← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 94

Sashe 65

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin awa biyu Gwaggo da Ayyah suka kammala kimtsa komai, sannan kusan sha É—aya na dare, Ayya ce taje cikin dubara ta sanar ma Ammi dan ba'ason faÉ—in haihuwar sai safiya idan ALLAH ya kaimu.
Addu'a kawai Ammi tayi amma bata zoba.
Ayyah ta kama hannun Ahmad suka shiga ɗakin ya tsaya daga ƙofar ɗaki, jaririn dake nannaɗe cikin zani ta ɗakko masa, dukda da akwai ɗan ƙarni-ƙarni jikinsa, dan zaitun kawai aka shafa masa hakan bai hana Ahmad amsarshiba jikinsa sai tsuma yake, lokacin da idonsa ya sauka akan yaron kuwa sai suka ciko da ƙwalla, ya ɗora bakinsa akan goshin yaron ya sumbata yana murmushi.
Ayyah ma dake murmushi tana kallonsa tace, “Ɗan albarka nayi miji gashi nan tubar kalla masha ALLAH�.
Murmushi yayma Ayyah sai dai bai iya cewa komaiba, jiyake kamar ya maida yaron cikin jikinsa, ya kai dubansa ga Rumana dake kwance a kan gado ta juya musu baya wani wahalallen barci yay awon gaba da ita, Iya ko data sake kimtse-kimtse, dan so take ta É—aurayema yaron jiki ko yayane, Rumana dai anÉ—an gargasa matane kafin safiya.
Murya a sanyaye yace, “Ayyah Gwal ɗin fa?�.
Ayyah tace, “Wane kuma Gwal ɗan albarka?�.
Fahimtar suɓutar bakin da yayne ya sakashi miƙa mata yaron ya fita da sauri yana dariya.
Iya da duk take saurarensu tace, “Ɗan jakar uba, a gaban uwar takama Gwal zaka ce? Ashe bamu kaɗai akema rashin kunyar ba, ni dana gama wahalar amsar maka haihuwar wannan raguwar matar taka baka fara tambayata ba sai ita�.
Shi dai bai bata amsaba yama fice daga gidan cikin tsagwaron farin ciki da yarasa a ina zaije ya juyesa ko zaiji sassauci.

Ayyah da sai lokacin ta fahimci inda zancensa ya dosa itama tai dariya tana girgiza kai.
Sai da Iya ta kammala komai tsaf ta fice sanan Ayyah taje har É—aki ta kamo Gwaggo dan dole tazo taga baby.
Lokacin kusan sha biyu ma.
Gwaggo ta É—aukesa tai masa addu'a tana mai kallonsa tamkar sanda ta haifi Ahmad, Rumana dai tanata barcinta batasan wainar da ake toyawa ba.
Gwaggo na fita su fa'iza suka shigo, sai santin É—an yaron suke, sukam, ai sai da Gwaggo ta korasu suje su kwanta sannan.

Ahmad ma da wannan tsagwaron farin ciki ya isa gida, har zai kwanta ya tuna akwai najasa a jikinsa, dole yaje yay wanka tare da ɗauro alwala, saima ya kasa kwanciyar kuma ya hau nafilfilin miƙama UBANGIJI godiya.
A wannan dare haka wannan ahali suka kwana cikin tsagwaron farin ciki mara misaltuwa.

