← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 94

Sashe 43

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Samina kuwa É—akinta ta shiga tunda dama ta sansa, ta faÉ—a kan gado tana fashewa da wani kuka mai ciwo, farawa da iyawa kenan, daga tarewarta Ma'aruff ya rasa dami zai tarbeta sai wannan rashin mutuncin?.
Kuka tasha bana wasaba, ga maganin matan da aka É—irka mata sai cizonta yake, har mararta ta fara mata ciwo.
Ganinfa zata halaka kanta kusan biyu na dare ta sake miƙewa ta koma ɗakin Ma'aruff.
Kwance ta iskesa hankalinsa kwance yana barci, cikin sanɗa ta haye gadon tare da ɗaga bargon ta shige cikin jikinsa ta ƙanƙamesa.
Cikin jan tsaki Ma'aruff daya farka yace, “K wane salon iskancine wai haka ina barci zakizo ki tadani?�.
Banza tai masa ta fara masa salon data san yana saurin ruftawa, da zafin nama ya tureta daga jikinsa.
“K banason rashin mutunci fa, mike damun tunaninkine?�.
Kuka mai tsuma zuciya Samina ta fashe masa dashi tana roƙonsa ya taimaketa karta mutu, sai faman riƙe mara take tana matse baki, ga hawaye wasu na bin wasu.
Shiko kallonta yakeyi da maÉ—aukakin mamaki, shi sai yau yake fahimtarma abinda mahaifiyarsa ke faÉ—a masa akan rashin dacewarsa da wannan yarinyar......
Katse tunaninsa Samina data manne masa a jiki tayi, ya janye jikinsa yana hararta, “Wlhy ki kama kanki, ni na aikeki kisha abinda zai hanaki zaman lafiyar? Can kije kiji da matsalarki ni dai barci nakeji, dan haka tashi kibarmin ɗaki kokuma na fitar dake wlhy�.
Sabon kuka Samina ta fashe dashi tana durƙusawa a gabansa tana roƙonsa, amma sam yaƙi saurarenta saima faɗi yake ta fitar masa a ɗaki, inba hakaba wlhy zai lakaɗa mata duka, abinda take son shi baida ra'ayinsa yanzun.

DAREN FARKO ya zama DAREN WAHALA, Inji amarya Samina dake neman shiɗewa saboda azabar ziwon da mararta take mata, ruwan sanyi kam harta gaji da sheƙa ma jikinta ta sadaƙar mutuwa zatayi kawai kafin wayewar gari, tayi nadamar biyema su mama gaje da suka dinga ɗirka mata magunguna duk dan ta burge Ma'aruff, kuka kam tayi harma ta rasa hawayen zubarwa, Ahmad ya faɗo mata a rai, yanda yay wani irin murjewa ga wani sheƙi da choco fatarsa keyi, kawai saita shiga kawosa cikin ranta a wani irin yanayin daya sakata kuma fashewa da kuka, dan kuwa tana ƙiyastashi a rantane zuciyarta na hasko mata Ahmad tare da Umm-Ruman.
Jitai tamkar numfashinta zai bar gangar jikinta lokacin da hakan yazo mata a cikin rai.

