Sashe 85
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tana shirin barci suka shigo, ya kwantar da Abu-Talib dake a kafaɗarsa yana barici, Haysam kam ido ras, sai zuwa yay ya rungume ƙafafun Rumana yana fadin, “Ummie oyoyo�.
Juyowa tai tana murmushi, tace, “Babana kun dawo?�.
Tai maganar tana satar kallon Ahmad da ke ƙoƙarin shiga toilet fuska babu walwala..
Haysam kuwa na ƙoƙarin bata amsa, da labarin inda sukaje.
Sam hankalinta baya a kan yaron har Ahmad ya fito, yazo ya ja Haysam ya cire masa kayan jikinsa sannan ya É—aukesa zuwa bathroom, tana nan zaune suka fito yayi masa wanka, ita dai batace komaiba harya gama shiryashi ya tafi kaisa É—akin Zainab inda yake kwana yanzun.
Yaɗan jima kafin ya dawo, tasan yanacan yana lallaɓa Haysam yay barcine.
Ita kuma lokacin tanama Abu-Talib wankane yana kuka, ta kammala ta fito tai masa shirin barci shima ta bashi tea, ƙinsha ma yayi, data fahimci a ƙoshe yake saita ƙyalesa kawai ta kwantar dashi.
Alokacin ne Ahmad ya dawo ɗakin, nanma ɗindai bai kalli inda takeba, ita dai ta daure ta tambayesa ko akwai abinda yake buƙata?.
Sai cayay mata a'a.
Shiru kawai tai tana kallonsa, ya shiga bayi yayo wanka ya fito yay shirin barci, har lokacin idonta biyu kuma tana zaune.
Koda ya kammala shirinsa sai ya kwanta tamkar baisan tanayiba.
Zuwa can itama ta gaji da zaman da tunane-tunane ta matsa jikinsa ta kwanta tana gyara musu bargo.
Ahmad najinta amma sai baiyi ko motsiba, tai guntun murmushi kawai tana lumshe idanu, hannunta nakan ƙirjinsa tana yawo dashi.
Tace, â€Haba Zumana, minayi haka da zafi ake irin wannan fushin dani ne wai?â€?.
Shiru yay mata tamkar bai jiba, bata gajiba dai ta sake maimaitawa, nanma yay shiru, itako bata fasaba ta cigaba da neman harmutsa masa tunani.
Da Ahmad fa yaji yana neman hawa Network gashi yana fushi sai yay saurin riƙe mata hannu, “Miye haka wai Ruman? Ki barni barci nakeji�.
“Yaya ya za'ai na bari bayan kana fushi dani? Yanzu yayen da nayi shine laifi dan ALLAH?�.
A matuƙar fusace ya juyo gareta yana faɗin, “Okey bama abune mara ƙyauba kikayi? Yanzu ace Umm-Ruman ina cikin gidannan harki yayemin yaro ban saniba? Duka shekararsa nawa? Ɗaya fa da wata bakwai, saurin mikikeyi da bazaki barshi ya cika shekara biyunba? Okey ke yanzu kin girma ko? Duk abinda kikaji yuwuwarsa cikin rai baƙya buƙatar kowa a cikinsa, hakafa kika yaye Haysam ban saniba, nai miki shiru a lokacin shine yanzuma kika sake saboda kin gama rainani ga sa'anki ko......?�
Innalillahi kawai Rumana ke ambata, ganin yanda ya birkice da masifa tamkar ba shiba, akan ƙanƙanin abunda ita bata kallesa wani abun kirki ba.
Sai da ta bari ya gama sannan, ita dai batace uffanba, ranar ma kwanciya kowa ƙarshen gado yay barci, tasan ko haƙuri ta bashi sai dai ta sake tunzurashi yay sama, to garama tai shiru da bakinta yafi alkairi, idan ya huce daga baya ta bashi haƙuri.
Da safe kuma yay ficewarsa makaranta bayan yasan tana kicin tana ƙoƙarin haɗa musu karin kumallo.
