← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 94

Sashe 70

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lallai tunanin Samina yazo da ruɗani a gareta, ya kuma karanta mata ba dai-daiba, dan kuwa dai yau ango Ma'aruff ko lemon bai damu da shaba balle akai ga giya, yana manne da amaryarsa da sukasha soyayyarsu, duk da dai daga ƙarshe abin yazo masa da ruɗani, dan kuwa dai amarya a fafake take ba budurwa bace, wani ya ɗana.
Ance wanzami baya son jarfa, hakan yasaka hankalin Ma'aruff tashi matuƙa, ya hauta da bala'i ta taka masa birki nan take, dan ta tabbatar masa bazata ɗauki haukarsa ba, harda tambayarsa wai shi dama budurcinta ne matsalarsa?.
Wannan tambaya ta ƙonama Ma'aruff rai, sai dai ya gaza cewa uffan saboda wani shegen tsoron Mufida yaji ya mamayesa.

“Aiki ga mai ƙareka”😂⛹‍♀

___________________________________

Su Umm-Ruman masu jego kam an kammala wanka, tayi dumurmur da ita kamar ka sace ta ka gudu, hakama Haysam abin sha'awa, ga ƙyawun yaro da yay gado uwa da uba nata fitowa, dama iyayen kamarsu ɗaya, hakan yasa bama a iya banbance dawa yake kama a cikinsu, wasuma sukance ya ɗara iyayen ƙyau.
Ita kanta Rumana takan zauna taita kallonsa idan babu kowa kusa, a ranta tana ƙiyasta yanzufa wannan mallakinsune ita da Yayanta.
Hakan na saka zuciyarta farin ciki sosai, shi kansa Ahmad idan ya kira labarinsa mafi yawa nakan Haysam, wataran Rumana har nuna kishinta take a fili, shiko yayta mata dariya, hotunan Haysam kam ai kullum sai an masa an tura masa, idan ita batayiba ma Mudan zaiyi ko Abu da aka sayi waya shima ya shigo gari da ƴar mai shan jininsa😂.

Umm-Ruman ta fara ƙoƙarin zagaya dangi ziyara, wanda da farko da Ahmad yaso kawo tirjiya Ayyah ta taka masa birki akan dolema yasama ransa haƙuri tunda haka al'adar take, sannan tunda Rumana tai aure ina yake barinta zuwa? Tanada dangin mahaifiya a gari suma kuma ai suna buƙatarta, ga dangin gwaggo suma ya kamata ta ringa shiga.
Dole yay shiru yabi umarni kam, aiko saiga su Rumana har shema ita dasu fa'iza, kwannansu huÉ—u suka dawo da tarin alkairi, dan Æ´an Shema sunji daÉ—in wannan ziyara sosai.
Cikin ƴaƴan ƴan uwa kuwa wani ya maƙalema Fa'iza, kuma da gaske yake babu ƙarya, itama dai Fa'izan ta amsa, dan yay mata, sai dai fargabarta batason zama Shema kamar yanda ta sanarma su Rumana.
Sun bata shawarar addu'a kawai da neman zaɓin ALLAH, dan yafi kowa sanin abinda ya tsara.
Da zaman wankan Rumana, da ziyarce-ziyarcenta kusan watanni biyu da wasu Æ´an kwanaki da tafiyar Ahmad.
Dan haka ya fara shirin zuwa gida, sai dai a wannan karon yasha banban da zuwan baya, dan kuwa zaizone domin ɗauke matarsa da ɗansa su koma kusa dashi kamar yanda iyayensu sukai masa alƙawari.
Ranar juma'a kwatsam babu zato sai gashi, kowa yayi murnar ganinsa kuwa, musamman yara da sukasan zasuci tsaraba kamar yanda ya saba kawo musu.
Ita dai Rumana duk wannan bikin murnar dawowar Ahmad da ake tana sashensu tanaji amma bata zoba, yaga dai Haysam dake goye a bayan Zainab yana barci.
Bayan yasha ruwa ya miƙe kamar yanda ya saba domin gaida matan gidan dasu iya.
Sashensu Iya ya fara shiga, ya gaisa da kakanninsa daketa tsokanarsa da cewar angon zumuÉ—i.
Shi dai dariya kawai yakeyi, dan kuwa dai sun gama ranfosa.
Koda ya fito sai ya shiga Sashen baba iliyasu, nanma ya gaisa da matansa sannan ya nufi sashen su Umm-Ruman, dan tunda bai gantaba asashensu yasan tana nan.
Sai dai anan É—inma bai gantanba harya gama gaisawa da Ammi, ita mama gaje ma bata gidan.
Duk kuma Rumana na jinsu, dan tana ɗakin baba tana masa shara, hakan yasa taita leƙen Ahmad ta window ba tare daya saniba.
Shima dai haka kawai zuciyarsa da idanunsa suka karkata ga É—akin baban, sai yakeji kamar akwai abunsa mai muhimmanci a cikin É—akin.
Yana fita kuwa Ammi ta ƙwalamata kira.
Fitowa Rumana tai da sharar data kwashe tana amsawa.
“Ammi gani�
“Na ganki ai, k bakiji mijinki ya dawo bane?�.
Shiru Rumana tai bata iya cewa komaiba, ta dai duƙar da kai ƙasa, itama Ammin bata sake ce mata komaiba tama ɗauke kanta daga gareta baki ɗaya.
Sai da ta kammala abinda takeyi sannan ta nufi sashen su Ahmad É—in a kunyace, dan Ammi sai antaya mata harara takeyi.

