← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 94

Sashe 23

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yau gidan namu ya kasance na mutum Uku, dan kuwa amarya za'a kawo mana, amma dai bazawara ce kamar yanda Maman Ama ta sanar min.
Tun da hantsi Æ´an uwanta sukazo sukai mata jere, hakan yasani yini a É—aki dan ni bancika son sakewa cikin mutane da yawaba, musamman ma waÉ—anda ban saniba.
Ban sami nutsuwar zaman wajenba sai da suka wuce bayan la'asar, sannan ne na fito nai wanka, na dafa taliya dai-dai cikina dan nasan Yah Ahmad ba dawowa ci zaiba, tunda ya cemin yau yana da aiki sosai a shago, maybe shi da gida sai dare.
Daga nan ƙofata na fito na saka kujera ina duba buks ɗina na makaranta, dan ban fidda ran Yah Ahmad zai barni na zana koda ssce ne ba.
Jefi-jefi nakan amsa maganar Maman Ama da duk rabinta gulmar dangin baƙuwar amaryarmu ne da sukazo sukai jere.
Ni dai ban yarda nace komaiba, iyakata dariya ko nace ALLAH ya ƙyauta, daga ƙarshema da naga zata takurani sai na ɗauki kayan karatun na shige ɗaki kamar zanyi wani aiki a ciki, zama na nai, ban sake fitowa ba sai da aka kira magriba, nazo nai alwala na koma ɗaki, dan baƙi sunɗan fara shigowa, da alama dai dangin angone da zasu tarbi amarya.
Ni dai gaishesu kawai nayi nai shigewata.
Zan kabbara salla biyu a cikinsu suka leƙo wai na taimakesu da buta suyi alwala, miƙa musu nayi na kabbara salla ta, ina cikinyi suka shigo, ganin salla nake suka shinfiɗa tabarma suma suka tayar.
Koda muka idar basu fita ba, sai hira suke jana da ita, duk tambayoyin nasu dai akan son sanin nima amaryace?, ina É—an amsa musu abinda zan iya saboda naga sun girmemin sosai.

Muna idar da sallar isha'i ne Yah Ahmad ya shigo da sallama, ganin bani kaÉ—ai bace sai ya koma da baya ba tare da yace komaiba.
Hakan da suka ganine ya sakasu miƙewa suna min godiya, a tsaye suka iskeshi, suka gaidashi suna barin wajen zuwa ƙofar ɗakin maman Ama da sauran ƴan uwansu suke can sukai salla.

Sannu nai masa ina amsar leda viva dake hannunsa, wadda Ayyah ta sako masa kwanikan tuwo a ciki.
Da yauwa ya amsa yana zama a bakin gadon, “Waɗannan fa?� yay tambayar yana kallona.
“Uhm baƙine ƴan tarbar amaryar da zata tare a gidannan yau�.
Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru, saboda wayarsa da tai ring, É—agawa yay suna magana, wadda na fahimci dai akan É—inkine.
Kwanikan abincin na fiddo a ledar, koda na buÉ—e naga tuwo sai bance komaiba na maida na rufe.
Dai-dai ya ajiye wayar, hakan yasashi faɗin, “Da ruwan zafi a gidannan?�.
“Eh, akwai wanda na dafa ɗazun�.
Miƙewa yayi tsaye yana ƙoƙarin cire maɓallan rigar jikinsa mai dogon hannu, “Juye min shi naɗan watsa, zafi ya isheni banzo nayi wanka ɗazun ba�.
Da “To� kawai na amsa masa, na shiga bin Umarninsa tamkar yanda ya bada.
Bayan na haɗa ruwan bayin naje nakai masa, lokacin dana dawo harya cire kayan ya saka jallabiya, ya ɗauki kwandon soso da sosan sa ya fice. Ni kuma sai na kwashe kayansa da ya cire ya ajiyemin saman gado, a raina inata tseguminsa, wani lokacin sai naita ganin kamar Yah Ahmad bai karatu mai zurfi ba na boko, dan sam bashi da irin son gayunan da ƙwalisar samarin yanzu masu irin shekarunsa, yana dai da tsafta gwargwado, amma itama tunda abunnan ya faru tsakaninsa da Samina sai tayi rauni, jiba fa, rabonsa da wanka tun ƙarfe uku da wasu mintuna na yammar jiya, sai yanzune kusan takwas da rabi na dare zai sakeyi, inba sa'a ba daga haka kuma sai gobe da yamma.
“To ke ina ruwanki?� wata zuciyata ta faɗa cikin gargaɗina.
“Haka nefa wlhy� na faɗa a fili kamar mai bama wani amsa.
Kafin ya fito najiyo hayaniya ta ɗan fara cika gidan, da alama dai tawagar amarya sun fara shigowa...........✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WhgANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(15)*

