← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 94

Sashe 46

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

............Gaba É—aya yinin ranar haka ta yini sukuku fuska babu walwala, su maman Ama sunyi gulmar harsun gaji, har dare bata iya sakin jikintaba, dan koda su Salima sukazo bata shiga sabgarsuba, tunma suna tsokanarta har suka koma tausayinta da lallashi.
Washe garima dai zuciyarta duk babu sukuni ta tashi, gashi ta gwada Number ɗayan layinsa daya cire amma bai shigaba, hakan ya tabbatar mata dai yana a ƙasa ɗin tunda dama babu waya ya tafi.
Su Salima na gama tayata aiki suka tafi gida, ita kaÉ—ai suka bari tunda yanzu babu makaranta, sai islamiyya.
Kwanciyarta tayi a ɗaki, alwala kawai ke fiddota, abincima ƙin dafawa tai sai shayi ta haɗa tasha ta sake kwanciya.
Kusan bayan la'asarne tana kwance tajiyo hayaniya a tsakar gidan, bata motsaba balle ta fita, dan daga ɗakin tana iya jiyo komai, kishiyar Kausar ce tazo gidan ashe take ciwa maman Ama mutunci akan munafunci data saka Kausar ta ƙulla musu wajen mijinta akan biyan kuɗin makarantar yaranta.
Hayaniya dai sosai har maƙwafta suka shigo, wasa-wasa dai saiga gida ya cika, dan yanda nakeji ana hayaniyar sosai kamar za'a fasan bangon ɗaki kawai ya isheni amsa.
Har sukaci suka tsire bayan mijin maman Amatullah ɗin ya shigo aka raba daƙyar ban leƙaba, sai fatan shiriya da nake nema musu kawai.
Tun daga wannan ranar maman Ama da Kausar suka shiga gaba, babu mai kula wani a cikinsu, nidai nawa kallone, duk da kowannensu yana neman laɓewa ya shigo jikina danya soki ɗan uwansa, sam bana basu fuska nikam, danaga ma abin zai zama takura saina koma yin har wanke-wanke a babbar robata a cikin ɗaki kawai, dama dai shike fiddoni tsakar gidan harna daɗe asamu damata, wani lokacin kuma su Fa'iza keyi.

Ranar da Yah Ahmad ya cika kwana goma da tafiya ina kwance a ɗaki bayan sallar zuhur ina kallon film ɗin da Abu ya turomin a waya kira ya shigo, ɓaro-ɓaro Number Yah Ahmad da yay save da suna *My N2* ta bayyana, wani farin ciki ya kamani, na lumshe idanu ina haɗiyar numfashi da sauri-sauri, kamar maijin tsoron taɓa wayar haka na danna alamar amsawa, kafin nakai wayar kunnena a hankali.
Dagani harshi babu wanda yay magana kusan Seconds goma.....
“Babie R� ya Ahmad ya faɗa a hankali cikin katse shirunmu.
Idanu na sake lumshewa ina murmushi, nima na amsa a hankali da faɗin, “Uhyim Yayana�.
“Har yanzu dai Yayan?� ya sake faɗa cikin sanyaya murya.
Dariyace taso kufcemin yanda yay maganar irin kamar a shagwaɓa ɗinnan, na danneta da ƙyar, amma sai jinai yace, “Dariyama kike mani ko? Babu damuwa zan rama ai nima�.
“Ba dariya nakeba fa Yaya, ina yini?�.
“Badai haƙura zanba saina rama, ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?�.
“Alhmdllh Yaya, sai dai kewarkafa�.
Daɗi ya kama Ahmad jin furucin Rumana, yay murmushi mai sautin da har take jiyowa, “Nima hakan take Babie R, gaskiya kice na dawo gida�.
Dariya Umm-Ruman ta sanya masa, dan yanzun kam ciki shagwaɓa yay furucinsa na ƙarshe, tace, “Tab ai yayana idan ta nice ka dawo da gudu ma, to amma kuma banason ka wahala, kai zamanka ina nan ina maka addu'a�.
“Da gaske Babie na?�.
“ALLAH kuwa yaya� tai maganar da alamun jin kunya.
“Tom shikenan ta hannun damar, yanzu miye labari?�.
“Labarai kam da yawa yayana�.
“To wanne zan samu daga ciki?�.
“Saika zaɓa ka darje�.
Yace, “Inye kaga Ahmad ɗan gatan Ruman, to abani na soyayya�.
Siririyar dariya Rumana tayi tana rufe fuska kamar tana gabansa, tace, “Kai yaya ALLAH sai nake ganin kamar ba kaiba�.
Dariya sosai ta bashi shima, dan haka ya shigayin kayansa, “Wato kamar ba niba ko? To ai kece kika maidani hakan Babie R, shiyyasa nake yaba ƙoƙarin ki, dan na kula da zafinki kikazo dan kin tsare ko ina babu wasa�.
“Nagode Yayana� Rumana ta faɗa tana share hawayen jin daɗi dake silalo mata saman fuska.
“Nine ya kamata na gode miki babie na, yanzu dai ki huta abinki, muna kasuwane, dama nakirane saboda yanzun nan na ɗora layin akan waya, idan muka tashi zan kira kinji�.
“To Yaya ALLAH ya bada sa'a, sai anjima�.
“Okey babu damuwa, amma idan na sake kira karnaji wannan Yayan�.
Murmushi Umm-Rumana tayi, koda ya yanke saita sumbaci wayar tana rungumeta a ƙirji.
Tun daga wannan kiran sai yazam kullum da daddare Yaya Ahmad saiya kirani, nikuma nakan kirashi da safe na gaishesa.

