Sashe 10
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsagwaron gayu Samina ta fito da ga ɗakin Inna mari, sai ƙamshi take zabgawa, wanda bai saniba bazai taɓa ɗauka ta fitone da ga irin gida nasu Ahmad ba.
Tana ma inna mari da iya sallama wayarta ta shiga ƙara, tsaki taja mara sauti, dan tasan dai bai wuce Ahmad sarkin naci ba, dan duk kiran da yay mata tana zaune tana kwalliyane, amma dan iya shege taƙi ta ɗaga.
Amma Ma'aruff na kiranta yace ya iso ta fito jiki yana rawa.
Sam idanunta bai kai kansu Ahmad ba, saboda suna daga bayantane, taku take ɗai-ɗai tamkar tazo filin gasar sarauniyar ƙyau ne, ƙamshinta kuwa tuni ya buɗe hancin Ahmad da Sufyan da ke binta da kallo baki buɗe tamkar sakarkaru.
Daga cikin motar Ma'aruff dake kallonta ya miƙa hannu ya buɗe mata murfin gefensa, a gaban idonsu Ahmad ta shige motar.
Wani ƙululun baƙin ciki da ya tokare maƙoshin Ahmad ne ya wuce da ƙyar, yaso ya danne amma sai ya kasa, ya yunƙura cikin zafin nama zai je gareta Sufyan yay azamar ruƙo hannunsa yana girgiza masa kai.
Dole Ahmad ya haƙura ya zubama motar ido har tabar wajen, Sufyan dake ɗaukarsu video recording a waya ya sauke yana sauke numfashi kusan a tare.
Baicema Ahmad komaiba akan hakan, sai Mashin da ta haye abinsa ya tayar yanama Ahmad nuni da shima ya hau suje.
Har sukaje inda suke son zuwa babu wanda yay magana balle su É—akko zancen Samina.
Sun isa wajen ƙawarsu mai suna Zaheedah, tare sukai karatu da ita, da farko catai tanason Ahmad, amma sai bai ɓoye mataba ya sanar mata yanada wadda zai aura tayi haƙuri.
Tayi fushi a lokacin, amma daga baya sai ta dawo kuma tace su zama abokai, badan Ahmad ya soba ya amince saboda matsawar Sufyan da Ameen, tun daga lokacin sai suketa zuminci, tare da taimakon juna akan karatu har ALLAH yasa suka gama.
Sun cigaba da zumincinsu, yayinda suke haÉ—uwa jefi-jefi dasu Ahmad É—in, sai ko waya ita sunayi akai akai.
Tarbar mutunci suka samu daga wajen Zahidah, ta kaisu har falon baƙi dake a cikin gidansu, kafin wani dogon lokaci an cika musu gabansu da kayan ciye-ciye.
Sufyan ne kawai yaÉ—anci wani abu, amma banda Ahmad dake a zumi, wanda dole ya faÉ—a musu azumi yakeyi saboda fushi da Zaheeda tayi akan baici abin gidansuba.
Gaisuwa sukayi cikin mutunta juna, kafin su É—ora da hirar yaushe gamo, dan sun É—an daÉ—e basu haÉ—uba.
Sun mata bayani akan abinda ya kawosu game da taimakon da zatai musu akan yaya maryam.
“Karka damu Shema, insha ALLAHU zan bada gudunmawata, domin gyaran aure aiba abin wasa baneba, amma ku yaya maganar naku auren? Musamman ma kai Shema da nasan akwai matar tamu a hannu?�.
Murmushin yaƙe kawai Ahmad yayi, amma baice komaiba, sai Sufyan ne ya bata amsa da faɗin, karki damu, soon zakiji bayani mai daɗi insha ALLAHU�.
Cikin faɗaɗa murmushi tace, “To ALLAH ya tabbatar mana, ya kuma kaimu lokacin�.
Da amin suka amsa, inda Ahmad ƙoƙarin danne ɓacin ransa kawai yakeyi a wajen.
Kusan awarsu biyu a gidan sannan sukai mata sallama suka tafi, bayan ta haɗasu da leda ta kayan shan ruwan Ahmad. Da ƙyar suka amso, dan sai da ta ɓata rai sosai sannan.
