Sashe 33
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Zuwa wannan lokacin maganar Ma'aruff ta shiga gidansu Samina, yayinda alakarsu ta sake ƙazanta sosai, dan tunda aka tsaida bikinsu wata biyu kacal sai yazam babu abinda Ma'aruff ke burin samu daga gareta sai jikinta.
Har takai dai yau yaci galabar rabata da budurcinta a gidan gonarsa, tasha kuka iyakar iyawa, shiko ya katsatstsareta da lallashi da daÉ—in baki akan ai babu komai tunda shine zai aureta, kuma bikin nasu duka saura wata É—aya ne kacal ai.
Tun tana kuka da ƙarfin zuciya har ta aminta da daɗin bakinsa, ya tainaka mata ta gyara jikinta, tare da saka abokinsa ya kawo mata magunguna da allurar rage raɗaɗi, ya kuma kaita Shop rite yay mata shopping na hauka da bai taɓa mata irinsaba, ya maidota hargida tare da bata maƙudan kuɗi.
Mudanseer dake shago Shi da Abu yana kallon yanda Ma'aruff keta saukema Samina kaya niki-niƙi, baki kawai ya taɓe ya ɗauke kansa danshi yanzu babu abinda ya damesa da ita.
Maimakon lokacin da aka shiga da kayan Mama gaje ta fahimci halin da Samina take ciki sai idonta yafi karkata ga manyan ledojin.
Duk uwa mai hankali aka taɓa mata yarinya, kuma yarinyar ta dawo gareta a randa abin ya faru dolene ta fahimci akwai matsala, dan duk macen da aka raba da budurci komai tsahon shekarun da take dashi babu aure wlhy sai taji daban, idan ko babu aurene fargabar fara yinta bata hanyar daya daceba koda itace takai kanta saikin sameta tattare da ita, iyaye kalubale ne agareku, dan yanzu har sai ƙaton banza ya gama lalata miki ƴa a waje ta ɗau ciki ta zubar bama ki saniba saboda sakaci da sakarci kosan duniya irin namu.
Da wannan damar rashin kulawar tamu samari keta lalata yara ta yanar gizo da zahiri ba tareda kun fargaba, damuwarki kawai ki gyarama mijinki kanki dacin kwalliyar tafiya biki domin ki birge mata ƴan uwanki, idan kishiyace dake hankalinki na kanta, saikiga ƙanin uban yarinya ko ƙaninki ko wani na kusa daku ya gama warware tufkar tarbiyyar da kukayi kina nan shatata da baki, sai rashin mutunci ya saka saurayi sakin videon baɗalar da yay da ƴarki a yanar gizo ki haukace har takaiki da faɗawa wani hali ki kamu da ciwon hawan jini kona zuciya, bayan kuma kinbar gini tun ran tubani.
A tunanina duk uwa datasan ƴarta budurwa nada wayar yakamata tazam mai saka mata idanu akan wayar, kodama bata da ita ki saka mata ido tunda akwai ta ƙawaye.
Tanan suke shiga yanar gizo su haɗu da ƴan iskan facebook, ko istagram, ko litatafan batsa dake yawo a kowacce irin kafa ta yanar gizo, ko ƙawa ta sakata a group da sunan group ɗin matan aure wanda idonsu ya rufe basajin tsoron ALLAH duk abinda yake haramun shine abun kallonsu, wanda yake haramun shine abin furtawarsu da jinsu a zuwan wai koyan rayuwar aure, ke wane kidahumancin ya baki tunanin sai an ɗakko shaiɗancin tsiraicin wani kin ganine zakisan yanda zaki rayu da mijinki?, wlhy matan aure kaiconku da wannan wawancin mai toshe ƙofofin hasken zuciya da kashe gani.
Ƴammata da yawa daga shiga irin waɗannan groups suna canja suna komai ke fara tabarɓare musu, idan k uwa baƙya bibiyar lamarinta daga haka sai kiga komai da kika gina ya tarwatse.
Wlhy kuzama masu kulawa kafin ku riski ranar kuka da nadama akan Æ´aÆ´anku, domin sai ALLAH yay miki tambaya dalla-dalla akan tarbiyyarta.