___________________________________

Ahmad ma kam baisan tanaiba, dan tun sanda ake dambarwar abokan ango sunce bazasu É—auki tsoffi a motaba ya shigo gidan ya kaÉ—a kan matarsa suka É—auki hanyar gida.
Tana sashensu sunashan hira da Amminta da ƙannen Ammi da sukazo bikin Zainab taje ta sanar mata saƙon kira daga Ahmad akan tazo su wuce gida.
Sam bataso wannan tafiya ba, dama ga tsoro a ranta na abinda ya faru a daren shekaran jiya, Ammi tai mata tsawa ganin taƙi ko motsi balle shirin tafiyar.
Tashi tai tana matsar hawaye ta kimtsa ta fito, a sashensu ta iskesa suna faɗan da suka saba shi da Sakina, tun suna ƙanana idan tace masa ƙaninta sai ya ɓata rai saboda bayaso, to har yanzu da take a gidan aure ga ƴaƴa ba dainawa sukaiba, dan ko gidanta yaje sai sunyi.
Ta girmesan amma tsiran bawani baneba, shiyyasa hakan ke bashi haushi.
Su Yaya Maryam nata musu dariya Rumana ta shigo, ya zubama kan Sakina ranƙwashi yay saurin nufar hanyar ƙofar gida yana faɗin Rumana ta samesa a waje.
Sosai yanzu kowa ke musu dariya har Ayyah da Gwaggo, dan kuwa Sakina taji zafin ranƙwashin nan sosai.
Ya tsaya mana inba tsoroba, kuma zata kamashi saita rama.
Ita kanta Rumana abun nasu ya matuƙar bata dariya, dan haka tabisa da kallo tana murmushi.
Sallama taima su Ayyah dasu Yaya Maryam ɗin ta fita, lokacin anata hayaniya a ƙofar gida da abokan ango, dube-duben inda zataga Ahmad takeyi, duk da kuwa ƙofar gidan akwai hasken wutar nefa da aka kawo.
Jin an kama hannunta tai saurin juyowa, ganin Yah Ahmad ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali, baice mata komaiba yaja hannunta suka bar wajen.

★★★★

Duk da Ahmad ya lura da fushin da takeyi sai ya shareta kamar bai fahimci abinda take jima haushin ba, lokacin da suka shigo gidan shiru dan kowa ya shige ɗaki ya kwanta, Ahmad ya buɗe musu ƙofa suka shiga.
Kayan jikinsa ya rage itako Rumana ta samu waje ta zauna tanata kumbura fuska.
Baibi takanta ba ya haÉ—a ruwan wanka ya tafi yowa, har ya dawo É—akin tana a inda ya barta, murmushi yayi kaÉ—an yana girgiza kai, yasa tawul ya goge ruwan jikinsa ya shiga shirin barci.
Sai lokacin itama ta miƙe ta ɗeba ruwan ta fita, da kallo kawai ya bita amma uffan bai ce ba.
Itama dai wankan tayo, lokacin data shigo harya kwanta, sai dai ba barci yakeba waya yakeyi, Rumana ta kalli agogon ɗakin sannan ta kallesa, duk da bataji da wa yake wayarba hakan ya bata haushi, tako sake tsuƙe fuska waje guda.
Duk abinda take Ahmad na lure da ita, ta kammala mutsu-mustun shirinta tazo gefen gadon nesa dashi ta kwanta a takure.
Dai-dai nan ya ajiye wayar shima, matsowa yay tsakkiyar gadon ya jawota ta dawo jikinsa.
Hancinsa saman dokin wuyanta yana hura mata iska yace, “Kodai mu koma ne kima amaryar zaman ɗaki?�.
Tasan baƙa ya faɗa mata, dan haka tai shiru, murya a shaƙe ya sake faɗin, “Dake fa nake magana�.
“A'a� ta faɗa tana ƙanƙame jikinta saboda abinda yake mata da hannunsa a cikin jiki.
Bai sake magana ba sai sabon salo daya canjama kwanciyar tasu.

“Yau ɗinma dai babu sauƙi� cewar Umm-Rumana a zuciya tana share hawaye bayan ta gama gurzuwa a hannun jaruman mazaje.
Da taimakon Ahmad yau ɗinma ta kimtsa jikinta tanata masa kuka, da yake kukan da biyune harda haushin ƙin barinta ta kwana gida sai na yau ya nema finma na shekaran jiyan, shi dai Ahmad idanuma ya zuba mata, sai dai a ƙasan ransa yanajin tausayinta dan shi kansa yasan shiɗin bana wasan yara bane, tunda yana a ganiyar ƙuruciyarsa ne, kuma yanzunma aka fara wasan🤭.
Yanata lallashinta ta sigar shafa mata baya har barci ya kwashesu a haka su dukansu.

