Sashe 41
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tare sukaci suka ƙoshi, duk da dai Rumana najin kunya, shiko ko'a jikinsa kai tsaye yake komansa babu wani risini, sai yanzun take sake yarda da maganar mutane dake faɗin mutum mai shiru-shiru baida sauƙi idan yaso abu, duk da ba koda yaushe ya cika fara'a ba bata damuba, dan itama ba fara'arce da itaba.
Ruwan wanka ta haɗa masa ta tafi kaiwa, ta juyo zata fito sukaci karo dashi a ƙofar bayin, tsare hanyar yay ya hanata fita, cikin dauriya tace, “Yaya ga ruwan nan�.
“Na gani ai� ya faɗa yana jan hannunta, ya tura ƙofar bayin.
Da sauri tace, “Yay...�
“Shiii bansan surutu� yay maganar babu wasa a fuskarsa.
Dole taja bakinta ta kulle, tanaji tana gani ya cire mata kaya kamar yanda shima ya cire jallabiyar da ya sako kawai a jikinsa, babu shiri Rumana ta rufe idanu ruf, jikinta har tsuma yake saboda tsagwaron kunyar data mamayeta, mamakinsa ne ke sake girmama a ranta, wai dama haka Yaya Ahmad É—innan yake?.
Haka akai wannan wanka babu wani sakewa daga Umm-Rumana, suka fito yana riƙe da kayanta ita kuma botikin wankan.
A yanzun kam taji daɗi da babu ko ɗaya daga matan gidansu a waje, sai dai bata saniba mijin maman Ama ya gansu, jikinsa kuwa har ɓari yake wajen zuwa ya bama matarsa labarin abinda ya gani.
Lokacin da take leƙensu ta Window Ahmad na tsaye yana brush a wajen, ga iskar hadari data fara kaɗawa, Rumana ma fitowa tai domin yin brush ɗin, cikin zuciyarta tanajin daɗin canjawar yayanta, dama tasan tun can da shi mai tsaftane, ruɗanin Samina kawai daya sakama ransane ya nema susutar dashi.
Tana kammala alwalar barci isaka mai ƙarfi ta taso, cak Ahmad ya ɗauketa ita da butar yay ɗaki dasu suna dariya saboda tsorata da tayi wai catake iskarce tai sama da ita.
Kausar dake ƙoƙarin rufe ɗaki dan yau mijinta a gidan Uwargida yake tace, “Watsatstsu kawai� Tana jan tsaki.
Ahmad kam sai da ya dire Rumana a tsakkiyar É—akin sannan ya juya ya rufe musu nasu É—akin.
Ko a wajen shirin barcinma dai Rumana nata muƙu-muƙu, a zuciyarta tana ƙunƙuni akan figaggar rigar da Ahmad ya ciro cikin kayansa ya bata wai ta saka, dan ƙyau rigar tayi ƙyau, sai dai dole kaji kunyar sakata a gaban wanda bake matuƙar ganin girma.
Kodata saci kallonsa sai taga ko'a kwalar rigarsa, shi boxer ma kawai ya saka ya haye gado a hakansa ya kwanta yana kallonta, dan yace idan ta gama tazo gabansa yaga yanda rigar tai mata.
Ita dai tasan inhar a haka za'a cigaba ta bani da Yah Ahmad a gidannan, tunda ta lura shi babu ruwansa da kawaici agaban kowa, duk abinda yazo masa a rai shi yakeyi.
Dole tabi umarninsa dan babu wasan jayayya a tsakaninsu, shiko ya ware ido yana ƙare mata kallo daga sama har ƙasa, daga ƙarshe yajawota ta faɗo jikinsa ya mirgina tsakkiyar gadon da ita yana sauke mata tagwayen kisses.
