← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 94

Sashe 79

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

.............A gidan Gaddafi suka yada zango, dan Hafsat tace itace mai tarban.
Sun iske abinci kuwa mai rai da lafiya na musamman da aka shirya domin su, yanda Rumana ta sake da Hafsat sosai ya faranta ran Ahmad, dan ya kula Babie R É—insa ta sake wayewa sosai fiye da sanin da yay mata kafin tahowarsa.
Sai kuwa satar kallon juna suke ita da shi suna sakarma juna murmushi.
Bayan sunci sunsha kowa yay nak sukai shirin tafiya gidansu suma.
Gaddafi dake miƙewa yace, “Ai sai dai ku tafi ku biyu, amma ni nan a barmin ƙanwata Zainab da yarona kuma surukina Haysam sumin kwana biyu kafin su biyo bayanku ko Zainabu?� ya ƙare maganar da kallon Zainab.
Babu musu Zainab dake riƙe da Subayya ta amsa cikin ɗoki, dan batason a rabata da ƴar ƙyaƙyƙyawar yarinyar dama.
Murmushi Ahmad yayi, dan sarai ya fahimci abokin nasa kuma ɗan uwansa a wannan ƙasa dama ya basu suje su more kewarsu shi da Gwal ɗinsa.
Da alama kuma shirin harda Hafsat a ciki, dan É—aki ta janye Rumana ta bata wasu abubuwa akan suna zuwa gida yanzu kartai sanya tai amfani dasu.
Murmushi Rumana tai tayi tanama Hafsat godiya, dan Hafsat zata iya girme mata, saboda ita tayi karatu har matakin masters ma kafin ALLAH yay aurenta da Gaddafi, amma da yake tanada ƙaramin jiki bazaka taɓa kawo cewa ta girmi Rumanan ba, kasancewar ana cikin yanayin jin daɗi kuma Hafsat akwai gaye da tsafta.
Wayo akaima Haysam suka gudu, to saima akai sa'a shi bai farga da fitar tasu ba, hankalinsa na kan Baby Subayya gaba É—aya.

★★★★�

Ahmad dake tuƙa motar Gaddafi da suka taho a ciki sai faman murmushi suke suna shaƙar ƙamshin juna shi da Gwal ɗinsa.
Amma abin mamaki bakunansu sun gaza furta komai, yakan juyo dai ya kalleta lokaci-lokaci, itama dai satar kallonsa taketayi ta gefen ido.
A cikin wannan yanayin dai ALLAH ya kaisu gida lafiya, sosai gidan yayma Rumana ƙyau, duk da kasancewar madaidaici kuma basu kaɗai bane, amma sashen kowa daban dan ɓangare ukune a gidan, kuma duk haya suke a ciki.
Bayan Ahmad yay fakin ya zagaya ya buÉ—ema Rumana itama.
Wannan girmamawa ta ƙayatar da ita sosai, tai murmushi tana miƙa masa hannu kamar yanda ya miƙa mata nasa shima.
Babu wanda baiji wani sabon yanayiba tsakanin a jikinsa ba shi da ita lokacin da suke rumtse hannayen cikin juna, amma sai ko wanne ya fuske abinsa saboda tsaro ba tsoro ba😎🥺.
Sai da ya É—auki wasu kayan sannan ya nuna mata hanya alamar suje, tai guntun murmushi itama tana É—aukar akwatin Zainab daya rage dan basu wani kwaso kayaba kamar yanda yace mata, akwatinta babba ita da Haysam, sai na Zainab É—an madaidaici, sai Handbag É—inta da wata jikka itama dai madaidaiciya.
Kansa ya girgiza mata alamar ta ajiye zai ɗauka, amma sai ta noƙe kafaɗa tare da girgiza masa kai itama.
Ya lumshe ido yana kaÉ—a mata kai alamar suje to.
Gaba yay tana binsa biye har ciki. Sosai gidan ya kuma ƙayatar da Rumana, dan ya haɗu babu ƙarya masha ALLAH.
Rayuwa kenan, duk mai rai baya yanke ƙauna da rahmar ALLAH, ko a mafarkinsu basu taɓa tunanin zuwa wannan matsayinba a rayuwarsu........
Rungumetan da taji anyine da zare a kwatin hannunta ya sata kawo numfashi mai ƙarfi tana dawowa duniyar mutane, kallonsa tai, shima idanunsa a kanta.
Ya zare handbag ɗin hannunta yana kuma mannata da jikinsa, su duka sauke numfashi suke a gurguje saboda tsigar jikinsu dake mimmiƙewa.
Umm-Ruman ta ƙanƙame Ahmad itama tana sake masa wani kuka mai tsuma zuciya da ruhin masoyin ƙwarai daya fahimci na shagwaɓane kawai.
Murmushi Ahmad yayi yana ɗagota jikinsa, idanu kawai ya zuba mata ganin yanda take hawaye harda shashsheka, ya sake murmusawa yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa maiɗan ɗaci tare da jinginata da bangon da suke gab dashi.
Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta tare da ɗora bakinsa kan nata......😚🤫