Sufyan yaso su ƙara zuwa wani waje danya ragema Ahmad ɓacin ran da ya lura yakai ƙololuwa a ciki, amma sai Ahmad ɗin yaƙi yarda, yace su wuce gida kawai.
Sufyan na kafe mashin a majisarsu Ahmad bai zaunaba, hannu kawai ya bama su Salisu dake zaune su uku kawai suka gaisa ya nufi gida abinsa.
A ɗakinsu na zaure ya yada zango, da ƙyar ya iya zame kayan jikinsa ya zauna daga shi sai best da boxer, baiyi auneba yaji jawaye masu ɗumi nabin kumatunsa.
Wai yau shine akan idonsa yarinyar da ya gama ɗorama buri ta shige motar waninsa ba shiba, bayan yaji a ransa tabbas taga kiran da yay mata a waya taƙi ɗauka.
Gaba É—aya kansa ya kulle game da Samina, ya rasa wane kalar tunani zaiyi ko zaiji sassauci.
Bai motsa daga wajenba har aka kira sallar zuhur, ya tashi daƙyar ya fice bayan ya saka jallabiya a jikinsa.
Suna idar da salla É—akin ya sake dawowa ya kwanta, nanma dai tunaninsa ya É—ora daga inda ya tsaya, bai sake fitaba sai da la'asar tayi, an idar da salla ya sake nufo gida, zamansa ke da wuya a bakin katifarsu Sufyan ya shigo É—akin da sallama.
Hannu ya bashi sukai musabaha, kafin ya zauna a kusa dashi gefen katifar,
“Abokina ba tunani ko ɓacin rai akanta ya kamata ka sakama ranka ba, ɗaukar mataki da gaggawa kafin abun yay nisa shine yafi dacewa da kai, bansan miyyasa a kullum kake maida kanka ragon namiji akan Samina ba, ka riga ka sakema yarinyarne da yawa shiyyasa har take iya kawo maka waɗannan salon rainin wayon tamkar ba kanuwarka ba, ni dai yanzu da zakaji da ka shareta kawai, kaje ka samu su baba da maganar aurenku, gara ko hayar ɗaki ɗayane ka kama, tunda dai gwargwadon iko kana samun taro da kwabon da zaka iya riƙeku koda ba'a samu komai baja-baja ba, kaga saita karasa karatunta a cikin gidanka hankalinka kwance�.
Sosai shawarar Sufyan taima Ahmad daɗi, ya kuma gamsu da ita ɗari bisa ɗari, godiya yay masa akan hakan, daga nan suka ɗan ƙara tattaunawa akan maganar yaya maryam, Sufyan ya kara masa shawara game da Samina kuma.
A haka Mudanseer ya shigo ya samesu, gaidasu yayi ya ajiye kayan hannunsa ya fice zuwa cikin gida saboda azabar yunwar da yakeji.
________________________________
Bayan sallar isha'i Ahmad na zaune a ƙofar ɗakin Ayyah yana buɗa baki, sai dai rabin hankalinsa nakan wayarsa, da alama dai akwai abinda yake tsumayen gani, amma yaƙi ya shigo......
“Ɗan albarka wai bazaka ajiye wayar nan kayi buɗa baki bane?�.
Murmushi Ahmad yayi yana ajiye wayar gefensa, ya cigaba da cin alalar da Ayyan tai masa dan buɗa bakin, sai dai zuciyarsa sam babu daɗi, yau gaba ɗaya da ɓacin ran SAMINA ya yini a ransa, ya kuma tura mata massege akan ta dawo gida yau ɗinnan sai dai har zuwa yanzun bata shigoba, ya kirata kuma wayar a kashe.
Yana cin abincin yana sauraren hirar ƙannensa dake daga can gefensa a ƙofar ɗakin barcinsu, sai Ayyah da Gwaggo dake a ƙofar ɗakin gwaggon suna cin tuwo suma
Shigowar saƙo a wayar tasane ya sakashi saurin ɗaukarta har jikinsa na rawa, ko da ya buɗe saƙon sai yaga abokinsane Sufiyan yake masa “Please call me�, numfashi ya ɗan sauke a ɓoye, zuciyarsa duk a cunkushe.
