← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 94

Sashe 88

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A asibiti sosai su Inna mari sukaji ciwuka, gashi duk sun galabaita, dole dai aka basu gado, tare da taimakon gaggawa, komai Mudan ne ya biya na asibitin, dan sai da aljihunsa yay kankat harya haÉ—a da cin bashi.
An kwantar dasu tsahon kwana uku kafin a basu sallama.
Daga Mama gaje har inna mari sunsha kuka bisa wannan tashin hankali, dan tun daga wannan lokacinma dai Inna mari lafiya ta gagareta, sai da ta kaita da kwanciya cutar ajali, haka zataita rusar kuka da sambatu, tare da kiran sunan Samina ta yafe mata, sai dai ina Samina batajinta, hasalima tana É—aya daga cikin waÉ—anda Saminar tafi tsana a yanzun a duniya.
Takai kusan watanni uku tana jiyya ALLAH yay mata rasuwa.
Wannan mutuwa ce ta kuma susuta mama gaje, lamarin da ake tunani na taɓuwar hankali ya sake bayyana a gareta, dan itama haka kawai saita kama surutai, kokuma tai zaune jugum ba im ba im-im, saita haɗa kwana biyu bataima wani magana ba, komai sai dai tayita binsa da idanu.
A lokacin Ahmad har waya yasa aka bata yay mata gaisuwa, sai dai ko Umm-Ruman bai sanarma rasuwarba, dan tana fama da laulayin cikin Abu-Talib lokacin.

Ɓangaren su Ma'aruff kuwa sai komai ya koma yay lif, dan mahaifin Mufida ya fahimci bazasu sami abinda sukeso ga Ma'ruff ta wannan hanyarba, dole ya tirsasa Mufida ta koma lallaɓa Ma'aruff.
Sai dai lallaɓawar sam batai amfaniba, dan shan giyar da yake ta kuma ɓaci sosai, Har takai hantarsa ta taɓu ba tare da kowa ya saniba, a tsaitsaye ya fara ciwo tamkar wasa, tun yana ɗaukar lamarib ba komaiba har abun ya kaisa ga kwanciya, dukda mufida tasan baida lafiya taƙi faɗama mamansa ta kuma ƙi taimakonsa zuwa asibiti, saima takurama rayuwarsa da tai da batun ɗakko takardun nan.
Jikin Ma'aruff yayi matuƙaryin tsamari, har takai ranar ya gaza a yin komai yana ɗaki kwance rijib, yanaji wayarsa na ring tunda farar safiya amma ya kasa ɗauka ya duba wanene mai kiran, gashi sam baiji koda motsin Afrah ba a gidan balle na Mufida.
Hawaye masu zafi suka gangaro masa a kumatu, inda zai iya da tuni ya É—auki wayarnan ya kira Mominsu ya shaida mata halin da yake ciki ko zai damu taimako daga garesu.
Har kusan azhar babu motsin Mufida, hakanne ya tabbatar masa bama ta gidan, koma bata kwana a cikinsaba, dan tun jiya da magriba dama yaji kamar motsin fitarta, daga nan bai sake jinta ba, to duk zatonsa kodan yayi barci da wurine harta dawo bai saniba, sai dai zuwa yanzukam yaji a ransama bata dawo ba tun jiyan.
Jiyo knocking ƙofar da ake da ɗan ƙarfine ya katse masa tunaninsa, dagaji dai ba bugune na lafiya ba, gashi duk yanda yaso tashi ya gaza hakan, kuma yana tunanin Mufida kullesa tayi....
Bai kai ƙarshen tunaninsaba ya jiyo maganar mai gadi sama-sama yana faɗi musu anya kuwa yana nan?.
Sai kuma ya jiyo maganar Mominsu kamar tana kuka, ya rimtse idanunsa zuciyarsa na sake salon bugu, dan kuwa dai tabbas yaji a jikinsa babu lafiya......
Maganar ƙanwarsa data zagayo ta bayan Window ɗin ɗakinsace ta sakashi jin sassauci, ta shiga sallallami ganinsa kwance a gado da alamar yana cikin mawuyacin haline, da gudu tabar wajen tana ƙwala kiran sunan mominsu da tabbatar musu yana ciki kwance.
Nan take suka fara ƙoƙarin ɓalle ƙifar, cikin amincin ALLAH suka sami nasara da taimakon baba mai gadi.