Komai cak ya tsayama musu, ji da ganinsu gaba ɗaya baya tare da duniyar mutane, takai har ƙafafunsu na neman gaza ɗaukarsu, ganin suna neman zubewa a wajen Umm-Ruman ta janye da ƙyar tana faɗawa ƙirjinsa ta ƙanƙamesa.
Bashi da zaɓin da ya wuce shima ya ƙanƙametan, suka durƙushe ƙasa a tare suna sauke huttai tamkar waɗanda sukai gudu a sahara.
Sunja kusan mintuna biyar a wajen basu iya tashiba, babu abinda suke faÉ—ama juna sai irin kewar da sukayi da nisan da ya jawo hakan.
Ahmad dake kallon bakin Umm-Ruman tana zubo masa bayani ɗunbin kewarsa da tayi ya shafa fuskarta yana haɗiye ƙwallar data taru masa a idanu na tausayin kansu.
“Gwal ɗina ke ta dabance a duniyata, bakina yayi kaɗan wajen furta miki kalaman godiya ko kewa da ƙishirwar jinki a kusa dani dana tsinci kaina a wattani goma sha ɗayannan, kinriga da kin zama Ahmad, Ahmad ya zama ke tuni, kece zuciyata, kece jinin jikina, kece farin cikina da komaina matata, ashe kema haka kike sona?�.
Sake ƙanƙamesa Rumana tayi tana dariya yanzu, shima dariyar yake mata, da ƙyar suka miƙe a wajen manne da juna.

________________________________

Bayan sunyi wanka Ahmad ya fita gabatar da sallar magrib da Isha'i, yabar Rumana itama zatayi anan.
Kafin ya dawo duk abinda Hafsat tace tayi sai da tai abunta, dama gashi kafin su tahi Ayyah da Iya sun mata tsumawa ta musamman, Yaya Maryam ma da tata gudunmawar, banda wanda itama taima kanta a bayan fage.
Kasancewar cikinsu taf yake basa tare da yunwa Ahmad ya shigo musu hannu rabbana, dan jiya duk wani sayayya data dace ya yita a gidan na kayan abinci, to sai yazam harda fruits duk ya ajiye gwargwadon ƙarfinsa.
Koda ya dawo É—in zaman gaisawa sukayi da tambayar Æ´an uwa da abokan arziki.
Daki-daki kuma take sanar masa da saƙon gaisuwar kowa yake masa.
Yaji daɗi kuma yanata amsawa da godiya, daga ƙarshe dai hirar ta canja sabon salo zuwa......🤫.

😚to babu ruwana, su o'e an buɗe kunnuwa aji, salon aje wajen malam ace Bilyn Abdull ce ta hiɗi😌😏🤣⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀.

★★★★�

Rumus Umm-Ruman ta tashi a wannan rana, dan da gaske dai Ahmad ya fanshe watanninsa na kewa.
Kallo guda zakai musu ka fuskanci É—unbin farin cikin da suke ciki, ALLAH ya sosuma ranar tazo a ranar hutu bazaije makaranta ba, amma ya dace yaje wajen business dinsu da sukeyi da Gaddafi kamar yanda ya saba a duk randa baida karatu.
Sai dai ba zai iya hakanba, to tunma da safe Gaddafin ya kirasa akan ya hutashshesa basai ya fitoba.
Hakanne ya saka Ahmad sake bararrajewa sukai ramuwar barcinsu na dare da ya gagara.
Koda suka tashima tare suka shiga kitchen suka haɗa abincin rana dan ba'ace masa breakfast ba dai😹.

A wannan yini dai gaba É—ayansa a kogin soyewa da rushewa waÉ—annan ma'aurata sukayishi, suna manne da juna kowa na bama É—an uwansa labarin abinda akai a watanni 11 da basa tare, sai kiran Æ´an gida da Ahmad yayi suka gaisa.
Washe gari ma har rana Ahmad na gida, sai da ƙyar da yamma ya iya fita makaranta saboda yanada lecture ɗin yamma.

Kwannan su Umm-Ruman biyar da zuwa saudia sannan su Haysam suka dawo nan gidan, familyn Ahmad ya dunƙule waje guda kamar yanda ya daɗe yana kewa.
Dan danan shaƙuwa ta shiga tsakaninsa da Haysam sosai, dan yana jansu a jiki shi da Zainab dansu sami farin ciki daga tsamosu a dangi da yayi, soyayya kuwa shida Gwal ɗinsa ai ba'a cewa komai.

Suna da watanni biyu da zuwa saudia Ahmad ya nemawa Zainab makaranta, shima Haysam kuwa aka sakashi, duk da ma dai Gaddafi ne ya ɗauki nauyin saka Haysam makaranta dan yana ƙaunar yaron, haka zasuzo su ɗaukesa yaje can yay musu kwana biyu.
Wannan yasa Haysam yazama mai gida biyu, yau yana gidansu gobe yana gidan Gaddafi, idanma akai kwanaki ba'a kaisaba sai yayta kuka yana kiran sunan Ubaya, (Subayya kenan yake nufi😂).
Itama dai Umm-Ruman ɗin Ahmad yanada burin sakata makarantar, danshi dama can mai sha'awar son ganin iyalinsa sunyi zurfi a karatune, hakan yasa yaji bazaiyi ƙasa a gwiwa ba, dukda shi bamai ƙarfi bane zaiyi ƙoƙari da abinda ALLAH ya hore masa insha ALLAHU, tunda da dai karatune ya kawosa ƙasar ba kasuwanciba, amma duk da haka babu abinda zai cema UBANGIJI sai Alhmdllh.
A gefe kuma yanata zuba ido yaga gwal ɗinsa ta fara laulayi, dan Ahmad yay ƙwarin da ko ciki ta samu a yanzu basu da wata damuwa, ballema yaron yanada girman jiki, hakan yasa ta yayesa tun yanada shekara ɗaya da rabi, gashi yanzu har yanada skekara biyu da wata ɗaya.
Tom ALLAH dai bai kawo É—inba, sai dai a cigaba da fata.

_______________________________

*_NAGERIA🇳🇬_*
_Ya kamata mu waiwayi Samina matar manya😉😌_⛹‍♀
Chapter 79 · 0% Book details