← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 94

Sashe 4

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ƙawaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu yasan suɗin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels ɗin hausa, rayuwar jin daɗi da dukiya da akeyi a novels na ƙayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya buɗama Ahmad ɗinta shima yay arziƙi ya gina musu ƙaton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daɗi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taɓa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiɗin dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da ɗaukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ƙawane ke ɗaukar hankalinta da ƙara faɗaɗa burinta, tama kai inhar buk bana masu ƙazamin arziƙi bane ƴan gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faɗin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ƙyawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk ɗin saboda shauƙi.
HaÉ—uwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ƙyaƙyƙyawace babu laifi.
Ƙananun burikan Samina sun fara faɗaɗa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ƙwalkwali Ahmad kuɗin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ƴar kalar manyan mutane babu wani jan aji take miƙa kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ƙananun sabbin ɗabi'unta harya kasa haƙuri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci haƙuri tabasa, ta shirya masa ƙaryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu É—inne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taɓa wayewaba ta zama cikakkiyar ƴar jami'a balle shima ta maidoshi kan hanya su shinfiɗa ƙyaƙyƙyawan rayuwa irinta jaruman littafi🤦🏻‍♀.............✍�

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*

*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(3)*

...........Da waɗannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruɗin su Nafy, idonta ya fara buɗewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan baƙi masu lokaci, wannan damar samarin jami'a ƴan ƙwalisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ƴaƴan manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana'a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba ɗaya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ƙananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ƙyawune kawai Ahmad ɗin zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waɗanda zasu iya linkashi ƙyawun, ga kuɗi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluɓe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaɗayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluɓe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taɓa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai alƙawarin aure a kansu da ƙaunar juna mai ƙarfin gaske.

_________________________

A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ƙarya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ƙawarta da za'ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ƙawarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin É—in Sufyan zai kaita.
Hakan ba ƙaramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.

Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan...... Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ƙwala mata daga waje yasa gabanta faɗuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.

“Samina!, Samina!!, Wai Samina baƙya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne?�.
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga É—akin dake can cikin wani lungu tana gyara É—aurin É—ankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
“Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, ɗan kwalifa nake ɗaurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki?�.
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ƙokarin hura wuta ta riƙe, “Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Baƙya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ƙyaɗan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro�.
Baki Samina ta ɗan taɓe tana gyara zaman gyalen kafaɗarta, “Iya nifa wlhy banajin daɗin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ƙyau a rayuwata dan ALLAH?�.
“Ba nace kina wani abu mara ƙyau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan ɗabi'u mara amfani�.
“A'a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ƙuruciyarta ba? Naga ba aure aka ɗaura musu ba alƙawarin auren ne kawai ko?�.
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faɗa tana ƙokarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace, “Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ƙyau take bata ƙarko, tunda har da alƙawarin auren, wataranama ɗaurawa za'ayi kamar yanda muke fata
“Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata�.
“Hakane Mari�.
Iya ta faɗa tana ɗauke kanta daga garesu ta koma ƙoƙarin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi, “inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za'a fara kamun ƙarfe uku na yammane�.
“To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ƴan saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ƙokarin taɗo ƙafarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu�.
“Humm Inna ai mutanen duniya ba'a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arziƙin kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune�.
“Maganarki na kan hanya wlhy ƴar albarka, kedai jeki karki makara�.
“Okey my sweet kakus bye�.
“Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye�.
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige ɗakinta tana ƙyalkyata dariyar sake ƙular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ƙure musu.
Chapter 4 · 0% Book details