← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 94

Sashe 5

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar an saita Samina na fitowa daga ƙozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa ɗan dandamalin dakalin dake ƙofar gidan maƙwafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ƙarema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ƙyaƙykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ƙyaƙyƙyawar surarsa suyi ɗas.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ƙube da ita kaɗai ta iya saninsa dashi ta ƙarshen gayunsa ya saka, ta zauna ɗas akansa, inda daga bayan ƙeyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ƙarancin kuɗi mai kama dana ƴan makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ƴan saƙe suma masu ƙarancin kuɗi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira ɗari huɗu ɗaure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun ɗauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da ɓoyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ƙamshin turarensa yake mai ƙarancin kuɗi, amma akwai daɗi ga hancin mai shaƙa.
Ganinta ya sakashi miƙewa yana ƙawata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
“Barka da fitowa tauraruwar mata ma'abociyar haske da walwali�.
Samina ta kallesa a wani yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faɗin, “Kai yaya, dama zakazo ɗin amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare�.
Murmushi yaɗanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki, “Yi haƙuri Samie na, banzo danna hanaki ƙyautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba�.
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace, “Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan?�.
Huci yaɗan fidda mai ɗaci, dan ta fara ƙokarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data ɗakko, amma kasancewarsa sonta na ɗawainiya dashi saiya sauke numfashi da ƙokarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
“Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin ɗin Sufiyanu ne na aro danna sauƙaƙa miki wahala�.
“Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu alƙawarin binsu dan ALLAH�.
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ƙaunar alakar Samina da su Nafyn gidan ɗan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu'amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faɗin,
“Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki buƙaci wani abu a wajen�.
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuɗi, babu kunya tazo ta amshe kuɗin dayake miƙomata canzazzu ƴan hamsin-hamsin rabin bandir ɗaya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuÉ—in a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaÉ—ai.
Ta É—aga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.

Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin ɗin dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta ɓacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yauƙi da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani ɗinnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma'anar SO ɗinba.
Ya ɗauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin ɗin yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana ɓare-ɓaren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ƙasa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ƙarfinsa amma sam yaƙi fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ƙasa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam'i.
Bayan an idar duk suka fito ɗai-ɗai zuwa majalisarsu da suka kafa a ƙofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya miƙama Sufyanu key ɗin mashin ɗin yana faɗin, “Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci�.
Amin suka faɗa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key ɗin ke faɗin Sharukhan ɗinmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka�.
Murmushin yaƙe Ahmad yayi kawai, ya kishingiɗa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da, “Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema ɗaurin auren, kasan mata da shegen son bidi'a, shiyyasa a kullum ake ƙara nisanta talaka da samun aure cikin sauƙi�.
Cikin damuwa Rabilu yace, “Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ƴammata amma babu kuɗin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana'oi munkuma ɗanyi karatun, inaga waɗanda basuda sana'ar babu karatun kumafa�.
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harɗe kafafunsa dake lilo a ƙasan benci, “Abokai wlhy bidi'oin biki suna taka rawar gani wajen ɗora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ƙara yawaitar fyaɗe, yanzu irina masu ƙarfin sha'awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ƴar wani ka jefa kanka a halaka da ƴan uwanka a damuwa ko�.
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ƙaikayi, yace “Uhumm� kawai ba tare da ya ƙara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
“Sharukhan yaya dai?�.
Ameenu da tun É—azun baice komaiba ya faÉ—a yana kallon Ahmad É—in shima.
BuÉ—e ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da Æ´ammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuÉ—i keyi lokacin bikinsu.

Sallar isha'ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waÉ—anda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ƙarin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
Ƙarfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.

Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke maƙwaftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.

Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ƙaramin ƙarfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuɗe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo ɗaya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daɗewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ƙofar banɗakinsu.
A shiga farkon gidan É—akunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha'u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa ɓara kuka saboda rashin ganin ɗanta kusa da ita, “K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ƴaƴa, inama ya shiga shima uban ɓarnar� Ahmad ya ƙare maganar yana leƙa ƙasan kejin kajinsu kozai gano ɗan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya zaƙulosa ya kai gabanta ya ajiye kafin ya shige ainahin cikin gidan da sallama.
Mahaifiyarsa da ƴar kunya ke tsakaninsu saboda shine na fari a gabanta ya fara cin karo tana ɗibar ruwa a tulun dake ƙasan barandar ɗakunansu cikin kofin silba.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tamkar batama gansaba, sai ƙannensa dake zaune a tabarma da fitila a gabansu sun baza littatafaine suka amsa masa, sai kuma Ayyah matar babansu ta farko dake riƙe dashi a ɗakinta data amsa itama daga cikin ɗakinta.
Ya gaida Gwaggo data gama zuba ruwan harta É—ora a tiren data shirya abincin babansu tana shirin É—auka zuwa É—akinsa, sau É—aya ta amsa ta É—auki tiren tai gaba abinta, yaÉ—an bita da kallo yana kauda kansa a lokaci É—aya.....
Ayyah dake fitowa ta katsesa da faɗin, “Ɗan albarka ka dawo?�.
Murmushi yay mata yana ƙarasawa gabanta da cewa, “Eh Ayyah na, ina yini?�.
“Lafiya lau ɗan albarka, kaga tashi ga abincinka nan yau miyarka nasaka akai dole a gidannan, maza kaci karya huce, ga manshanu nan dana soya maka ɗazun�.
Cikin faɗaɗa fara'arsa ya miƙe yana faɗin, “ALLAH ya saka da alkairi Ayyah na, ya jiƙan malam ya ƙara muku nisan kwana da lafiya�.
Amin ta faɗa ita da ƙannensa.
Baba dake daga can ɗakinsa duk suna jinsu shi da gwaggo, ba yaune suka fara ganin hakanba, dan soyayyar Ayyah da Ahmad ALLAH ne kawai yasan iyakarta, amma ba mutumba, inhar ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba itace ta haifesaba.
Chapter 5 · 0% Book details