Sashe 48
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
..............Jini sosai ya ɓallema Samina, abinda ya tsorata su Ma'aruff kenan suka ɗauketa zuwa asibiti, gaggawar fara ƙoƙarin shawo matsalar Aliyu ya farayi, da ƙyar aka samu komai ya dai-daita bayan baƙar wahalar da yasha.
Ma'aruff sai jan tagwayen tsaki yakeyi, ya kasa zaune ya kasa tsaye har sai da Adam ya fito sannan.
Kwantar masa da hankali yayi akan an samu dai-daiton komai, yanzu haka zasu kai Samina É—akin hutune.
Numfashi ya sauke a hankali, sai lokacinne ya tuna da batun aikinsa, waya ya ciro yay kira Mama gaje ya sanar mata akan tazo asibitin ta samesu.
Hankalinta ya tashi sosai, da yake batasan ina zata gano asibitinba saboda private ne sai ta tasa ƙanin Rumana gaba Kamalu suka tafi dan ya rakata, bata sanarma kowaba saboda a ƙofar gida ta gamu da Kamalun ta iza ƙeyarsa suka tafi.
Koda suka iso suna gaisawa da Ma'aruff ya kaita ɗakin da aka kai Samina sai yay mata bayanin ɓari Samina tayi, daga haka yay musu sallama ya tafi akan shi zaije Office ne saiya dawo.
Yanda Samina ta rame ya tadama mama gaje hankali, amma data tuna ɓari akace tayi saita danganta ramar da kwaikwan ciki, sai dai a ƙasan ranta tana mamakin miyasa Samina bata taɓa sanar mata ta samu cikiba koda wasa? Yanzu kuma auren sati uku ne har an samu cikin da zai iya zubewa?.
Batai zurfi a wannan tunaninba ta watsar da shi gefe kawai ta É—akko wani.
Kamalu shine ya koma gida ya sanar musu Samina na asibiti babu lafiya, kowa yasha mamaki, amma da yake ba biyema shirmen mama gaje sukeba sai sukai shirin zuwa su dubata.
Yayinda yaran gidan suka fara tafiya kaima yayyensu na ma'auri labarin.
Harsu Ayyah sukazo duba Samina asibiti tana barci bata farkaba, kowa yayi mamakin ganin ramar da Samina tayi a sati uku da aure kacal, hakama zancen ɓarewar ciki ya tsayama kowa a rai.
Ammi ce kawai data daɗe da fahimtar Samina nada shigar ciki tun tana gida abun bai bata mamakiba, sai dai tana tausayin mama gaje akan ƙarancin rashin kulawa da saka idanu akan yaranta.
Basu baro asibitinba sai gab da magriba, har zuwa lokacin kuma babu ko ɗaya daga dangin mijin Samina daya leƙo, shima kansa Ma'aruff ɗin bai dawo ba, sai Inna mari da Iya da sukaje, sai ko dangi ɗai-ɗai irin na kusa da labarin yaje musu suma suka ɗan lalleƙo.
Har zuwa lokacin kuma Samina nata barci bata farkaba, su dai sallama sukai musu suka taho akan sai kuma gobe idan ALLAH ya kaimu, dan malaman asibitin sun fara maganar sunyi yawa, da sun tsaya har sai Saminar ta farka suma.
Bayan dawowarsu gidane suma su Baba suka tafi duba Saminar, sun isa babu jimawa ne ta farfaÉ—o.
Da ihu da fisge-fisge Samina ta farka, sai ambatar sunan Ma'aruff take akan itafa tanason cikinta karsu zubar mata, babu wanda bai shiga ruÉ—aniba, su sam sunma kasa fahimtar mi Samina ke faÉ—a.
Dr Adam yace duk su fita daga É—akin Please.
A daidai wannan lokacinne kuma Ma'aruff ya dawo, daka gansa zaka san hankalinsa kwance, kuma daga gida yake, dan bakayan É—azun da safe banema a jikinsa, babu tausayi ya wankama Samina dake cikin halin rashin sanin mi takeyi mari,
“K dan ubanki duniya kike faɗama yanda aikai ne?�
Da sauri Adam ya janyesa yana masifa, “Wai kai MJ mike damun kankane? Yarinyar dama batasan ina a hankalinta yakeba kakema wannan Marin? Kaji tausayin halin da muka sakata mana, wlhy badan tanada sauran shan ruwaba a ɗazun zata iya rasa ranta, kai baka da wani abin birgewa sai dukan mace? Wannan fa matarkace ta sunna ba matan banza daka sabama wannan rayuwarba, Mtsoww, baka sha giyarba ma rasa hankalinka ake......�
A fusace Ma'aruff ya dakatar da Dr Adam, “Malam karka faɗamin babu daɗi mana, bansan shishshigi kaima ka sani�.
