← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 94

Sashe 30

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahmad kam Sufyan ya iske yana jiransa da mashin a ƙofar gida, dan haka ya haye suka ɗauki hanyar tasha.
Koda suka isa sai suka iske mota ana mata lodin zuwa garin porthercout, babu wani tunani aran Ahmad ya faɗa bisa shawarar Sufyan, motar dama dai ta gama cika, gurin mutum ɗaya ya rage rak, Ahmad na shiga suka tashi, har motar ta fice a tashar suna ɗagama juna hannu shi da Sufyan...............✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_GDW_*

*(18)*

...........Taci kuka sosai harta godema ALLAH, dole masu iya magana suce sabo akema kuka ba mutuwa ba, harta fara jiyo motsin maman Ama da yaranta a tsakar gida ita batai ko yunƙurin tashiba, ahakama barci ɓarawo ya sake saceta, saboda jiya sun daɗe basu kwanta ba.
Gaba É—aya barcin nata sai ya kasance mafarkin Ahmad ne.

Kusan goma Kausar ta fito daga ɗakinta zatayi brush, tabi tsakar gidan da kallo kafin takai dubanta ga maman Ama dake can ƙofar ɗakinta tana haɗa zoɓonta na saidawa.
“Yau gidan namu bai samu ƴar sharar safenba kenan? Ko gimbiyar tamu babu lafiya ne?�.
Ƴar dariya Maman Ama tayi, taɗan taɓe baki cikin iya gulma tana faɗin, “Zaune dafa'an murar kwaɗo, inaga dai kewar tafiyar maigidace ta hanata fitowa�.
“Yo ina mijin ya tafi?� cewar Kausar tana matsowa kusa da maman Ama.
“Uhum wai neman kuɗifa, Kausar nifa wlhy mijin yarinyarnan sai naga tamkar bai taɓa riƙe biroba balle akai ga zaman aji, amma waifa nan inda yake digiri garai�.
Cikin tsantsar hassada Kausar tace, “Yo digirin banza, maman Ahmad ai yanzu wannan ruwan dare ce, ALLAH ma yasa ko a ajin ba na ƙarshe yake ɗaukaba, ita da ba uwar wani abu ya taɓa mataba ma miye na damuwa dan ya tafi mtsooow�.
Dariya sosai Maman Ama keyi, tace, Kijiki da wata magana, idan baiyi mai gaba ɗaya ba, kika sani ko yanayin ƴan kananun ayyuka, duk namijin dai da zai kwana da mace ɗaki ɗaya bai iya mata komaiba ai idan kaji gangami da labari, ALLAH sai dai idan bashi da lafiya ne�.
“Nimafa nayi wannan tunanin wlhy, ko ogana da ina bashi labari cayaymin sai dai idan mijin baida lafaiya, amma wane lusarine za'a kawoma budurwa kamar wannan ya iya kallonta ya kauda kai kuma su kwana lafiya su tashi a ɗaki ɗaya�.
“Kin daiji magana, wlhy hasashenmu duk ɗayane, inaga baida lafiya dai sai yake fakewa da damuwar dan waccan ta ƙisane�.
Sosai suka kwashe da dariya, har suna haɗa baki wajen faɗin “Tamɓele kenan�.

