← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 94

Sashe 92

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ruwan wanka Gwaggo ta haɗama Samina, kasancewar jikinta babu ƙwari sai iya ta shiga danta taimaka mata.
Wanka sosai na haƙiƙa iya taima Samina, kasancewar ruwane mai zafi sosai sai taji daɗin jikinta, har kanta sai da iya ta wanko matahi tas, sai ga Samina an fito daɗan fasali, dukda bilicin ya rigada ya gama lalatata, dukya lalata mata fata ya maisheta tamkar wata tsohuwa, ga wahalar datasha a jail.
ÆŠakin Gwaggo aka kaita, zainab ta bata kayanta ta saka, sannana aka kawo mata tea tasha dan hanjinta ya wartsake.
Tana cikin shan shayinne Ahmad daya fita ya shigo gidan, magana yayi akan Saminar ta fito Mudan ya kaita asibiti dan a duba lafiyarta.
Kowa yay na'am da hakan, dan haka Samina na kammala shan shayin da kaÉ—anma ta iya sha Zainab ta kamota suka fika fito.
Asibiti mai ƙyau Mudan ya kaita bisa Umarnin Ahmad.
Shikuma ya ɗauki Abu-Turab daya maƙale masa suka tafi gida.
Koda yazo gidan bai faÉ—ama Rumana komaiba, sai Abu-Turab ne ke sanar mata yaga ojuju a gidansu Baba.
Ta ɗauka shirmensane kawai, dan haka tai dariya ta share zancen, amma sai Abu-Turab yayta maimaitawa maganar, hardai ta ƙosa ta tambayi Ahmad dake cin abinci yana saurarensu ƙarin bayani.
Kamar bazai tankaba yacigaba dacin tuwonsa, sai da ya gama tsaf yamaje É—akinsa yayo wanka ya dawo sannan yake sanar mata Samina ce fa da suka É—akko a jail Abu-Turab É—in ya gani.
Dukda Rumana bataga Samina ba yanda Ahmad ke bata labari saida tayi hawaye.
Shiko ya tsaya kawai yana kallonta da mamaki, to miye abin kuka anan? Kuma tunma bata gantaba, idan ta ganta kuma sai yaya kenan?.
Baki ya taɓe yana ɗauke kansa gefe, hakan sai ya bama Rumana haushi, dan a ganinta itama bai kamata Ahmad ɗin ya cigaba da riƙe Samina ba har yanzu, yadace ace ya yafe mata komai ya wuce kawai.
Tashi tai ta bar masa falon tana kuka, shiko ya bita da kallo harta haye sama sannan ya sauke numfashi yana girgiza kai da murmushi, irin ita mai Æ´ar uwarnan ko.

Duk binciken da Doctor yayi baiga wata matsalaba tattare da Samina, sai olsa kawai dake damunta, sai zazzaɓin cizon sauro da jininta daya hau, saiko tashin jin ƙarfin jiki.
A take suka bata gado, aka saka mata ƙarin ruwa.

★★★★�

Kwanan Samina uku a asibiti, tana samun dukkan kulawa ta musamman, dan dukkan abinda ake buƙata Ahmad tsaye yake akai, hatta da abincin da likitan ya bada shawarar a ringa maba Samina haka Rumana kullum ke ƙoƙarin dafawa akaima Samina, dukda dai Ahmad ya hanata zuwa dubata asibitin, a cewarsa saita gama fushin dashi sannan.
Ganin dai da gaske ba barinta zaiyi tajeba saita sakko daga haushinsa da takeji ta bashi haƙuri.
To aranar da yamma yace ta shirya yakaita su duba Saminar.
Taji daɗi, ta shirya tsaf cikin baƙar abaya ta larabawa tare da naɗa kanta da gayalen jallabiyar, tayi ƙyau sosai, har Ahmad yaji kihin barinta ta fita a haka.
Da dai tai masa ƴar shagwaɓa sai kawai ya haƙura suka tafi.
Acan suka iske su Zainab dasu Haysam suma Mudan ya kaisu.
Sosai hankalin Samina ya tashi da ganin ƴaƴan Ahmad da Rumana, da yanzu itace a wannan matsayin, amma gashi son zuciya ya jata takai kanta ga hanyar data gaza ɓillewa, tayi kuka sosai tamkar zata shiɗe, Rumana ta rungumeta a jikinta tana lallashi da tabbatr mata komai ya wuce dan ALLAH tabar kuka, ta ɗauka hakan matsayin ƙaddara kawai.
Ahmad na ɗakin amma ko kallo basu ishesa ba, daga ƙarshema ya fita hannunsa riƙe da Abu-Turab zuwa wajen likita.