_________________________
Æan garen Samina kuwa sosai ganin Ahmad ya zauna mata a rai, duk da Æ™oÆ™arin turesa da take a rai hakan ya gagara, yau daren É—aurin aurenta da Ma'aruff amma Ahmad yazo ya cunkushe dukkan tunaninta, koda sukaje wajen party É—in da suka shirya iyakar su Æ™awaye da abokansa kasa sakewa tai, duk da shima Ma'aruff É—in ta lura tunda aka fara hidimar bikin nan yaketa wani É—aÉ—É—aure mata, abinda yasa batabi takansa ba saboda duk kuÉ—in data buÆ™ata bata yake, abinda kawai ta kawo a ranta rashin son auren nasu da Mahaifiyarsa ta nuna Æ™uru-kuru ne, dukda yana Æ™oÆ™arin son ganin bata fahimtaba.
A yau kuma asabar aka wayi gari safiyar ɗaurin aure, gidan nasu ya cika saboda isowar ƴan shema, ga kuma dangin mama gaje na nan cikin gari da ƙawayenta sun ƙaru.
Bakajin komai sai ƙamshin girki da hayaniyar data cika gidan, dan girke-girke ake na garari, su dai su baba iyakar ƙarfinsu suka bada, amma mama gaje tace sunfi ƙarfin dafa wannan abincin a bikinsu, gefe ta ajiye kayan dasu baban suka bada ta fiddo tasu sayayyar, dama ta raba wasu ayyukan gidajen ƙawayenta.
★★★★�
Kusan sha ɗaya na safe su Kausar ana tsakar gida ana sana'ar ta gulma, wata maƙociyarsu maman Aysha ta shigo suna mata gulmar Rumana sai ga Rumana da Ahmad sun fito cikin gayun daya nema zauta zukatansu.
Rumana na sanye da les ruwan makuba daya haska choco ɗin fatarta, an masa kwalliya da kalar ruwan zuma kaɗan, gashi Ahmad yay mata ɗinkin daya zauna mata sosai a jiki tamkar irin matan manyan nan dake ji da hutu, tasha awarwarayenta da sarƙa masu ƙyau da tsari, tundaga kan takalma zuwa mayafi da bag duk sabbine, Ahmad ma na sanye da sabuwar shadda ruwan zuma sai maiƙo take, ko angon sai dai ya nuna masa tsadar kaya amma ba tsarin kwalliya ba, ƙamshin khumran da Rumana ta shafa da turaren Ahmad ɗin sun gauraye sun bada wani ƙamshi mai tsayama maƙiyi a maƙoshi.
Yana riƙe da bag ɗin Rumanan a hannunsa sai leda mai ɗan girma baƙa itama, ta rufe ɗakin ta juyo suka haɗa ido suna sakarma juna lallausan murmushi, ido ya kashe mata ita kuma taɗan murguɗa masa baki.
“Ni ko?�. Ya faɗa yana matsota.
Baya taja tana sassanyar dariya da gyara mayafinta, “Yi haƙuri ba kaiba� itama ta faɗa a hankalin.
Ƴar ƙwafa yay ya nufi hanyar fita riƙe da bag ɗin da ledar ba tare daya bataba.
Ita kuma ta ƙarasa gasu maman Ama tana faɗa musu ta tafi wajen biki sai sun ƙaraso suma.
Da ƙyar suka iya amsa mata su duka har maman Aysha ɗin, ta kaɗa kanta ta bi mijinta suka rakata da harara.
Ba ƙaramin tsaya musu a rai wankan Umm-Ruman yayiba, dan ko makaho ya laluba yasan sunyi ƙyau sosai, kamar sune akema bikin.
A soro ta iske Ahmad tsaye yana jiranta, ya miƙa mata bag ɗinta, amsa tayi tana cewa, “Thanks yayana�.
Baice komaiba sai kallo da yake binta dashi, shi kansa ganin matar tasa yake kamar ba itaba, dan kuwa ya kuma tabbatarwa jikin Umm-Ruman nason abu mai ƙyau, kamar yanda mutane ke faɗa akansa shima.
