sabbin dabi'u.

Ranar wata litinin Safina da Halima sunje students affairs na cikin Jami'ar, gun a cike da dalibai kowa na yin abin da yake gabansa.

Suna daga can baya, kamar ance da Safina 'daga kai, sai ta hango Farida Torondi, da Uncle Mk na Sa'adah, da wata da bata ganeta ba.
A hanzarce ta zunguri Halima da hankalinta ke kan waya ta mata nuni da abin da ta gani.

"Munafiki dama ai nasan cin amanar Gogel yake yi, marar mutunci, ba dama aje gidansa ya dinga 'dacin rai da muzurai kenan, banda rashin gaskiya, menene na zargin mutane suna zuga maka matarka, ai dan yasan yana rashin gaskiya a waje ne".

Kafin su kammala, har su Farida sun gama sun fice tare da Mk.

Halima so take su wuce gidan Sa'adah, yayin da Safina tace ita ba zata iya zuwa ko'ina ba tare da taci abinci ba, dan haka suka zarce capteria.

Anan ma suka sake yin tozali da Mk da su Farida suna cin abinci suna hirar su cikin nisha'di.

Suka kewaye su, suka tafi can baya suka zauna, ta inda su Farida baza su gansu ba, yayin da sukuma idonsu na kan duk motsin su, suna daukarwa Sa'adah rahoto.

Halima fadi take "wannan mutumin mugune, ya rufe yar mutane ya hanata fahimtar komai. ashe shi yana nan yana sheke ayarsa"

Safina ta furzar da hucin takaici tace saboda Allah kiga ya hanata karatu, shima daf yake da ya kammala Masters dinsa, (Jami'ar ce ta dauki nauyin karatun nasa). Sannan yana tarayya da mai yin degree a fannin hada magunguna (pharmacy), above all daga rich family ta fito, oh Allah sarki! na tausayawa poor Sa'adah".

"Ka'dan kenan a sharrin namiji" inji Halima da take jin tamkar taje ta rufe su da duka.

Suna zaune suka ga su Mk sun mike, sun fita, a motarsa ya 'debi su, kuma Farida ce ta shiga gaban motar.

Ba'kin ciki ya kamasu da gaske suka ji, suna taya kawarsu kishi, Safina tace "takaici na daya, da bamu samu damar yiwa Gogel bidiyon su ba".

Halima ta amsa da cewa "wlh kuwa basirar yin hakan ba ta zo mana ba"

Daga capteria, basu zame ko ina ba, sai gidan Sa'adah, suka kwashe komai suka fa'da mata, a kokarinsu na tserar da ita daga cin amanar namiji, ita kuma bata gane duk mai zuwa ya fa'da maka abin da zai ruguza farin cikin ka, ba masoyi na hakika bane, mai sonka idan yaga abin da zai tayar maka da hankali! 'Boye maka yake yi mussaman a fannin auratayya tunda dai kowa yasan namiji is entitled to 4 wives, dan angan shi da budurwa matu'kar ba ba'dala suke yi ba Ina ruwan ki?

Kuka ta dinga yi, tana fa'da musu kwanaki biyun nan wulakanci ya ke tata mata, ya tsiri ya yi wanka da magariba ya she'ka kwalliya ya ce mata ya tafi shago, ba zai dawo ba sai after 11.

Suka hada baki wurin cewa "karya yake miki ba wani shago, wurin Farida yake zuwa, yau munga zahiri".

Safina da ta fi Halima kishi tace duk ranar da ya wuce goma na dare bai shigo ba, ki rufe gidanki, ya koma can su kwana tare, ai dan ya ganki sanyi kalau ne ya samu damar yin wani abin"

"Wallahi kisan me kike ciki akan makaranta, baya son ki dinga ganin mai yake yi, shiyasa yake ta miki yawo da hankali akan karatunki, oh mai za'a yi da irin su Mk".

Ita dai banda kuka ba abin da take yi, tana jin wani irin kullutu ya tokare mata wuya da zuciyar ta, ya sababa mata nauyin kirji, da kyar take zuko numfashi.

Haka suka tafi suka barta da kunan rai, suna jaddada mata tasan matakin dauka akan mijinta🤔

Wawiyar kuma ta cika fam! tana jin yau ko yafi gyatumarsa kokari, ba zai yaudare ta da kalamansa na yaudara ba, ya maida ta wata nympho, da sun fara rigima sai yasan yadda ya yi suka kusanci juna shikenan sai ya kashe fa'dan, da zarar ya hau samanta bata sake tuna komai na bacin rai a tsakaninsu.

Ta ci kukanta ta 'koshi bayan tafiyar su, sai ta yi dabarar fara karatun kura'ani dan ta sami sau'kin 'kullutun dake neman fasa mata zuciya da makoshi.

A haka ya dawo ya tarar da ita, ta sami sau'kin bacin ran da ta ke ji.
Chapter 47 · 0% Book details