A ranar aka sallamesu da daddare, sai kuma lokacin sauran ƴan gidan sukasan da dawowar Samina har Baba Yusha'u, yako tubure Samina bazata zauna a gidanba, anyi lallashin duniya yaƙi sauraren kowa hatta iya.
Fahimtar da sukai ransa a ɓacene yasa baba yace Ahmad ya tafi da samina ta zauna a gidansa harsu shawo kan baba Yusha'u, dan yanzu yana cikin fushine zai iya furtama Samina dukkan abinda yazo bakinsa.
Sam Ahmad baiso hakanba, amma sai yaga Umm-Rumana na ɗokim ita, hakan datai ba ƙaramin haushi ta bashiba, dan haka yasa Mudan ya kaisu gida akan shi akwai inda zaijene.
Rumana sarai ta fahimci dankar ya ɗauki Samina ne, amma sai batace komaiba ta barsa, dan ita lamarin Ahmad ma yanzu al'ajab yake bata, idan ya riƙe abu a rai ya riƙesa kenan, kafin ya sakko asha fama.

Ɗakin baƙi na gidan aka bama Samina, Rumana ta ɗeba wasu kayanta ta bata, dukda sun mata yawa haka taketa zundumawa, tsakaninta da Ahmad kuwa ko kallonta bayayi, idanma ta gaishesa sau ɗaya yake amsawa ya ɗauke kansa, idanko tana falon ƙasa shi baya zama, hakan na masifar damunta, dukda tana nan maƙale da mugun sonsa da yafi na baya yawa tasan yamata nisa a yanzu, danshi mijin ƙanwartane, ƙanwar tatama uba ɗaya, ko matan duniya sun ƙare tasan bata isa kida kallo ga Ahmad ba a yanzun.
Wani lokacinma da gayya yakema Umm-Ruma wani abun a gabanta, aiko hakan yana zafarta a rai, dan takanci kukanta sosai.

Kamar wasa zancen gitowar Samina ya fara zagaye bakunan mutane, da biyu ake zuwa ganinta gidan sai dai a iske batanan, wasu sukance ɓoyewa take, wasu kuma suce tana gidan inna mari ne wajen babarta.
To koma dai miye abin tsegumi bai ƙarewa a bakunan mutane.