Yanda suka shigo suka iske Ma'aruff ya kuma birkita dukkanin tunaninsu, suka shiga share hawaye da jera masa tambayoyi, sai dai bai iya basu amsar ko guda ɗayaba shima, sai binsu da kallon tsoro yake ganinsu duk da raunuka a jiki an liƙe da bandeji.
Babu maganar jan dogon zance sukai ƙoƙarin cewa a kaisa asibiti, duk da sunsan basu da ko sisin kwabo tare dasu, amma suna tunanin shi ƙila a samu wani abu a accaunt ɗinsa tunda da alama su Mufida basu taɓa komai na nan gidanba.
Ramar da yayice ta saka suka iya É—akkosa su uku ba tare da sunji wani uban nauyiba sam, suna shirin sakashi a motane wata motar tai hon, hakan yasa Momi cewa maigadi yaje ya buÉ—e gate yaga wanene?.
Babu jimawa sai ga baba maigadi ya dawo a kiÉ—ime, momi ta shiga tambayarsa ko lafiya?.
Yace, “Hajiya wlhy wai wasune sukazo suke maganar nan gidansu ne�.
Cikin matuƙar razani ƙannen Ma'aruff da Mominsu sukace, “Gidansu kuma?!�.
“Wlhy kuwa hajiya, gasu nanma zasu shigo......�
Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu har mutanen suka ƙaraso, sai wani cika suke da batsewa.
Su dai su Momi sun zuba musu idanu kawai.
Ɗaya a cikinsu ne ya fara bayani ko gaisuwa babu balle lura da halin da Ma'aruff yake ciki baiyiba, “Hajiya mune waɗanda suka sayi gidannan, kuma hajiyar da suka sayar mana sun tabbatar mana kafin muzo kun tashi, amma kuma sai gashi mun iske saɓanin hakan�.
Baki buɗe duk suke kallonsu, cikin ƙannen Ma'aruff ɗaya ta samu baki faɗin, “Hajiya kuma? Wace hajiyace ta saida muku gidan bayan ga mai gidan nan shi baisan anyiba?�.
Kallon juna sukai suma, ɗaya yace, “Bamu gane mi kuke nufiba?, to mudai Hajiya mufida sunanta, kuma ita da Mahaifinta suka kawomu mukaga gidan sati uku da suka shige, tun a ranar muka biyasu rabin kuɗin, jiya kuma muka cikasa biyasu sauran suka bamu takardun gida yau ɗinnan da safe�.
Baya kawai momi tai ta yanke jiki ta faÉ—i a sume, nan take hayaniya ta kaure.
Ma'aruff ya amshi takardun daƙyar ya duba, tabbas takardun gidanne, to amma a garin yaya sukaje hannun su Mufida bayan yasan suna gidan momi?.
Bai samu amsaba saboda tashin hankalin da suke ciki, masu gida kuwa sallama sukai musu suka tafi akan sun basu nanda sati guda su kwashe komansu su basu gidansu suna bukata.
Babu wanda yabi ta kansu, dan suna a ruÉ—anin da baki bazai iya furtawaba sam.

★★★★�

An karɓi su Ma'aruff cikin gaggawa saboda asibitin su Adam sukaje, hankalin Adam yayi masifar tashi da ganin halin da Ma'aruff yake ciki, ya kwana biyu basu haɗuba saboda shima aiki yay masa yawa a tsakanin nan.
An samu damar ceto rayuwar mamansu Ma'aruff da hawan jini ya nema saka zuciyarta bugawa, yanayin da take na firgici yasa dole akai mata allurar barci danta samu hutu.
Ma'aruff kam gwaje-gwaje aka shiga masa, bayan bincike mai zurfi aka gano hantarsa tayi masifar kamuwa da ciwo harta harbi ƙodarsa, ba komaine ya jawo hakanba gareshi sai giyar da ya maida ruwa🤦🏻‍♀� .
Hankalin ƴan uwansa ya kuma tashi kololuwa, basusan yanda zasu fassara wannan tsakaninba a rayuwarsu, a daren jiya ƴan fashi sukai musu dirar mikiya a gida bisa jagirancin mahaifin Mufida da ƙiri da muzu babu kunyar ALLAH yazo musu a zahirinsa, bayan ya gama zayyane musu komai dangane da burinsa a kansu tare da zage momi tas sannan suka ƙwace komai, dukkanin takardun company ɗinsu da dukkanin na kaddarorinsu, ya kuma saka akai musu dukan tsiya, dukan da yay tunanin momi ta mutune suka fice suka barsu.
Sai dai da yake shi rai a hannun ALLAH yake ba wani shegeba, sai ALLAH yasa babu wanda yama samu wani mummunan rauni, sai dai sumar da sukai da kuma ciwuka da targaÉ—e ga wasunsu.
Da taimakon ma'aikatan gidan aka kaisu asibiti tun a daren, shinefa aketa kiran Ma'aruff bai amsaba, hankalin momi ya tashi ta matsa sai tazo ta ganshi duk da tana cikin halin rashin jin daÉ—in jiki, amma tana tsoron kar shima su Mufida sun masa wani mummunan abun, shinefa sukazo suka iske wannan musibar kuma ta saida gidan Ma'aruff din dasu Mufida sukayi da halin ciwo da yake a ciki.

*_MAI RABON SHAN DUKA, BAYAJIN ƘWAƁO SAI YA SHA_*

Dolene a kira ahalin Ma'aruff da wannan kalma, dan itace dai-dai da yanayin da suka tsinci kansu a ciki a halin yanzun kam.
Lokacin da duniya ke kai masa babu wanda ya isa faɗa masa giya nada illa ga ɗan adam, yasha faɗama Samina cewar kuɗinsane, jikinsane, sannan ra'ayinsane, sai gashi itama giyar kuwa da dukiyar sun tabbatar masa da su lokacine dasu, sannan shi komai a rayuwa da bawa yakeji dashi wata rana labarine, (watarana ma masu labarin baza'a samuba inji babana😭, haka yakansha faɗa mana cewar duniya labari, watarana masu labarin babusu😭😭🙏🏻, ya rabbi ka gafarta masa da dukkan waɗanda suka rigamu kwanta dama).
Momi dake ganin Samina bata dace da rayuwar É—antaba saboda É—iyar talakawace ita, shiyyasa ta aura masa É—iyar É—an uwanta wanda batasan shaho bane a gareta, ya daÉ—e cikin shawagin ganin ya É—auke dukkan wani jin daÉ—inta, ga samako nan ya biyo baya wanda ya dace da ita.
Duk tsiyar da Ma'aruff ke aikatawa ta shaye-shaye da lalata ƴaƴan jama'a sarai ta sani, kuma tanaji tana gani amma soyayyarsa ta rufe mata ido ta kasa ƙwaɓarsa saboda karta ɓata masa rai ko makamcin hakan.
Gashi yau babu dukiyar, babu lafiyar, babu komai da suke tunƙahon dashi ko taƙamar, komai ya ƙare, komai ya lalace tamkarma ba'a tarasuba.
Chapter 88 · 0% Book details