Duk wannan shagali da suke Rumana ma batasan sunaiba, barcinta take abinta.
Bata farka ba sai kusan sha biyu, ta tashi a firgice da mamakin barcin da ta sha, brush da buta ta ɗauka ta fito, Kausar da maman Ama na tsakar gida zaune, Kausar na tsifar kai daga ƙofar ɗakinta maman Ama kuma na tsince shinkafar da zata girka.
Su duka zubamata ido sukai tamkar yaune suka fara ganinta, Rumana ta gaishesu tana tambayar inasu Ahmad.
“Suna ƙofar gida, amma lafiya kuwa da barci har rana Amarya?�.
“Lafiya lau maman Ama, kainane kawai kemin ciwo kaɗan-ƙaɗan�.
“Ayya to ALLAH ya sauwaƙe�. Mama Ama tai maganar suna kallon juna da Kausar kowanne na taɓe baki.
Kausar tace, “Amin, to Amarya ko dai mun samo baby ne?�.
Murmushi kawai Rumana tai mata ta ajiye brush ɗin ta ƙoƙarin shiga bayi ta tsinkayo maman Ama nabama Kausar amsar tambayarta......,
“Hhhh kema Kausar akwaiki da son zance dai, kin taɓa ganin gonar da ba'a taɓa mata ko gewaya ba ta fidda tsirrai? Dama kin tsaya a abinda ta faɗa ɗin yafi�.
Naɗan ciza leɓena dukda ban gama fahimtar zancen nasuba nasan akwai shaƙiyanci a ciki, yanda suka kwashe da dariya kawai ya tabbatarmin da hakan.
Sosai ƙyanƙyami ya kamata ganin bayin duk datti, dan bata tashiba baza'a samu wanda zai tsaftaceba, sai kace ita kaɗai ke amfani dashi, waje ta dawo tai brush ta koma ɗaki abunta.
Bata zauna ba ta hau gyaran ɗakinta, sai da ta kimtsa komai tsaf tayo shara ta goge ledan da ruwa da omo tasa turaren wuta sannan ta dawo sharar waje, har lokacin kuma su maman Ama ana zaune ai ana gulmar maƙwafta, wance tayi kaza wance tace kaza.
Rumana dai bata saka musu bakiba harta kammala sharar tsakar gidan taja ruwa a rijiya, tana ƙoƙarin fara wanke ƴan kwanikan da sukai amfani dasune mijin Kausar ya shigo gidan, gaidashi sukai ita da maman Ama.
Maman Ama na ganin Kausar da mijinta sun shige sai ta É—akko boket tazo gaban rijiya É—ibar ruwa.
Dama ina kallon yanda take hararar ledar hannun mijin Kausar kamar idonta zai faɗo ƙasa.
Tana zira gugar ne take faɗin “Amarya bakiga mutuniyarki ana karya ƙugu su miji ya kawo cefane ba, batasan munsan komaiba yanzu, sai abinda kishiyarta tace miji keyi�.
Murmushi kawai nayi amma bance uffanba, maimakon maman Ama taji haushi tai shiru itama sai ta cigaba da zaro zance akan Kausar, azamar kammala abinda nake nayi nabar wajen ina faɗin, “ALLAH ya ƙyauta to�.
Ina kallo ta bini da wata harara tana taɓe baki, na girgiza kai kawai na ɗauki ruwa da omo naje na tsaftace bayin sannan nazo na ɗiba ruwan wanka a rijiya.
Har lokacin kuma Kausar basu fitoba, maman Ama na zaune tana facing É—in É—akinsu tamkar mai hango abinda sukeyi a ciki.

Lokacin dana fito wanka sai haÉ—iyar zuciya take, harda dukan Amatullah.
Ni dariyama ta bani, na shige É—aki abina inayin kayata a zuciya.
Ƙin fitowa nai, ina shirin ɗora taliya a ɗaki sai ga sallamar Zainab.
Ta shigo É—auke da kwanon silba.
Cikin ɗokin ganinta nake faɗin, “Ga autar gwaggo ga autar Ayyah�.
Itama dariyar takeyi da cewa, “Kai Yaya Rumana, sai kace wadda tazo daga legas�.
“Lallai yarinya, kinsan kuwa yanda nakejin daɗi idan na ganku, daga ina haka?�.
“Daga gida nake, Ayya ce tace na kawo miki wainar rogo da mukayi�.
“Kai-kai kice yau daɗi kukeci a gidan malam ɗin?, duk ni kaɗai wannan?�.
“Eh mana� Zainab ta faɗa tana ƴar dariya.
Na kashe rishon ina cewa, “Aini to nama fasa dafa komai, wannan kam tama isheni�.
Zainab data kwanta a tabarma tace, “Ai aunty fa'iza ma tace anjima zasu taho itada aunty Salima nan, tace karkiyi girki zasu yo muku taɓa ka lashe�.
“To ALLAH ya kawosu lafiya�.
Haka Rumana ta zauna taci wainarta ta rogo tai nak, sunata hirarsu da Zainab, har aka kira sallar la'asar sannan ta miƙe alwala, itama Zainab alwalar tayo sukai sallah, bayan sun idar ta bata naira talatin kuɗin napep da aya da gyaɗa tace taje gida kar a nemeta.
Godiya tai mata ta wuce, itako ta jawo littatafan makaranta ta hau dubawa.

_______________________________
Chapter 30 · 0% Book details