Cikin katse masa tunani ta miƙa hannu zata amshi ledar hannunsa, saiya janye yana girgiza mata kai, ya nuna mata hanya yana faɗin, “Ke kanki badan kar ace na cika rawar ƙafaba da ɗaukarki zanyi bazakisha wahala ba�.
Gaba Rumana tai da sauri tana murmushi, yayanta wlhy yafi mijin novel É—in da Samina ta tafka kuskure akan nemansa.
Duk inda suka gitta kallonsu akeyi, hakan kuma saiya zafi Ahmad a zuciya, ya tsaida musu napep suka shiga yana jan tsaki.
Da mamaki Rumana ta kallesa, sai ya galla mata harara yana faɗin, “Da nasan kowanne banza zai nema ɗora idonsa akan matata wlhy da hijjab zaki sawo Mtsoww�.
Gefe Rumana ta maida kanta tana ƙoƙarin haɗiye dariyar dake neman kufce mata, tofa kishifa kenan? Dan idanunsa harsun kaɗa saboda ɓacin rai.
Kallo bai dawo kansuba ma sai da suka iso ƙofar gidansu, gaba ɗaya mutane sukai musu caa da idanu, abokan Ahmad kam wani ihu suka saki harda masu fito tamkar anci ƙwallo suna haɗa baki wajen ambatar “Sai mai zafin mu!!�.
Daƙuwa Ahmad yay musu yana cije baki.
Ba tare da yasan mi yayi ba yaja hannun Rumana sukai cikin gida wai duk dan mutane subar gane masa mata.
Murmushi baba ilyasu da Baba Yusha'u dake ƙofar gidan suma sukayi suna girgiza kawunansu, Baba kuwa ai shi harda kunya yaji, dukda yaji daɗin ganin ƴaƴan nasu cikin aminci da kuma kishin Rumana daya hango a fuskar Ahmad ɗin kodan abunda yayi.
Rumana nason tace ya saki mata hannu amma tanajin tsoro, a haka suka shigo har cikin gidan sashensu, inda yake cike da Æ´an Shema matan da akazo dasu É—aurin aure.
Aiko abokan wasa sukai musu caa da sheri, shi saima lokacin ya fahimci tsiyar daya tafka, gashi sunyi ido huÉ—u da Gwaggo da Ayyah dake tsaye suna magana, gwaggo dai kallo É—aya tai musu ta É—auke kanta, Ayyah ko saita hau dariya mai nuna tsagwaron farin ciki.
Gasu Yaya Maryam daga gefe suma suna dariyar da kare su Ahmad ɗin daga sherin da abokan wasa suke masa akan ya kamo Rumana kamar yana tsoron kar wani ya ƙwace masa.
Murmushi kawai yayi ya saki mata hannu a hankali, ya sosa gefen wuyansa tare da takawa zuwa ga iyayensu Æ´an shema dake wajen.
Rumana kam ai tunda suka tsaya kanta ta sunkuyar kawai ƙasa, jitake inama ƙasa ta tsage ta shige saboda kunya, bata iya ta motsa ba sai da Ayyah tazo ta kama hannunta sannan, amma sai tafiya take a hahharɗe.
Ayyah ta ƙarasa da ita inda Ahmad ke durƙushe yana kwasar gaisuwa da saka albarkar dangin mahaifan nasu, durƙusawa itama Rumana tayi kanta a ƙasa bata yarda ta kalli kowa ba ta shiga gaishesu.
Wata dake matsayin yayar su babansu ce ta jawo hannunta tana faɗin, “Wannan ƴar tawa anya babu ajiyar mijina ko kishiya anan?.
Nanfa kowa ya shiga faɗin albarkacin bakinsa, Ahmad dai tunda ya saci kallon Rumana saiya miƙe dan yaga su Wasila abokan wasansu ba ɗaga masa ƙafa zasuyiba, shi kuma ba iya maida murtani yakeba dama can.
Wajen Ayyah ya nufa suma ya gaishesu yanata wani soshe-soshen kai, ita Ayyah ma saiya bata dariya.
★★★★★★