★★★★★★

Asubar fari Ayyah ta fito baba ya taimaka mata suka haɗa wutar ɗora ruwan wanka, lokacin da ake ƙoƙarin shiga massalaci ai harya tafaso cikin amincin UBANGIJI.
Iya na idar da salla nan tayo, ita taima Rumana cikakken wanka mai gamsar da jikin duk wata maijego data samesa, Ayyah kuma taima jinjiri, Fa'iza ta kimtsa ɗakin Ayyah aka kunna turaren wuta ɗaki ya ɗauki ƙamshin jego.
An naɗe yaro a kayan sanyin da aka sakama Ahmad lokacin yana jinjiri shima ruwan ganye da ratsin fari, (kunsan mutan da akwai ɓoyo da bama abu muhimmanci, dama Ayyah tai alƙawarin inhar ALLAH ya kaita da rai, duk randa Ahmad yay aure ya haihu kayan da za'a fara sakama ɗansa ko ƴarsa kenan) to gashi ALLAH ya cika mata burinta kuwa, da yake kuma kayan saƙace mai inganci da tsari.
Shiko sai barcinsa yake yaji É—umi.
Kafin gari ya gama haske har gwaggo ta kammala damun kunu da yaji kayan ƙamshi, ga kuma shayi shima yaji kayan ƙamshin.
Mudan ya shigo gaishesu yay gamo da wannan farin ciki, dan shi bai shigo gidanba a jiya yanata dinkin wasu anguna kusan ma kwana yay, da yake kuma ba wani É—aga murya sukeba sai baisan mi ake cikiba, ko fitar Yah Ahmad bai ganiba, ya daiga shigowarsa bayan sallar isha'i.
Gaba ɗaya farinciki ya gama rufesa, ya ƙwaƙume jinjiri tamkar zai maidasa ciki, koda baba ya shigo a lokacin dan shima sai yanzune zai gansa da ƙyar Mudan ya bashi, ita dai Rumana kanta na a ƙasa ko Mudan ɗin ta kasa amsawa santinsa balle kuma ga baba ya shigo.
Ta dai gaidashi, ya tambayeta yaya jikinta? Ta amsa da ƙyar.
Jariri daketa barci yaji daÉ—in wanka yasha addu'oi wajen baba, Mudan ko ya fice nemi kayan shayi da Ayyah ta faÉ—a masa.
Babu daɗewa ya dawo harda soyayyen ƙwai.
Sai a lokacin kuma Iya ta dage ta callara ghuÉ—a domin tabbatarma kowa dai anyi haihuwa.
Ba ƙaramin faɗuwar gaba wannan ghuɗa ta saka mama gaje ba, itace farkon isowa sashen su Ahmad kafin sauran matan gidan.
Sai dai yanda suka iske mai jego tsaf ya tabbar musu da haihuwar bata yanzu bace, nanfa aka shiga taya juna murna da tsokanar jariri kasancewarsa jika a wajensu.
Mama gaje dai ta ciki na ciki, dan duk a rikice tace tana ƙoƙarin danne wane kawai.
Gida dai ya kacame da murna, duk da farar safiyar nan yaran gidan haka sukaita rige-rigen bin gidajen yayunsu dan sukai musu labari.

Sanda Ahmad ya iso gidan kuwa, duk yanda yaso shiga ɗakin Ayyah su gaisa da Rumana hakan gagararsa yay, dole ya haƙura bayan yaɗan gaggaisa da matan gidan sukai masa barka da addu'a wa jariri dole ya haƙura ya koma ƙofar gida wajen abokansa da suma suka kacame masa da murna, bakinsa ya kasa rufuwa kuwa sai murmushi yake saki.

Mama gaje kam ɗaki ta koma tamkar wata zararriya, sai ƙoƙarin kiran Number Samina take yaƙi tafiya, sai tsaki take tana faman zagaye ɗakinta da waya a hannu, wani irin zafi na azalzalar zuciyarta🥴...........✍�

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_

_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*

2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*

_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_37_*

*_MATAR AUDU😜🥱_*

.........Lokacin da mama gaje ke a wannan ruÉ—ani na neman number Samina ido rufe tana can suna tafka bala'i da Ma'aruff.
Dan gaba É—aya a kwanakin nan dama sai a hankula, asirin da ke a jikinsa ya bar jikinsa, hakan yasa sam Samina ta kasa gane kansa a wannan lokutan.
A daren jiya kuma bayan sun gama rigima akan fitar da zaiyi ta dare ta tareshi akan baizai fitaba ya shashsheƙa mata maruka ya fice abinsa, zama tai taci kukanta gwargwadon iko ta haƙura dan kanta, sai kusan ƙarfe ɗaya ya dawo gidan, tana ɗakinta ta kasa barci har lokacin, amma sai bata fitoba dan duk zatonta shi kaɗaine yauma ya dawo a bigensa kamar yanda ya saba.
Sai dai bata saniba tare yake da karuwarsa, kuma sabuwar ƙawarta Basira, wadda suke kira (Basy), suka shige ɗakinsa kuma suka kulle kansu, ranar a nan Basy ta kwana.
Chapter 65 · 0% Book details