Ɓangaren su Maman Amatullah kuwa sunyi gabarsu ta kusan sati uku suka koma suka sake ɗinkewa kuwa, a raina nace kudai aiki ya sama.
Tunda kuma suka ƙyalla ido suka ganni da babbar waya a hannu duk sai hankulansu ya tashi, a daren ranar muna jiyo Kausar na tafka rigima da mijinta akan sai ya saya mata babbar waya.
Shiko yace baida kuÉ—i yanzu, idan zatai hakuri da tata tayi, idan bazataiba to saita sayama kanta shidai baida.
Wannan furuci ya kawo musu rigima sosai, dan har cemasa take mijin Umm-Ruman ɗan balaguro da bai kaisa komaiba gashinan ya sayama matarsa tana ɗaga musu hanci a gida da ita, wlhy bazata cigaba da riƙe waya mai madannaiba itama ƴar shafi ɗinnan takeso mai shan jini.
Wannan al'amari ya daɗe yana bani mamaki, da safe koda na gaisheta ƙin amsani tayi, nasan ban mata komaiba dan haka na watsar da lamarinta, ita dai hassada ga mai rabo ai takice.
Ita dayake Maman Ama tafita bariki da wayo sai bata nuna ko a fuskaba, amma abun na sassakar mata rai sosai, da tanada dama saita kaɓe shegiyar wayar waran a ƙasa ta kwararratse muga tsiya.

_______________________________

A sati ukun nan da Samina ta ɗauka a gidan Ma'aruff komai ya gama susuce mata, soyayyar da take tunani yay mata tanadi ko alamarta ba gani takeba, ashe Ma'aruff riƙaƙƙen ɗan giyane, sannan kullum dare sai ya fita ta rasa ina yake zuwa?.
Karfe taran dare nayi zai fice daga gidan, bazai dawo ba sai ɗaya, wani lokacinma ɗayan ta wuce yake shigowa, lokuta da dama kuma cikin mayen giyane, yazo yayta mata amai mai wari, yakumace saita gyara, idan tai masa gaddama ya kusanceta da ƙarfin ƙwanji na tsantsar mugunta ya lakaɗa mata duka dole tayi tana kuka.
Idan gari ya waye kuwa yayta bata haƙuri akan shi baisan yayiba, zata zauna tai masa nasiha yay shiru kamar ya ɗauka, cikin kulawar juna zata taimaka masa ya shirya ya wuce office, idan ya dawoma zaka gansa normal, har ya nuna mata ƴar kulawa suyi ɗan soyayyarsu idan yanada buƙatarta ya sauke nauyi, amma taran dare nayi duk wayon dazai mata yabar gidan ya sanshi.
Gaba ɗaya ta rasa a ina matsalar take?, ga mahaifiyarsa ƙiri-ƙiri take nuna bata sonta, hakama ƙannensa, sauƙinta ɗaya sunajin shakkarsa kuma ba zuwa gidanma sukeba sai idan ta kama dole.
Amarya nayin ƙiba itadai rama tayi, sai wani haske take ƙirjinta ya cika yay fam, ga shegen kwaɗayi dake yawan damunta, sauƙinta ma idan tace ya sayo mata abu yakan sayo, sannan bai rageta a ci da shaba ta kowanne fanni, jin daɗi da kayan more rayuwa na cikin gida komai bata rasaba, dolene idan kazo gidanta ka kirata mai sa'a, sai dai matsalar tanaga farin ciki, dan kuwa kaso ɗaya bisa uku kawai take samu, shima wani lokacin batama samun.
Ƙawayenta fa kullum cikin zuwa suke ganin ɗakin amarya kashi-kashi, kowacce tanaji inama itace cikin wannan daular.
Idan suna ma kansu addu'ar samun ya tata saitai ta kallonsu kawai, dan kuwa kallon kitse sukema rogo.
Ƙannenta ma suna zuwa, hakama dangin mama gaje da ƙawayenta, sauran yaran gidansune dai har yau bataga ƙeyar kowaba, hatta da yayarta binta da suke ciki ɗaya batazo mataba.
A koda yaushe mama gaje da inna mari cikin aiko mata da kayan mata da ƴan ƙulle-ƙullensu na wurin malamai suke, kuma duk tana ƙoƙarin yi, amma ta kula Ma'aruff shegen taurin zuciyane dashi, wani lokacin idan tai wani abu sai taga kamar ya kamashi idan yana kwantar mata da kai, har sai ta fara murna sai kuma komai yazo ya burkuce.
Babu abinda ke É—aga hankalinta irin shan giyar da yakeyi, ta tsani warinta, ga aman da yake mata mai azabar wari, har kasa cin abinci take idan ta tunosa.
Chapter 46 · 0% Book details