← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 94

Sashe 71

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ɓangaren Samina sam abubuwa babu sauƙi, komai sake rikice mata yakeyi, dan yanzu idan har kikaga Ma'aruff a sashenta to tabbas Mufida bata gida ne kokuma sunyi faɗa, ko yazo mata a buge ta korosa, dan tace bazai taɓa zama mata a sashe yan warin giya ba, bai dametaba yaje yay ta sha shiya sani, amma babu maganar raɓarta.
Tofa shine sai kiga ya taho wajen wadda ya raina Samina, ita kuma da bakinta bai iya mutuwa saboda azabar tsiwa da yace kule zatace cas, kafin kace mi sunyi sama, yako bubbugeta babu abinda yasha kansa.
Ya saka mai gadi ya hana kowa zuwa wajenta saboda zugar Mufida, ashe lokacin bikima shine yasa aka hana ƙawayenta shigowa gidan, sai da ta kira Nafy tana mata tsogumi shine ta sanar da ita komai daya faru, ran Samina ya ɓaci suka haura sama da Ma'aruff, ranarma sunci uban faɗa a gidan Mufida nata kwasar dariya.

Dolene duk wanda yasan Samina ya ganta a tsakanin nan ya tausaya mata, tayi figi-figi da ita kamar wadda aka ƙwato daga bakin kura, gashi saboda man bilicin ɗin data daina shafawa saboda ƙarewar nata ƙuraje sun mata futu-futu da fuska, nan yayi baƙi nan yayi ja, fuskar tai wata iri kamar wadda ta tashi daga jiyyar ƙuna.
Duk ɓarin kuɗin da yake mata da yanzu ya daina, sai abinda mufida tace akeyi a gidan.
Da kuka na maganin damuwa da tuni Samina yayi mata, sunan Ahmad kuwa ai babu fashi a rana saita ambata sama da sau goma, abu kaÉ—an Ma'aruff yay mata saitace da Yaa Ahmad ne da ba hakaba.
Ga rashin mutuncin dangi miji, sosai surukarta ke nuna fifiko tsakaninta da Mufida.

__________________________________

A randa Ahmad yazo a ranar yayma iyayensa tuni akan maganar abinda ya kawosa nason tafiya da iyalansa, dan yace kwana uku zaiyi kacal ma su juya.
Babu wanda yay musu a cikinsu, tunda dama kowa yasan da zancen, dan haka shiri kawai suka somayi.
Sai kuma Rumana duk ta shiga damuwa, ta roƙesa dan ALLAH su tafi da Zainab tunda ta gama firamare ɗinta, idan sukaje can sai a sata sakandire.
Da farko dai yay shiru kamar bazai amince ba, amma da yaga tana kuka sai yace zai tun tuɓi su baba idan sun amince, idan sunce a'a tofa sai dai tayi haƙuri, tunda da dai ga Haysam nan ya ishe ɗauke kewa.
Ita dai tata addu'ar ALLAH yasa a dace, da dare ya samu baba da maganar bayan ya fara sanarma Ayyah dama.
Baba yaso tirjewa, hakama gwaggo, amma da Ayyah ta saka baki sai suka amince, koda suka sanarma malam da iya fatan alkairi sukayi, iya tace dama tanada niyyar magana akan abama su Rumana wata a yaran gidan.
Ana gobe zasu tafi Rumana taje can gidansu, su mama Ama na soro zaune suna hira da makwafta, mamakin ganinta ya kamasu, dan a zatonsu kota dawone, har wata maman Salim na faɗin, “Maman Haysam masu jego na dawowar dare ke ta rana kike?�
Murmushi tayi amma bata bata amsaba sai da ta zauna, suka amshi Haysam dake bayan ƙanwarta khadija suna yaba ƙyawun da yaron ya ƙara.
Sai da ta gaisa da kowa kafin tace, “Ba dawowa naiba, munzo muku sallamane dan da sassafe zamu wuce�.
Cikin mamaki duk suk kalleta, maman Ama ta ɗora da tambayar “Yo ina kuma zakuje amarya?�.
Kafin Rumana ta bada amsa khadija ta amshe da faɗin, “Porthercout zasu tafi ita da yayanmu�.
Kallon kallo aka koma. Kausar tace, “Yawon shaƙatawa za'a kenan Amarya?�.
Nanma Khadija dai ta bata amsa da faɗin, “A'a zasu koma can dai da zama sai dai suzo mana yawo�.
Tsitt soron yayi, sai maman Aysha ce cikin yaƙe ta katse shirun, “A to lallai su marya gara wasai, kice guduwa za'ai kudu a barmu, su Haysam ashe ƴan kudanci za'a koma�.
A yanda take maganar kawai ya isa tabbatarma da mutum bada daÉ—in rai takeyiba.
Su kuma sauran sai famar yaƙe sukeyi, ita dai Rumana miƙewa tai ta nufi ɗakinta, shigarta babu jimawa sai ga Ahmad shima ya shigo.
Ya wuto su maman Ama Haysam na wajensu.