Banza Dr Adam yay masa, ya shiga ƙoƙarin ganin Samina da numfashinta ke fita da ƙyar bama taimakon gaggawa, dole dai allurar barcin ya sake mata saboda sam bata a cikin hayyacinta, a ƙasan ransa yana dana sanin biyema Ma'aruff akan wannan aikin.
Acan waje kuwa su mama gaje na iya jiyo hayaniyar su Ma'aruff, sai dai basajin mi suke faÉ—a, tuninsu ma duk ruÉ—ewar halin da Saminar ke cikine ya jawo hakan, hakan yasa suma suka sake rikicewa ainun.
A fusace Ma'aruff ya fice daga ɗakin, ko kallon su Baba dake wajen dasu mama gaje baiyiba balle su sami mutuncin a gaishesu, su duk ganinsu halin da matarsa ke cikine ya sakashi a ruɗani🥺.
Basusan ma yana fita daga asibitin zuwa yay ya tanaji giyarsa ba tare da tsaleliyar budurwa suka nufi gida, tunda yau babu Samina a cikinsa anan zai warwasa abinsa😢.
★★★★★★★★★★�
Ina bakin rijiya zaune ina wankin ƙarfin hali saboda kaina dake mani wani azabar ciwo, gaba ɗaya kwanakinnan haka nake fama da wannan ciwon kai, abinda kawai nasaka a raina basir ne yaymin mugun kamu da malleriya, sallamar yaran gidanmu ta sakani ɗago idanu na kallesu, ni kaɗaice dama a gidan, Kausar taje asibiti wai yaron cikinta na dawo mata a ƙirji, maman Amatullah kuwa tana gidansu sunan ƙanwarta data haihu, su Fa'iza kuwa tun da safema suka tafi gida yau.
Sallamarsu ta amsa fuskarta dai babu walwala.
“Ku kuma daga ina? Da wannan tsakar ranar khadija?�.
“Yaya Rumana daga gida mukefa, Yaya Samina ce bata da lafiya tana asibiti�.
Ajiye hijjab ɗin danake cuɗawa a cikin ruwan kumfar nai ina faɗin, “Ya salam, miya sameta haka?�.
“Muma bamu saniba, amma dai su Ammi ma duk sunacan sunje dubata�.
“Wayyo, to ALLAH ya bata lafiya, zan kira Yah Ahmad kuwa nasamu zuwa anjima naje na dubata�.
Haka Rumana ta cigaba da wankinta su khadija na tayata da hira, duk da ma ita ba saka musu baki takeba dan kanta dake ciwo, da yake wankin baida yawa dan danan ta kammala, tana share ruwan wajen Kausar ta shigo tana ɗaga ƙafa da ƙyar saboda ciki, duk da yanzu bata min magana hakan bai hanani mata sannu ba.
“Uhumm� kawai tace min ta buɗe ɗakinta ta shige.
Ban damuba, nima na haÉ—a robobin danai wankin na nufi nawa É—akin, muna shiga na bama su Khadija kantu daya rage a kayan sana'ata nace suje gida kar'a nemesu, dan nagaji da surutunsu nikam.
Da murna suka amsa suka wuce, nikuma na shiga duba magani dan nasha sai dai ma ashe ya ƙare, ƙaramin tsaki naja na haye gado na kwanta kozan samu sassauci.
Ring ɗin wayartane ya tasheta daga nannauyan barcin datai nisa a ciki, ta kai dubanta ga agogon ɗakin tana ƙoƙarin lalubo wayar a ƙasan filo.
Ƙarfe biyar na yamma, agogon ya nuna, tashi nai zaune a rikice dai dai na gama ciro wayan, Yaya Ahmad ne, kafin na ɗagama ta tsinke.
