← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 94

Sashe 93

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan biki da sati É—aya Ahmad suka nufi gidansu Inna mari bisa umarnin baba shi da Mudanseer.
Halin da suka iske mama gaje a ciki ya ɗaga musu hankali matuƙa, suka kwasheta zuwa asibitin dawanau.
Dukan wani taimako na musamman sun bada damar a batashi, cikin amincin ALLAH kuwa tafara samun sauƙi da yake abun baiyi nisaba, amma kuma likitocin sun tanbatar musu lokaci-lokaci ciwon zai ringa motsa mata, dan ɓacin raine ya taru mata a zuciya harya kai ga taɓa mata ƙwaƙwalwa.
An bata magunguna suka ɗakkota suka dawo da ita gida, a lokacinne Ahmad yay tunanin yakamata mama gaje ta koma gidansu kodan ta ringa samun kulawa, dan anan ƙarfin iya ya ƙare sosai, itama ƴarta sotake ta ɗauketa daga gidan, bai kamata kuma abar mama gaje ba kawai hakan zai sake girmama ciwonta.

Koda Ahmad yazoma da baba shawarar saiya aminta sosai, dan haka suka zaunar da baba Yusha'u sukai masa nasiha mai ratsa jiki akan yay haƙuri mama gaje ta dawo gidan da zama anan sashen iya ta ƙarasa rayuwarta, sai Samina ta cigaba da kula da ita har itama ALLAH ya bata miji tayi aure, dansu Ahmad watan gobe zasu koma saudiyya.
Yau ɗinma yaso turjewa, amma da sukaita lallashinsa sai ya yarda, dukda bada zaman aure zata dawo gidanba haka Ahmad yaɗan shirya masu ɗakin da zasu zauna ita da samina, katiface kawai sai kwabar kaya daɗan abin buƙata.
Haka aka dawo da mama gaje gidan abin tausayi, itama Samina akace ta dawo.
Jitai kamar ta fasa kuka, dan koda Ahmad baya kulata ganinsa da take yawanyi acan na saka zuciyarta yin sanyi, haka babu yanda zatayi ta dawo nan gifansu da zama.
Sai dai kuma sam babu jituwa tsakaninta da mama gaje, sai da su baba sukai mata faɗa akan hakan sannan ta nutsu ta fara bata kulawar da ake buƙata tana kaico da ALLAH wadai da rayuwar son zuciya da suka jefa kansu a ciki, da yanzu sune a daular dasu Ammi ke ciki, amma gasunan babu wan babu ƙanin, babu dukiya babu Ahmad, ita yanzu ko sunan ma'aruff ma batason tunawa a rayuwarta.
Tanaji tana gani fita ta gagari rayuwarta, saboda data fita yara zasu fara mata ihu, mazan dake majalissa na zunÉ—enta da dariya da kiranta *Matar manya*.
Wannan dalilan ya sakata haƙura da fita ko ina a rayuwarta, ga yaran Ahmad sam basa yarda da ita, Haysam ne kawai, shima zakiga yana ɗari-ɗari da ita, wanan abu har kuka yake sakata.
Dan akwai randa ta shigo sashen nasu Ahmad amsar ruwan zafi zata jiƙama mama gaje magani sai taci karo da Abu-Talib dake wasa a tsakar gidan ya faɗi, tai ƙoƙarin ɗagashi ya tashi yaronnan ya saka mata ihun kuka akan karta taɓashi.
Tana ƙoƙarin saukesane Ahmad ya shigo gidan, zuwansa kenan yazo gaushesu dan Abu-Talib ranar anan ya kwana shi da Haysam.
Jikinta har rawa yake wajen sauke Abu-Talib, a ranta tana tsoron kar Ahmad É—in yay tunanin wani abu taima yaron ne.
Dan taga Ahmad ya tsatstsareta da idanu fuska a É—aure, cikin rawar baki tace,
“Wlhy babu abinda nai masa, na iskesa ya faɗine shine nai ƙoƙarin tadashi amma yake kukan nan.......�
Hannu Ahmad ya ɗaga mata batare da yace komaiba, ya kama hannun Abu-Talib dake ɓoye a bayansa suka bar wajen.
Hakan yasa Samina juyawa ta koma tana kuka batare da ta shiga amsar ruwan zafinba.
Wannan yasa duk son da take nason jan yaran a jikinta ta haƙura, sai dai ta kallesu daga nesa kawai.

★★★★★★

A wannan tsakanin Sadiya ta haihu ƴan biyu duk mata, su Rumana suka shiga jerangiyar zuwa gidan har akai suna, kwanaki hudu da sunan ƴaƴan sadiya Fa'iza ma ta haihu na uku, suka sake rankayawa katsina, Samina bataso zuwaba amma ƴan uwan sukace ta cire komai a ranta ta ringa shiga cikinsu, haka suka sakata dole taje, cikin ƴan shema ma ta kasa sakewa tanata laɓe-laɓe.
Bayan dawowarsu daga sunan Fa'iza Umm-Ruman ta roƙa Ahmad ya barta suje gidansu da suka zauna ta gaishe da su maman Ama idan suna nan.
Bai musaba ya barta, shima da kansa ya kwashesu amota dukansu ya kaisu.
Chapter 93 · 0% Book details