★★�

Washe gari Ahmad na gida har azahar bai fita ko inaba, hakanne ya saka Rumana fahimtar itama dai bazataje ko inanba kenan.
Bataga fuskar tambayaba kuma dan haka tai shiru da bakinta sai haushi dake cinta a zuciya.
Bayan anyi sallar azhar ɗinne Zainab da Ni'ima ƙanwarta sukazo, taɗanji daɗi, dan kayayyakin bikine wanda Ayyah ta haɗo tace a kawo mata, a wajensu takejin ai suma su Yaya Maryam duk sun tafi gidajensu ma, gidanma sai iya dangin mama gaje ne kawai da suke shirin zuwa buɗar kai gidan Samina.

_________________________________

Ko wacce amarya tana saka daren farkonta a jerin tarihin daren tunawarta koda takai tsufa saboda muhimmancinsa a gareta, sa ɓanin Samina daya zame mata daren baƙin ciki da wahaltuwar ciwo, da safe tashi tai tamkar wadda aka tsamo daga bakin kura, tayi wujiga-wujiga cikin azabar ciwo, ga kukan wahala datasha idanu sunyi luhu-luhu.
Har lemon tsami sai da ta samo daƙyar a kicin ɗinsu tasha amma bataji yanda takeso ba, sai da taɗan samu kanta kaɗan harta sami damar gyara jikinta tai wanka, bataga ko ƙeyar ma'aruff ba a gidan kuma bataji motsinsa ba sam, gashi koɗan abincin da akan kawo daga gidan surukai washe garin kai amarya ita babu wanda ya kawo matashi.
Ƴar kazar amarcin da ango yake kawowa nanma bata sameta ba a daren jiya.
Komai ya dagule mata ta kowanne fanni, har zuhur bataga kowa ya leƙotaba ga yunwa ga damuwa ga ciwon mara, falo ta dawo ta kwanta cikin kujera tana hawaye, a lokacinne taji ana ƙwanƙwasa ƙofa.
Tashi tai bayan ta ciri tissue dake saman center table É—in falon ta goge hawayenta taje ta buÉ—e, Æ´an uwan mahaifiyartane da sukazo buÉ—ar kai.
Matsa musu tai suka shigo tana musu sannu da zuwa, su dai sai binta suke da kallo.
Duk da sunsha mamakin ganinta ita kaɗai a gidan sai basuce komaiba, yanda akasan amarya da farin jini sun zata kodai dangin mijinta sa iske wasu a ciki, duk da dai sun kula ƴan gayune kowa rayuwarsa yake babu ruwansa data wani, kuma yanda mijin nata yake firi-firi babu alamar kunya a idonsa ma ya hana kowa raɓarsu.
Yanayin da suka ganta wujiga-wujiga basu kawoma kansu tana cikin damuwa baneba, ca suke kawai dai angone ya mori amarcinsa musamman lura da yanda take tafiya da sukayi, ita kuma ciwon marane ya sakata tafiya a dudduƙe😣🤭.
Bata iya faÉ—ama kowa halin da take cikiba har suka gama hidimarsu bayan la'asar sukai shirin tafiya, a lokacin kuma motar ma'aruff ta shigo cikin gidan.
Ya fito daga mota sai wani tsume fuska yake tamkar baiga waÉ—anda suke a gidanba, kamarma zai wuce bazai gaidasu ba sai kuma dai miya gani oho masa, ya tsaya ya gaishesu cikin rashin girmamawa ya wuce abinsa.
Wannan abu kuwa ya saka kowa a cikinsu yaye baki suna binsa da kallo harya shige, ita kanta Samina abin ya sosa mata rai.
Su dai duk sun tafi zuciya a saɓule, yayinda wasu suka gumtsi abin faɗa da yaɗawa kuwa.
Chapter 43 · 0% Book details