← Book details Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 113

Sashe 29

Halin Yau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai tana gaskata mahaifiyarta, yau kadai da wayar take kashe ta samu rarar lokaci har sallar walaha ta yi. Ta kuma samu sukunin tattaunawa da uwarta, ta yi abin da ya dace na ayyukan yau da kullum.

Inna ta sake nisawa ta ce, "Ba namijin da za ki je kina masa wannan ba'kin dabi'un da kika fito da su, ku samu zaman lafiya da shi, duk son da yake miki kuwa. Ban hana ki amfani da waya ba, amma ki dinga ajiye ta sai kin kammala komai na aki, nauyi ne zai sake kama ki, shi namiji idan yana da mata komawa yake yi tamkar jariri komai sai an yi masa, ta ya ya za ki iya kula da miji da hidimar gida da wannan danne-dannen wayar da tun ana ganin na 'dokin wayar ne har kuma ya koma na kauyanci da asaranci ya zarce hankali da ka'ida."

A hankali Sa'adah ta ce, "Zan gyara Inna."

"Na ji za ki gyara, sai mai za ki ce mini kuma"? Inna ta fadi haka tare da zuba mata ido.

Cikin kunya "Sa'adah ta ce kai Inna don Allah, to ki yi hakuri."

Kai tsaye ta ce, "Tafiya za ki yi ki fara rayuwa da wani mutumin da ba ki saba da shi ba, ba shi kadai zaman zai kasance ba har da dukkan ahalinsa don haka ki koyi ba da hakuri idan kin yi laifi, ki kuma zama mai karbar gyara yayin da aka gyara miki laifinki, wannan shi ne mafi dadin zama a cikin mutane, na lura da ke ba da hakuri na miki nauyi, sai tura ta kai bango kike tuba wanda alamu ne na girman kai. idan mijinki ya gane kina da girman kai kuwa, wahalar ki zai yi don shi ma girman kan zai miki indai ya san ciwon kansa, sai dai idan solobiyo ne."

***

Bangaren MK yana ta Shirinsa musamman na gyran gidan da zai zauna, saukin da ya samu gidan mallkinsa ne da ya fado a gadonsa, tun lokacin yan haya suke ciki sai yanzu aka tashe su yake gyara, a unguwar Gadon Kaya gidan yake, ba wani babba ba ne amma tsarin gidan ya yi kyau, falo ne matsakaici mai dauke da manyan dakuna biyu da bandaki a cikin daki daya. Sai tsakar gida mai matsakaicin girma, daga gefe wani dakin ne shi ma da bandakinsa, sai daya gefen kuma kicin ne da wani bandakin karami, daga harabar gate kuma akwai karamin filin da zai dauki mota guda daya, ya shuka flowers sun fara fitowa wanda nan gaba za su 'kawata gurin.

Gini ne mai aminci amma ba tayals ba ne siminti ne a dakunan.
Shi kuwa a kokarinsa na son dadawa amarya Sa'adah yake son sanya mata tayals a falo da bandaki duk da a lokacin an fi saka carpet irin dan yankan nan.

Aka fara aikin gida sai lashe kudi yake yi sosai, wanda hakan ya sake mayar da MK ya zama very busy kullum aka tashi a makaranta yana gidan gurin masu aiki, ko wurin neman ku'dinsa ba shi da lokacin kansa wanda hakan ya sake karfafa
zaton Sa'adah na bai iya soyayya ba.

Shi yasa take kula Khalil har yanzu! take kuma shan soyayyar 2go, idan MK ya zo shike nan idan bai zo ba, huta roro ba ta kewarsa.

Sakamakonsu ya fito wanda WAEC din Sa'adah ta kasance ba yabo ba fallasa, amma NECO ta yi kyau sosai, a lokacin suka shirya bikin kammala makaranta da murnar sakamakonsu, ba laifi a shekarar an ci NECO sosai.

A *HANG OUT* suka shirya yin bikin, a lokacin gun ne yake tashe a wurin samari da 'yan-mata, da kyar Inna ta bar Sa'adah ta halarci taron.

Shi ma sai da ta yi karyar yayar Zainab ce ta haihu za su je, nan kuwa iya su 4stars ne, sai samarinsu na aji Irin su Khalil da kuma saurayin Halima Sagir.

Haka suka yi wannan bidirin. Sa'adah a takure saboda wannan ne karon farko da ta ta'ba zuwa wani guri da sunan party, kuma a cakude da maza sai abin ya zame mata bako, ga dai kayan kwalama cike da teburinta hatta ice ream da ta ke jarabar so bata iya 'dan'danawa a bakinta ba, Khalil sai kaffa-kaffa yake yi da ita don ta sake, ita kuma sai raya ina ma kulawa da iya soyayyar Khalil, MK ne ya iya su.

Tana cikin wannan tunanin wayarta, ta shiga ruri, tana dubawa taga MK ne, ta 'ki amsawa, tana tunanin idan ya ji wannan kidan sai ya ishe ta da tuhumar inda take.
Bai daina kiran ba har sai da ta yi shahadar amsawa, jin hayaniya da kade kade yasa shi tambayar inda take, ta karkace baki ta shirya karyar ta raka Zainab gidan suna, yayarta ce ta haihu, ya yi shiru ba don ya gamsu ba, saboda ki'dan music yake jiyowa ba dan ka'dan ba.
Ya nisa ya ce, "Son ganin ki nake yi, ya za a yi ke nan?"