Tunda tai sallama Ahmad dake zaune riƙe da Haysam daya tashi barci ya zuba mata idanu, itako taƙi kallon sashensa.
Ayyah tace, “Ɗiyata aida yanzu zanje biko, dan ko abinci na hana mijinki nikam sai kinzo�.
Murmushi Rumana tayi, aɗan in ina tace, “Shara naima Baba Ayyah�.
Ɗauke kai Ahmad yay daga kallonta ya maida ga Haysam, ji yake kamar ya haɗiye ɗan yaronsa, a ƙasan ransa kuwa yana tuno yanda yaji akan ɗakin baba, ashe kuwa tana ciki.
Duk wannan hidima da akeyi Gwaggo na É—akinta, tunda suka gaisa da Ahmad tai shigewarta É—akinta.

Umm-Rumana ta taka inda yake, kujerar dake gefensa kaɗan taja ta zauna, “Sannu da zuwa Yaya, ina yini?�.
“Sai yanzu aka san dani?�.
Yay maganar yana wasa da hannun Haysam.
Ita dai tunda tasan tayi laifi sai tace yayi haƙuri kawai, ta miƙe ta amso abincin da Ayyah ke kiranta ta ɗauka masa takai ɗaki.
Sai da ta shiga da kusan mintuna uku sannan ya shiga É—auke da É—ansa.
Tana ƙoƙarin zuba masa ya shigo, hakan yasa bata fasaba bakuma ta kallesu ba shida ɗan nasa.
Shiko ya kasa ɗauke idonsa a kanta, dan ƙyawun data ƙara da ƴar ƙibar datai mata ƙyau sunyi mugun tsole masa idanu.
Gabansa ta tura komai sannan ta ɗago ta kallesa, irin kallon da yake binta da shi na ƙurulla ya sakata jin kunya, tai murmushi tana ɗauke nata idon, “Yaya wai kallon fa?�.
Ajiyar zuciya ya sauke kaÉ—an yana janye idonsa da salon lumshewa.
Bai iya cewa komaiba, sai cokali daya É—auka zai fara cin abincin.
Katsesa tai da faɗin, “Kawoshi to yanda zakaji daɗin cin abincin�.
Bai musaba ya buɗe hannayensa alamar ta ɗauki Haysam ɗin dake kan cinyarsa, sai faman watsal-watsal yake da ƙafafu na lafiya da ALLAH ya bashi.
Tasowa tai ta duƙo domin ɗaukarsa, hakan ya basu kusanci sosai ita dashi, dan har suna iya jin saukar numfashin juna, kowa na shaƙar daddaɗan ƙamshin jikin ɗan uwansa, gashi yanda wuyan rigar yake daɗan girma ya samawa idon Ahmad abinci.
Ita dai tsigar jikinta na tashi ta É—auki Haysam a kasalance ta matsa baya.
Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya fara cin abincinsa.