...............Shigowa yay yana jan tsaki, da alama dai hayaniyar gidance ta bashi haushi, ni dai bance komai ba na amshi kayan wankan na fito waje danna zazzage ruwan jikin soson, ta wani ɓangare kuma na bashi damane ya kimtsa.
Ina kallon wasu suna nunani, da alama dai ana gulma tane, oho basu dameni ba, sai ma na É—auke kaina daga garesu.
GuÉ—ar data cika soron gidan ne ya tabbatar mana da cewar dai amarya ta iso, ilai kuwa sai gasu sun shigo da ita.
Ni dai ina daga ƙofar ɗaki ina kallonsu, har aka shige da ita ɗakinsa suna callara guɗa abinsu.
Murmushi na É—anyi, dan sun tunomin da randa nima aka kawoni gidan ina rusar ihun kuka.
“Sai kin gama kallonsu zakizo ki bani abinci ne?�.
Muryar Yah Ahmad ta maidoni hankalina, da sauri na girgiza masa kai ina faɗawa ɗakin jikina har ɓari yake.
Zaune na iskeshi saman tabarma, ya cire jallabiyar yana sanye da wando dogo mai taushi da riga, da alama dai na barcine.
Tuwon na zuba masa miyar kuɓewa ɗanya sai ƙamshi take, dukda babu nama a ciki girkin tsoffin mata irinsu Ayyah daban yake, musamman ma akan abinci irin na gargajiya da a yanzu yake gagarar matan hausawa, wata sai tai maka tuwon masara kaji tamkar ya jiƙe saboda tsabar rashin bashi nutsuwa.
“Kaɗan zaki saka� yay maganar idonsa nakan wayarsa.
Na amsa da to ina ƙoƙarin saka masa dai-dai misali a filet ɗin.
Koda na kammala sai na koma gefe zan zauna, amma sai ya katseni da cewar, “K mi kika ci?�.
“Da yamma na dafa taliya naci da mai da yaji, yanzu banajin yunwa�.
Baice min komaiba ya fara cin tuwonsa hankali kwance, kallo É—aya zakai masa kasan yanajin daÉ—insa sosai.

Yana tsaka da cin tuwon niko ina zaune gefensa kaɗan ina sauraren hayaniyar da gidan ya ɗauka mukaga an ɗaga labulen ɗakin kamar da gayya, da sauri na kalli ƙofar sai naga matashiyar mace ce ma, kafin nayi magana ta katseni da faɗin, “Mai ɗakinnan ruwan sha zaki sammin dan ALLAH�.
Miƙewa nai ina faɗin, “To� hakanne ya sakata shigowa gaba ɗaya tana kalle-kalle kamar ta ajiye wani abu a ɗakin, sai kuma naga ta fita da sauri tana cewa, “Ya salam, kuyi haƙuri dan ALLAH, wlhy bansan maigidanki na nanba�.
guntun Murmushi kawai nai mata na miƙa mata ruwa waje.
Ta amsa tana cewa “Na gode�.
Ni dai komawa nai ciki na zauna inda na taso, kallo É—aya kuma naima fuskar Yah Ahmad na fahimci yaji haushin abinda matar tayi.
Ni dai bance komaiba, kamar yanda shima bai tankaba ya cigaba da cin tuwonsa.
Bayan ya kammala yace na bashi ruwan wanke hannu.
Muƙewa nai na ɗebo a madaidaiciyar roba na kawo masa ya wanke, na fita naje na zubda, matar data roƙi ruwa ta bani kofina tana sake godiya.

Yanda naga ya ƙwanta da wurine na fahimci akwai damuwa, dan kuwa dai nasan ba barci yakeba tunanine kawai, kuma bazai wuce akan yaya Samina ba.
Haka kawai yau sai naji raina ya sosu, amma saina danne na maida kun nena ga ƴan kawo amarya daketa ƙoƙarin tafiya.
Zuwa wani lokaci gidan yay tsit, fita nai nayo alwalar barci na dawo ɗakin, na tura ƙofar na rufe da addu'a a bakina, na raɓa ta gefensa na haye gado nai kwanciyata.
Banma san lokacin da shima ya tashi ya kimtsa ya kwanta ba, ni dai tuni na jima a duniyar barci.
Chapter 23 · 0% Book details