A ki'dime ta ce, "Ai anjima za mu dawo na san dai zuwa magariba mun iso."

Da sauri ya ce, "Har Magariba za ki kai a waje? yanzu karfe 4, ki tabbatar biyar da rabi ta miki a gida, ina jiran ki."

Ya kashe wayarsa ba tare da ya jira mai za ta ce masa ba, saboda bai gamsu a gidan suna suke ba.

Ta yi shiru da waya a hannunta, tana tunanin yadda MK ya mata magana a gadarance tamkar ya zama mijinta, wani sashe na zuciyarta kuma so yake ta isa gida kafin lokacin da ya ce din.

Duk kokarin Sa'adah na son ta bar wurin da wuri ya ci tura, su Safina sun hana ta, kan dole ta kashe wayarta don kada MK ya sake samun ta.

Sai bayan Maghrib suka kawo ta gida, ita ce a gaban motar su Halima na baya, duk yadda ta so su ajiye ta a hanya Khalil kin yarda ya yi, don so yake mugun malaminsu ya ganta a motarsa tunda a unguwar yake sana'ar sa ta wanzanci, ya san kuma saboda shi take son su ajiye ta daga nesa.

Su Halima na sake zuga shi ta hanyar cewa, "Idan ka ajiye ta a hanya wallahi soyayyarka ba ta kai ba!"

Dai-dai lokacin MK yana kofar shagon kusa da jikin gidansu ana masa gyaran tayar mashin dinsa da ta yi faci, daf da shi Khalil ya tsaya, tsaleliyar mota(Continue Discussion) a wancan lokacin ita ce motar da take tashe ko'ina ka shiga maganar motar ake yi wanda shi ma ta mahaifiyarsa ce ya dauko, gaban Sa'adah ya sake tsananta bugawa musamman yadda hankalin mutanen wajen ya juyo kan motar, ga ta ita ce a gefen hannunsu, ma'ana tana bude kofa dole kowa ya gan ta.

A tsarin mahaifinta ba ma MK kawai ba, bai kamata mutanen gurin su gan ta ta fito a motar saurayi a irin wannan lokacin ba.

Ta rasa yadda za ta yi ta fita, musamman yadda kayan jikinta suka kamata sosai duk da mayafin babba ne. Sai dai shara-shara ne, hijabi ta saka da za ta fito, saboda Inna ba za ta barta ta fita da wannan dinkin ba wanda anko ne telan Safina ya dinka musu, da ma nufinta tana isa zaure ta maka Hijabinta baki alaikum.

Kunya da tozarci iri-iri suka dinga bin ilahirin jikinta, ganin yadda ta kasa fita a motar ya sanya Khalil fita ya zaga, ido biyu su ka yi da MK ya hura hanci ya dauke kai, ya bude gaban motar yana fadin fito, da kyar ta fito fuskarta a kasa ta kuma ja mayafin har kanta aka bita da ido, mazan da suke gun dukkansu a ransu yaba surarta suke yi har daya a cikin su wanda dan kwaya ne ya kasa hakuri, a fili ya furta "Kai waccan baby an zuba mata halitta Billahillazi da ina da kudi da na yi kerwa da ita."

Tun tsayuwar motar MK ya ji zuciyarsa ta tsinke musamman da ya ga mace a gaban motar ta kare fuskarta, haka kawai ya dinga fatan kar ta kasance Sa'adah ce, ya san zai yi wahalar gaske ta zama ita ce, amma sai ya kasa nutsuwa, a lokacin da ya ga Khalil ya fito da gadara sai ya tabbatar Sa'adatu ce, take ya ji wani irin matsanancin kishi ya kama shi, irin kishin da yake danne soyayya.

Maganar da wannan saurayin ya yi na yabon surar ta sai ya sake ninka bacin ransa wanda bai taba Jin irin sa a tsawon rayuwarsa ba.

Zuciyarsa ta yi zafi, take ya ji yawun bakinsa ya kafe makogaronsa ya bushe, kansa ya sara da wani irin ciwo mai tsananin gaske.

Ashe Sa'adah da Khalil ta fita, ashe shi yasa ta kashe wayarta, don ta nuna masa tana tare da wanda ya fi shi, ta kuma yarda ya kawo ta har titin da take da tabbacin zai iya ganin su a tare, karo na farko da ya ji ya yi kuskuren barin Farida saboda Sa'adah.

Ya tabbatar ta fi ta son sa kawai dai shi Sa'adah ce ta fi shiga zuciyarsa, kuma ta fi daukar hankalinsa.

Ko ta kan gyaran mashin din bai tsaya ba, ya tari abin hawa ya nufi gidansu, kafin ya isa wani irin zazzabi da azababben ciwon kai sun masa mugun kamu.

Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*

*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.

*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.

*TALLAH*.
Chapter 29 · 0% Book details