Kamar jira Haysam keyi ta ɗaukesa ya fara ƙananun kuka, banza tai masa, a ranta tana fadin, “Kujimin yaro da neman dalili?�.
Ahmad ya ɗago ido ya kalleta da mamaki, ga yaro na kuka amma tayi biris, kafin yay magana Ayyah dake waje tace, “Waishi wannan alhajin baza'aji da shi bane Rumana? Kema kinsan yunwa yakeji tunda barci ya tashi dama�.
Rumana tace, “Ayyah rigimace fa kawai, gashi nan zan bashi ruwa�.
Ayyah tace, “Ruwan ƙaniya, ki bashi nono kafin nazo kanki�.
Rumana ta dingure kan Haysam sannan taja hijjab ta saka wai batason Ahmad ya ganta, a haka ta fara Shayar dashi, shiko yaro kamar yasan za'aima ubansa buƙulu yaƙi amsa saboda zufar dole da aka ƙirƙirar masa.
Cikin haushi ta cire hijjab ɗin tana faɗin, “Kai wai ba a sirri da kai dan maigarin garinku?�.
Murmushi kawai Ahmad yayi yana É—auke idonsa daga kallonsu.
“Yaga za'a cuci masa Abbansa a hanashi ganin halalinsa ba dole yay boreba� Ahmad yay maganar ba tare da ya kalli Rumana ba.
Baki ta kumbura, amma bata tankaba, sai harar Haysam takeyi kamar yasan tanayi😝.
Shidai Ahmad ya samu tv, yanacin abincinsa yana kallo.
Rumana dai kasa jure wannan kallo tai, ta samu da Haysam yaÉ—an sha ta ciresa tana gyara rigarta, dai-dai lokacin Mudan ya shigo É—akin bayan yayi sallama sun amsa Ahmad ya bashi izinin shigowa.

“Ashe da gaske yaran nan suke kaiɗinne dai?�.
Murmushi Ahmad dake Kallon Mudan yayi, yana ƙaunar ƙanin nasa sosai, hakama Rumana dake ƙoƙarin miƙewa ta basu waje.
Mudan ya amshi Haysam daga hannunta yana gaishe da Yayansa, ita kuma ta fice a binta.
Bata sake shiyowa É—akinba. suko sunata hira abinsu, sai da aka kira sallar magriba Ahmad yabar gidan zuwa can gidansu, dan tun shigowarsa su Fa'iza suka tafi gyarawa.
Maman Amatullah kawai ya iske a tsakar gida tana shara, sai maman Aysha data shigo suke ƴar gulmarsu, kuma kamar an saita sunayi da Rumana ne akan wai taƙi dawowa.
Sai su Ahmad dake wasan ruwa a bakin rijiya shi da Amatullah.
A bazata sukaji sallamar Ahmad, wanda sarai yaji kalmar maman Aysha ta ƙarshe saboda bata magana a hankali ita dama.
Duk sai suka daburce wajen gaishesa da masa sannu da zuwa, shi dai ya amsa kawai ba tare da ko kallonsu yayi ba, Mudan yasa makulli ya buɗe masa ƙofar suka shiga.
Ko zama Mudan baiyiba ya fito yabar Ahmad.
A zuciyar Ahmad godiya yakema UBANGIJI da ya tsame matarsa ga wannan muguwar al'adar, shi sam bata birgesa tun ma yana yaro, sai kuma ALLAH ya soshi Ayyah da Gwaggo babu ruwansu da irin wannan tsogume-tsogumen ma.
Ya fito wanka yana alwala Kausar ta shigo itama, ashe gidan sunan ƙawarta taje, gaisawa sukai tana binsa da kallo.
Shi dai da baisan tanaiba ma tuni ya miƙe ya saka butar ɗaki ya fice abinsa.
Aiko kamar jira take ta nufi kicin inda maman Ama ke girki.
“Maman Ahmad wannan matar kuwa zata dawo? Ƙiri da muzu ta maida miji gwauron ƙarfi da yaji�.
Maman Ama ta fito tana taɓe baki, “Wlhy maman Siyama yanzu muma muka gam ni da maman Aysha, yanzu dai ai zamusha kallo, tunda ta gama wanka ga kuma miji ya dawo maji ma gani�.
Baki Kausar ta taɓe tana ƙoƙarin sauke Siyama dake goye a baya ta tashi barci, taja kujera ta zauna alamar koma ɗakin bazata shigaba balle tunanin yin salla.
Nanko suka sake buÉ—e babin gulmar Rumana da batasan sunaiba.

___________________________________
Chapter 70 · 0% Book details