An shiga hidimar bikin su Mudanseer, wanda ana saura kwanaki biyu É—aurin aure Ahmad ya É—auki su Rumana sukabi jirgi sai porthercout, ashe ita batasan Happy ce amaryar Mudanseer ba.
Wannan al'amari ya É—aure kan Rumana, to a ina Happy suka haÉ—u da yah Mudan haka?.
Sun sami tarba ta mutunci maiban mamaki ga ahalinsu Happy, kowa na mamakin canjawar É—an uwansa, sai da suka sami nutsuwane da daddare Happy ke bama Rumana labarin yanda suka haÉ—u da Mudan.
Ashe Ahmad take so ita tun kan su wuce saudiyya, amma shi sam yaƙi nuna ya fahimceta, bayan tafiyarsa ta shiga tashin hankali, taita masa messeges da kalaman soyayya amma sai baitaɓa bata amsaba, hasalima idan ta kirashu koshi ya kirata bazai taɓa nuna mata ko messeges ɗin ya ganiba.
Ta shiga damuwa sosai harta samu Abubakar da zancen, Abu yay dariya a wancan lokacin tare da bata haƙuri akan abinda yayansu yay mata.
Itako tace babu damuwa, ita bai taɓa ɓata mata raiba dan ta fahimci yana son matarsane sosai, bayason haɗata da kowa a rauwarsa.
Abubakar ne ya bata shawara akan Mudanseer, yakuma nuna mata hotonsa da tabbatar mata cewa kamannin Mudanseer É—aya da Ahmad, babu wani banbanci.
Koda taga Hoton yah Mudanseer ta aminta da zancen Abubakar, sai dai bataji son Mudanseer a rantaba, tadai cema Abubakar zatai tunani akai.
Koda suka rabu da Abubakar sai yakoma yayta cusama Mudanseer zancen Happy shima, tun Mudan na zagin Abubakar ɗin harya ɗan fara jin wani abu game da ita, saboda Ahmad ma dai ya shiga maganar, shi kuma Ahmad bason Happy ne bayayiba, har cikin ransa yanaji zai iya aurenta kodan ya tsamita daga duhun da take ciki, amma yana duba yanayin rayuwar da yake cikine, ƙarfinsa baikai ya riƙe mata biyuba a wancan lokacin, idan yace zai aje mace fiye da ɗaya rigima kawai zai haɗama kansa wajen ɗaukar nauyinsu na yau da kullum.
Hakan yasa yaso janta zuwa lokacin da zaiɗan sake ƙwari, to saikuma Abubakar yazo masa da batun Mudanseer, koda Ahmad ya tuntuɓi Mudan da batun yaga lallai ya karɓi zancen kuma yanason Happy ɗin saishi yaji zai iya haƙura ya barmass, dan da kai da kaya ai duk mallakar wuyane.
Da taimakon Ahmad Happy ta fara son Mudan, kafin wani lokaci soyayya tai ƙarfi a tsakaninsu, har Happy ɗin ta dawo karatu nan kano gidan wani uncle ɗinta.
Daga nanfa soyayya ta ƙara ƙarfi da shaƙuwa a tsakaninsu, da farko Gwaggo ta shiga damuwa da wannan soyaya tasu, dan ita a ganinta tayaya Mudan zai auri wadda bata salla?.
Amma sai baba ya zaunar da ita yay mata bayani yanda zata fahimta, yakumace suyi addu'a hankalin Happy ya dawo akan musulunci.
ALLAH mai komai da kowa kuwa da yake yaso Happy da rahama sai gashi ta musulunta a hannun Mudanseer ba tare da kowa nata yasaniba, ta zaɓi sunan Halimatussa'adiyya, Har zuwa yanzu kuma babu wanda yasan ta musulunta a cikin ahalinta, tayi alƙawarin sai tayi aure nauyinta ya koma kan mijinta sannan ta bayyanama iyayenta gaskiya, dan dama daƙyar suka yarda zata auri Mudan, saida aka kai ruwa rana sosai har abun ya sahafi Ahmad, daga baya kuma dai suka haƙura saboda tace zata kashe kanta kota gudu tabarsu har abada.
Rumana ta share hawaye tare da rungume Happy sunayi tare, ta tayata murna sosai da addu'ar fatan alkairi.
Samina ma da yake da ita sukaje har kuka tayi, da mamakin irin wannan ƙauna da Ahmad kema Umm-Ruman, saima ta fara tunanin kidai dama Ahmad yana son Rumana ne tuncan da?.
Bata da mai bata amsa, sai dai rayuwar Happy ta birgeta, ta kuma yarda Ruman ta mata nisa ita da Ahmad.

Ranar juma'a aka É—aura auren Happy (Halimatu) da angonta Mudanseer, a ranar su Rumana suka taho da amarya nan kano, bisa rakkiyar tsurarun danginta, tanata kukan rabuwa da iyayenta suma sunayi.
An fara kawota nan gidan su Ahmad, mutane nata ƙananun magana akan Mudan ya auri ƙabila.
Washe gari kuma aka ɗaura auren Abubakar da ɗiyar ƙanwar Gwaggo mai suna Zubaidah, daga nan aka haɗe shagalin biki akasha aka more.
Samina nata ɓoye-ɓoye amma hakan bai hana mutane bincikota ba dansu gani, sukda ma taɗanyi fasali haka kaita zunɗenta.
Bayan anyi biki an shashshare aka miƙa amare gidajensu, su Umm-Ruman kuma suka shiga barcin gajiya.

★★★★★★
Chapter 92 · 0% Book details