Ina ƙoƙarin sakkowa ya sake kira, dakatawa nai na ɗaga ina kaiwa kunne.
“Kina lafiya kuwa? Tun ɗazun nake kira amma babu amsa�.
Cikin yanayin wanda ya tashi a barci nace, “Kayi haƙuri Yaya, wlhy barci nake�.
Daga can yace, “Barci kuma? Lafiya dai ko?�.
“Lafiya ƙalau, kaina ne kawai kemin ciwo dan wankima na gama�..
“Na rasa wannan ciwon kai na miye haka? Kusan kullum yanzunfa sai kinyi?�.
“Wlhy kuwa Yaya, amma karka damu inaga basirne, zan aika iya ta bani magani�.
“ALLAH ya ƙara sauƙi, yanzu kinsha magani ko?�.
“A'a maganin ya ƙare, jira nake anjima idan Yah Mudan yazo sai ya sayo mani�.
“Bara kawai na kirashi sai ya kawo miki yanzun, ina zama da ciwo yaga daɗi�.
“To Yaya na gode, itama Yaya Samina ma bata da lafiya�.
Shiru yay kamar bai jitaba, hakan yasa tai tunanin baijinba ta sake maimaita masa.
Cikin halin ko in kula yace, “ALLAH ya ƙarama kowa lafiya�.
“Amin yaya, ammafa abin serious ne fa, dan tanama asibiti, na shirya naje na dubota dan ALLAH?�.
A hasale yaja tsaki yana faɗin, “Malama kiji da naki ciwon kinji, inada abunyi sai anjima� ƙit ya kashe wayarsa.
Shiru nayi a wajen tamkar ruwa ya cinyeni, na zame wayar a hankali ina kallonta kamar zan hangosa ta ciki, dama tun jiya nasan haushina yakeji saboda su Fa'iza sunce zasuje gidan Yaya Samina, nima saina tambayesa dan naje nagano ɗakin amarya daga nan mu wuce gidan sunan ƙanwar maman Ama da akeyi.
Aiko naci masifa, dan Yah Ahmad na asali dana sani ya komamin, tamkar zai jawoni daga wayar ya daka, daga ƙarshe ya kashe wayarsa ma baki ɗaya, na gwada kira yafi sau hamsin amma switch up, ni kuma yanzu sam banyi zaton abin zai ƙara ɓata masa raiba tunda dai ciwo akace.
Damuwa fal raina na tashi na fita, dan ko sallar la'asar banyiba, tsakar gidan shiru kamar babu mutum, dama dagani sai Kausar ne, mai raya gidan maman Ama ce kodan saboda ƙiriniyar yaranta.
Bayan na idar da salla na É—auki waya na kirashi, amma harta yanke bai É—agaminba, na kuma kira ban gajiba, sai da na jera masa kira goma sannan ya É—aga.
A hasale yace, “Ke wai bakisan ina kasuwa bane? Idan kika takura min da maganar nan zan ɓata miki rai wlhy�.
Bai jira ma mizan ceba yanzun ma ya sake yanke min wayar, hawaye masu ɗumi suka shiga rige-rigen fitowa a idanuna suna silalowa bisa kumatuna, ni bansan lokacin da ya farama Yaya Samina irin wannan baƙar tsanarba? nima dai na shagala wajen mantawa murɗaɗɗen halinsa ne, darajar aurenmu yasa na fara ganin haƙoransa a waje, suma ɗin a wannan zuwan.
Zamewa nai na kwanta ina cigaba da hawayena.
Sai bayan isha'i yau su Salima sukazo, dan sune ke a gidan saboda su Ammi sunje duba Yaya Samina a asibiti.
Yanda suke bani labarin halin da Yaya Saminar take ciki sai tausayinta ya kamani, na mata addu'a dan nasan tunda yace bazan jeba to bazanje ɗinba, dan sunan ƙanwar Maman Ama da yace bazanjeba jiya gashi banje ɗinba.
Sai da zan kwanta ne danaga har lokacin bai kiraniba nai masa text message na ban haƙuri da kalamai masu sanyi na tura masa.
Haka na kwanta cikin damuwa, da ƙyar barci ya ɗaukeni kuwa, dan ya sabamin duk dare ko bazamuyi hira mai tsaho ba dai zamu gaisa yaji lafiyata naji tashi kafin na kwanta.