Koda ta fito taga ya fita hakan ya mata bala'in ciwo a rai, har ƙwalla tayi, ita dai wannan saurin fushin na Ahmad bata sonshi sam wlhy, gashi da mitar fushi, idan yay zuciya takan jima bata shawo kansa sun dai-daitaba, danma dabarun da Iya ta bata tana ƙoƙarin aiki dasu, dan lokacin bikin su Fa'iza da suka ɗan daɗe a gida akwai randa Haysam ya faɗo daga kan gado yana barci, ita dai tasan a tsakkiyar gado ta kwantar dashi, yaronnan wajen mirgina-mirgina ya dawo gefe, daga ƙarshe ya faɗo ita kuma tana waje suna hira da iya, tofa sai faɗowar Haysam tai dai-dai da shigar Ahmad ɗakin, ya nufesa da gudu ya ɗaukesa, yaro yayta kuka, iya ta amshesa tana dudduba jikinsa sai ta fahimci yaji ciwone a hannu, ta kaisa wajen Malam ya duba sai ya tabbatar ciwo yaji, a take malam yay masa gyara saboda ya iya, aka sakamasa magani. To aiko wannan lamari ya zafi Ahmad, danshi a ganinsa laifin Rumana ne data kwantar da Haysam a bakin gadon saboda sakaci, haka ya zauna ya zazzaga mata masifa a ɗaki daga ƙarshe ya koma fushi, Rumana taci kukanta a ɗaki ta share hawaye, kwana biyu basa kula juna Iya na lure dasu, sai dai yanda basu faɗaba itama bata tankaba, sai aranar na ukune suna gab da komawa Porthercout Iya ta zaunar da Rumana tana koya mata dabarun zama da Ahmad ɗin. ta kuma tabbatar mata mafi yawan halayyar Ahmad ya samosune daga kakansu Malam Rabi'u mijinta, shiyyasa idan Ahmad ɗin na abu takan tuna ƙuruciyarsu da Malam sosai. Umm-Ruman taji daɗin wannan shawarwari na Iya, da sune kuma take samun damar fuskantar Ahmad ɗin a duk lokacin da yayisa.
Itama kasa cin komai tayi, sai Haysam da Zainab ne sukaci, shima Abu-Talib ta bashi nashi da yake iya ci sannan sukai shirin fita.
Kwana biyu yana haushi da ita, a na ukun kuma ta ƙara durƙusawa har ƙasa ta bashi haƙuri tana hawaye da amsar laifinta.
Sai da taita masa magiya kafin ya nuna ya haƙura tare da mata gargaɗi sosai akan karta sake.
A take ta rungumeshi, daga nan aka canja tasha zuwa wadda tafi ƙarfina🥱🤫.
“Dama ance faÉ—an masoya hutu😂⛹â€â™€â€?.
***********************
Rayuwa ta cigaba da shuɗawa su Rumana ana shekara ta Uku a makaranta, yayinda Ahmad yaketa ƙoƙari akan nasa karatun shima, dan haka sam baya wasa da damarsa.
A lokacin shima Abu-Talib an sakashi a makarantar su Haysam, hakama Subayya É—iyar Gaddafi, yanzu hakama Jiddahn ciki gareta tsoho itama.
Bayan shuÉ—awar wasu watanni Jiddah ta haihu namiji, su Rumana akasha hidima.
Itama babu jimawa sai ga wani cikin, nanma dai Ahmad yata murna tamkar ya goyata, inda itakam bataso cikinnan yanzuba kodan karatunsu da ya É—auki zafi yanzun, amma sai bata nunaba ta godema UBANGIJIN da ya bata, dan inharma Ahmad ya fuskanci hakan daga gareta lallai zasuyi uwarwatsine kawai..
Haka dai ta cigaba da rainon cikin nan, da sauƙi shi bai cika bata wahala ba, sai dai yawan son abu mai sanyi da takeyi.
Zainab ma ta cigaba da karatunta a sashen lafiya a wata makaranta dake Riyadh, dan haka acan take zaune gidan wani abokin Gaddafi balarabe ne shima da matarsa ɗaya da yaransu biyu, su ƴan asalin ƙasar Saudiyya ne, yanzu idan ka ganta wajen su Rumana weekend tazo ko hutu, weekend ɗinma hanata wani lokacin Ahmad yakeyi.
________________________________