Rumana ta amsa masa sallama tana cigaba da abinda takeyi, shima amsawa yay yana zama a bakin gadon idonsa a kanta, daure zuciyarsa kawai yake harsu tafi ba tare daya nema ruwan dazai kashe ƙishinsa daga gareta ba.
Itama ta lura da hakan, shiyyasa taketa addu'a da fatan harsu wuce kar yace yana buƙatarta, dan ita dai bazata sake maimaita abin kunyar da sukai a ranar da naƙudar Haysam ta dole tazo mataba.
Tana kimtse-kimtsenta yana binta da kallo, hakan yasa ta ƙwalama khadija kira, sarai Ahmad ya fahimci dalilin kiran khadijan, hakan yasa ya cije baki a ransa yana faɗin duk wayon amarya dai sai ansha manta, kuma zaki gane baki da wayo yarinya.
Ita dai batasan yanaiba, ta gama komai yanda ya dace dan yace dagasu sai kayan sawa zasu tafi, sai É—an abinda ba'a rasaba da Rumana ta É—auka.
Gab da magriba suka bar gidan tana jaddadama su Kausar kalmar a yafi juna.
A fili dai sunce suma a yafe, amma ƙasan zukatansu tamkar zasu kama da wuta haka sukeji, sunajin baƙar hassada akan wannan tafiya ta Umm-Rumana, ita kanta ta fahimci yaƙe kawai suke mata da dariyar gatsatsa wadda tafi kuka ciwo. Duk da ita sai takejin wani iri babu daɗi saboda sabo............✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻a: *_41_*

.............Washe gari suna idar da sallar asuba motarsu ta tashi, Rumana sai share hawaye takeyi, Zainab kam ko a kwalar rigarta murna taketayi, su kaɗaine a motar dan shata Ahmad ya ɗauka duk da kuɗin daya kashe hakan yafi musu sauƙi, dagasu sai kayansu, direba da Ahmad a gaba, zainab da Rumana da Haysam a baya.
Kuka sosai Rumana takeyi haka Æ´an uwanta, duk dauriyar Ammi sai da tayi hawaye itama, tunda motar ta wuce gidan sai ya koma tsit, kowa yanajin kewarsu a ransa, dan Ahmad ya zama wani jigo abin alfaharinsu.
Mama gaje kuwa babu abinda kecin ranta sai baƙin ciki, ko fitowa ba taiba lokacin da kowa ya fito ƙofar gida har iya domin ganin tafiyarsu.
Babu wanda ya damu da lamarinta, sukabi yaransu da addu'ar fatan alkairi sudai.

Sunyi tafiya mai nisa Rumana tana kuka, yayinda Zainab barci yay gaba da ita, dama Haysam tunda suka taho shi barcinsa yakeyi.
Ahmad da direba ma ba wata hira sukeba, saboda hankalin Ahmad naga Rumana, itama dai barcinne ya saceta.
Ajiyar zuciya a Ahmad yayi kaɗan, yana maijin tausayinta na tsigota da yay daga cikin dangi, bashi da wata mafita bayan wannan, duk da kasancewarsa ƙaramin ma'aikaci yanada ƙyau ya maida hankalinsa ga aikinsa tuƙuru, gashi karatu yakeson komawa, zai sake zama busy sosai, kuma koba komai yana buƙatar jinta a kusa dashi, itama karatun ya keso ta koma kafin yara su fara mata nauyi.
Chapter 71 · 0% Book details