A kullum canji yake sake gani da ga É—abi'un saminar sa, baisan mike shirin shigoma duniyar jin daÉ—insu ba sam? Sai a yaune ya fahimci inda matsalar take ashe.
Haka dai ya gama buɗa bakin zuciya duk babu daɗi, duk ƙaunarsa da alala sai gata yau batai masa wani daɗi ba.
Ruwa ya É—iba ya É—an watsama jikinsa, yazo ya shiga É—akin Ayya ya É—auki kayan barci ya fita zuwa É—akinsu na zaure.
Canja kayan yay ya fice waje wajen abokansa. Acan ya iske Sufiyan, sai da ya gaisa da kowa sannan yaja hannun Sufiyan suka koma gefe.
“Sufiy ya akaine? Naga kamin Please call me ne?�.
Kaɗan Sufyan ya sauke numfashi yana cije baki, “Abokina wlhy akwai matsalane?�.
“Matsala kuma Sufiy? Akanmi to?�.
“Wannan banzar yarinyar mana Sha'awa, wai ni zataima rashin mutunci akan ɗan uwanta na legas ɗinnan yazo wajenta?�.
Cike da mamaki Ahmad yace, “Itama Sha'awar abinda ta daukarma ranta kenan? Wai miyasa zukatan ƴammatan yanzu mafi yawansu sukafi karkata akan kuɗi da mai kuɗine abokina?�.
“Wlhy kuwa Ahmad, gaskiya bazan iyaba mace ta zauna tana zubamin iskanci, ya isa hakanan, wannan karon na barta har abada...�
Da sauri Ahmad ya katseshi da faɗin, “Haba Sufyan karkace haka mana, kaimafa kasan Sha'awa na sonka, ɗazunfa kaine ka gama fahimtar dani akan Samina, ƙilama kayi kuskuren fahimtar tane........�
“Ahmad kuskuren fahimta fa kace? Sam babu wani kuskuren fahimta akan batuna, Please kai daine kake neman kasa fahimtar tawa�.
“Kaga yi haƙuri abokina, wlhy na fahimceka, yanzu kabar komai a hannuna zan sameta, idan munji dalilinta bashi da muhimmanci sai kawai ka barta, amma nikam wannan abu yana bani mamaki na ƴammatan wannan zamanin, su kawai idan kaga suna kwantarma saurayi kai da nuna tsantsar ƙauna yanada wasu wakilai masu farar fuskane (kuɗi) a banki?, mafi yawancinsu haka halinsu yake, ƙalilanne na gari masu son mutum domin ALLAH, Shin suna mantawa da cewa su waɗan nan masu kudin da rarrafe suka tashi suma?�.
“Ahmad mubar zancennan, wlhy ƙaramin ɓacin rai kawai yakeyi, ai kai bakace hakaba, domin kuwa kayi sa'a, duk waɗannan banzayen halayyar sam Samina bata dashi, son gaskiya take nuna maka bawai wata abar banza dukiya ba, ko ganin da mukai mata ɗazun sai daga baya na zauna ina nazari akai, maybe ma ba abinda muke tunani bane akanta wlhy, naga rankane ya ɓaci kawai shiyyasa na sake barinka ka huce akan maganar�.
Ahmad da zancen Sufyan yay masa daÉ—i yay murmushi, dan yanason yaji ana yabon Saminar sa a koda yaushe.
Cikin abokansu suka koma suka zauna, daga nan fira ta ɓarke a tsakaninsu, duk da dai Ahmad yayi gum, sai maida hankalinsa da yay wajen cigaba da neman layin Samina.
Amma har lokacin kwanciya yay kowa yay yunÆ™urin tafiya gidansu bai sameta ba, a wannan daren da Æ´ar damuwa ya kwanta, garama jiya daga baya taÉ—an sanyaya masa ransa..............âœðŸ?
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋â¤ï¸NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋â¤ï¸NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋â¤ï¸SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋â¤ï¸NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* â¤ï¸ðŸ’‹NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