Wannan sakacin ne ya hana Mama gaje fahimtar komai akan Samina har Ammin su Umm-Rumana ita ta lura, ba ƙaramin ruɗani ta shigaba, sai dai tana tsoron tace wani abu aga zaƙewarta.
Samina kuwa kwanciya tai wahala ta sakata barcin dole, bata tashi farkawaba sai bayan sallar magriba, agaban mama gaje ta dafa ruwan zafi taje tai wanka dashi ta sake gasa jikinta kamar yanda taga ana cewa a novels, koda ta fito sama-sama taci abinci ta sake kwanciya, kobi takan kayan da mama gaje ta baza a É—akin bataiba saboda ita tasan wahalar da taci kafin ta samo kayan.
Haka Samina taita jiyyar jikinta har kwana biyu, ko É—aga wayar Ma'aruff batayi idan ya kirata saboda haushinsa da takeji, amma taji daÉ—in yanda ya nuna damuwarsa a kanta, sai turo mata massegea yake kamar hauka, wannan yasa a cikon kwana na huÉ—u ta kulasa.
Yako kalailayeta da daɗaɗan zantuka ranar, haryaci galaba a kanta tafito makaranta taje Office ɗinsa ta samesa, acan yakuma lallaɓata ya ƙara na biyu, ranarma taci kuka dan tasha wahala, amma daya lallaɓata da mayaudaran kalamanasa saita goge hawayenta saboda ta yarda dashi.
Tun daga wannan ranar ya maidata kamar wata matarsa, a gefe kuma yanata sakar mata kudi itada ƙawayenta suna shirin biki. Sati na biyu da kauda mata martabarta aka kawo lefenta daga gidansu ma'aruff akwati ashirin da huɗu cif, tare da katuwan jakkuna uku manya-manya, ɗaya na babanta, ɗaya na Mama gaje, ɗaya na danginta.
Ranar dai kam su Ayyah sunsha kallo, sun kumasha gori wajen mama gaje da danginta, ƴan anguwa kam ai kamar sa fasa gida kallon kaya, harda ƴan gayyar soɗi, dan ko su Maman Ama sai gasu sunzo ganin ƙwaf daga jin su Salima na sanarma Umm-Ruman cewar gobe za'a kawo lefen Yaya Samina.
Shine mutanenku sukai shiri Rumana bata saniba sukazo wai yimata kara tunda ita har yanzu bata fara zuwa gidaba baba Yusha'u ya hana, yace tai zamanta har Ahmad ya dawo ya bata izinin hakan, makaranta kawai take fita, shima kuma jarabawama suke zanawa ta ssce.
Ranar su Nafy ƙawayen Samina haka sukaita yawo da wannan lefe a social media, yayinda ya tadama ƴammata da yawa hankali da fatan suma sai an musu irinsa koma wanda ya fisa.
Harda masu takaicin inama sune, irinsu Kausar.
Koda sukaje suna bama Rumana labari tasha mamaki, dan ita bama ta kawo can sukajeba, amma sai batace dasu komaiba akan hakan dukda taji haushi.
_________________________________
Baba ne ya gindayama Ahmad sharaɗin ya tabbatar yazo gida anyi bikin Samina dashi, tunda shine namiji babba a gidan bai ƙyaitu ace baya nanba.
Dukda baiso hakaba dole yabi umarnin baba, tunda yanzu dai Alhmdllh, duk da bawasu maƙudan kuɗi ya samuba babu laifi tafiya tai riba, dama kuma ya gama shirinsa tsaf.
★★★★★★
Umm-Rumana duk da bata da tabbacin zuwa gidan bikin haka ta wanke kanta Salima ta yarfa mata kananun kitso, suka kawo ƙawarsu har gida tai mata ƙunshi mai ƙyau, haka kawai ta tsiri juya fasalin ɗakinta.
Tako tsare su Fa'iza suka tayata, komai suka canja masa muhalli ya koma kamar wani sabon ɗaki, aranar kuma su Samina ke shirya fatin ƙunshi a wani haɗaɗɗen hotel tsadajje.
Su Fa'iza duk sun gudu sunbarta ita kaÉ—ai a gidan, dan haka bayan tai wankanta tai kwanciyarta tana kwasar barcin gajiyar aikin da sukayi.