← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 94

Sashe 19

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tana cin abincin da aka sakata dole tana satar kallonsa yanda yake shan magani kamar zaiyi kuka, sai yayi kamar zai sha sai ya fasa yana matse ido, idan kuma ya jefa a baki da ƙyar yake haɗiyewa kamar zaiyi amai.
Ba sabon abu bane a wajenta tunda tasan baya son magani, ya ɓata lokaci sosai kafin ya gama shan maganin da bai wuce kwayoyi shida ba.
Ficewa yay, mintuna kaɗan sai gashi ya shigo, botiki ya ɗauka ya fita tare da ƙaramin banbunsu.
Hakan yasa Rumana miƙewa itama ta shiga tattare kwankan da suka gama, ta ɗakko wani filet ɗin ta juye kazar jiya ta ɗora a tiren da zainab ta kawo abinci ta ajiyesu gefe.
Mamaki ya bata ganin yana ɗibar ruwa, da alama dai gugar ya fiddo dan ga ƙugiya nan a gefe ya ajiye.
Kwanikan ta ajiye gefe ta koma ɗakin, tana ƙoƙarin shiga ta tsinkayo muryarsa yana faɗin, “Ki kwashe kwanikan nan shima ki fiddosa�.
“To� kawai ta iya cemasa.
Yanzu ita ina zata saka waɗannan kwankan haka? Duk da basu da yawa ɗakin babu wani fili mai yawa daya rage, kuma dai bata ce zata jerasu a ƙasa ba ai.
Haka dai ta gama fiddasu ta É—auki banbun takai masa, sai da ta É—auraye shi sannan ta ajiye.
Ya É—auki wanda ya cika da ruwan ya kai É—akin, itako sai kallonsa take, dan banbun yanacin kusan boket huÉ—u.
Ruwan ta ɗiba a ƙaramar roba ta koma gefe tana wanke kwanikan, shi kuma ya ɗauki banbun data ajiye ya maidashi ƙofar ɗakinsu ya ajiye, idan ya cika botiki sai yaje ya juye.
Hakan da Rumana ta ganine ya sata miƙewa tabar wanke-wanken, idan ya cika botikin sai taje ta juye, a haka har suka cika banbun da botikan uku, biyu na roba ɗaya na ƙarfe.
Ƙarasa wanke-wanke tazo tanai, shikuma ya ɗauki ruwan botikin ƙarfen ya nufi bayi.
A lokacin kuma Maman Ama... Ta fito riƙe da Amatullah tana kuka.
Rumana tai murmushi tana kallonsu da faɗin, “A'a Amatullah yaya dai?�.
“Rigima kawai mara dalili, ɗan zoɓon dana rage na ƙasan botiki ta zubarmin a ɗaki, shine kuma bazan gogeba sai na bar mata tai wanka a ciki�.
Rumana tace, “Lallai hajiyar ɓarna kenan, ina Yayana shi? Ban ganshiba tunda na tashi?�.
“Wannan ai tun jiya bama ya gidan, da ƙanwata tazo jiya da yamma ya maƙale mata sai da ta tafi dashi�.
“ALLAH sarki, to ALLAH ya dawo dashi lafiya�.
Rumana ta faÉ—a tana kama Amatullah data rarrafo wajenta.
ÆŠaukarta tayi, ta zauna a bakin rijiyar tana mata wasa, ahaka Ahmad yazo ya wucesu.
Ƙin shiga ɗakin Amatullah tayi, har sai da ya leƙo, kamar ance ta ɗago sai suka haɗa ido, “Zonan� ya faɗa kawai yana sakin labulen.
Miƙewa tai ɗauke da Amatullah ta nufi ɗakin.
Tsaye ta iskeshi yana taje sumarsa a gaban mirror, tace, “Gani Yaya�.
Bai tankaba sai da ya gama, ya ajiye kum ɗin yana faɗin, “Bara naje can gida baba na kirana, naga babu abin girki ko?�.
Tai jimm saboda bata gane kan tambayarba.
Katse mata tunani yay da cewar, “Risho nake nufi ko abin gawayi�.
“Eh babu, amma inaga zasu kawo yau sukace�.
“Okey� kawai ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaura agogo a hannunsa, mikuma ya tuna sai taji ya ja siririn tsaki tare da kuncesa ya buɗe jakar daya ɗauki kaya ya jefashi ciki, ya zaro wani ya saka, kumatun Amatullah dake miƙa masa hannu tanason ya ɗauketa yaɗan shafa ya wucesu batare da yace komaiba.
Rumana tai ajiyar zuya bayan ya fice tana É—an girgiza kai, aranta tana tunanin ko yaya wannan zama nasu zai kasance kenan oho?.
Fitowa tai tsakar gida tanama Amatullah wasa, inda maman Ahmad ke É—an mata hira daga kicin É—insu tana girkin rana.
Ita dai Rumana murmushin ta yafi hirar yawa, dan dama can ita bamai yawan magana bace, ta kuma kula Mama Amatullah akwai surutu.
A haka su Fa'iza sukazo suka iskesu, sosai Rumana taji daÉ—in ganinsu.
Suka shiga ɗaki sai shaƙiyanci suke mata, harda tambayarta wai yaya jiyan? Dan sunga Yah Ahmad a gida yanata ƙyallin angwanci.
Duka takai musu, suka kauce suna dariya, haka sukaita tsokanarta, kazar kuwa da suka gani sai da ta ɗiba musu, suka kuwa ci suna faɗin, “Tunda ke tsoro ya hanaki kici muko ci mukayi, Rumana wai dan ALLAH da wuya kamar yanda ake faɗa?�.
Rumana ta kalli Salima mai maganar tana faɗin, “Minene?�.
Gado Salima ta nuna mata da yin magana ƙasa-ƙasa kamar mai munafunci.
Tashi Rumana tayi tsaye, “Oh ni ALLAH ya shiryeku, ni dai babu ruwana wlhy, kuje ku tambayo Yah Ahmad ɗin mana�.
“Kutumelecy amma baki da man kai Rumana yasin� cewar Fa'iza.
Salima tace, “A'a so take ya maidamu niƙaƙƙiyar gyada ta ƙuli-ƙuli alkur'an, kinga kuwa yanzu da muka haɗu dashi a gida sai wani cin magani yakeyi, niko a raina har gulmarsa nayi, nace waishi Yah Ahmad yamayi auren bazai canjaba ne?�.
Dariya Fa'iza da Rumana suka sanya, Salima ma mai maganar ta tayasu tana sake cewa “Wlhy na zata yau zan ganshi fuska a washe, Rumana ko dai baki bada kai bane?�.
“Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso�.
Fa'iza tai saurin faɗin, “Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda ƴaƴansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi�.
Cikin marairaice murya Rumana tace, “Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku ƙarasa, ni kam nasan ai nayi kenan�.
“Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki ƙarasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai�.
Hararta Umm-Rumana tayi.
Suka sanya mata dariya.
Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau.
Rumana tace, “ALLAH ya ƙyauta to, ALLAH ya shiryeta�.
Amin dai, su Fa'iza suka faÉ—a a tare.

Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima ƙanwar Rumana suka kawo abincin rana da ƴan tarkacen kwanika da aka ƙara saima Umm-Rumana, harda ƙaramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da ƙatuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa.
Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka ɓalle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin ɗakin amarya, harma da mata maƙwafta ƴan gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.

_________________________
Chapter 19 · 0% Book details