← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 94

Sashe 17

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama-sama Ahmad ke jin Sufyan harya fice, daga bayama barci mai ƙarfi yay awon gaba dashi.
Har lokacin Rumana na tsaye tana hawaye, sai da taji tsayuwar ta gundireta ne ta ajiye ledojin hannunta ta nufi ƙofar ta rufe addu'a ɗauke da bakinta kamar yanda mahaifiyarta ta koyar da ita.
Zama tayi kawai ta zuba masa ido tsawon lokaci, tausayinsa na sake ratsa zuciyarta.
Itama kantane ke mata azabar ciwo, dan haka ta lallaɓa taja bargon dake saman gadon ta lullubama Ahmad data lura yana rawar ɗari, tana sakawa kuwa taga yajashi har saman kansa ya sake kudundunewa da ƙyau, ajiyar zuciya ta sauke tausayinsa na sake kamata.
Tsawon lokaci tana wajen har ta farajin saukar numfashinsa ya canja alamar barcinsa yay nisa sosai.
Tasan dolene a tausayama Yah Ahmad, dan halin da yake ciki abin dubawane, akwai tashin hankali abinda ka girma dashi a zuciyarka yazama shine sanadin rusa dukkan farin cikinka a dare guda.
Sabuwar tabarmar dake a ɗakin ta dauka ta shinfiɗa ƙasan ledar da aka saka a ɗakin ta kwanta ba tareda ta saka koda zaniba, sai filo data ɗauka kawai a gado saboda bata iya kwanciya babu shi.
Gyalen jikinta ta rufa dashi dukda bashi da wani kauri sosai.
A haka taci gaba da kukanta har itama barcin yay nasarar saceta, ga kanta yana sara mata sosai da ciwo.

_______________________________

A wannan darenma Samina da Ma'aruff sunsha hirarsu ta masoya, inda mafi yawan firar duk ta karkata wajen tsara yanda shagalin bikinsu zai kasance.
Daɗi tamkar zai narkar da ita, sai wani lumshe ido take tana dafe ƙirji da washe haƙora, har yanda take buƙatar lefenta ya kasance da kalar akwatunan da takeso da kayan gidan dazai zuba mata duk sai da ya tambayeta, sai events na garari na nunawa a gidajen tv da social media shima duksun tsara abinsu.
Cikin shagwaɓa take shaida masa yafayi ta turo manyansa, dan ita yanzu dukta tsani komai na gidansu, sotake ta kara gaba tabarsa kodan ƴan bani na iya.
Daga can Ma'aruff yay murmushi yana faɗin, “Karki damu gimbiyar mata, ni kaina na kagara na jiki a jikina lafe, ina baki gangariyar soyayya da babu sirkin ruwa a cikinta, burina kawai mallakarki tunda kinki bani damar hakan tun a yanzu, kince sai munyi aure, niko nayi biyayya na haƙura har a ɗaura a kawomin ke babie�.
“Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi haƙuri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan kaɗan daga aikinsa ya kwata cikin ƙarfi, niko kai kaɗai nake burin cikama alƙawarin kawo maka budurcina har gida�.
“Nagode ta wajena, shiyyasa nake ƙara jin sonki na ƙaruwa a raina a kowacce daƙiƙa, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a ƙirjina�.
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina É—in.
“Sai da Safe�
Samina ta faÉ—a a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da “Uhmm� kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.

Haka Samina tai barci da É—unbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shuÉ—e Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta taɓe tana jan tsaki, sai kuma ɗayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka ɗebe iyayensa, dan ko ƴan uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa ƙullin yaɗon wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............✍�

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*a: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(11)*

............Kiran sallar farko Ahmad ya farka, zazzaɓin ya sauka masa, sai dai akwai ciwon kai kaɗan-kaɗan, sai nauyin jiki da yakeji.
Ƙamshin sabon fenti dana katako ne ya tuna masa da inda yake, ya janye bargon da yake a ciki a hankali yana yunƙurawa ya tashi zaune, babu haske a ɗakin, dan Rumana ta saba idan zasu kwanta sai Ammi tace su kashe fitila, shiyyasa jiya da zata kwanta bayan ta gama shan kukanta sai ta kashe ta ajiye kusa da ita, a tunaninta ai zata riga Ahmad tashi da asuba.
Ahmad ya ɗan laluba ko zaiji wayarsa a jikinsa, sai dai babu, ya tura hannunsa ƙasan filon da ya tashi nanma babu.
Iska ya huro ƙaɗan a bakinsa yana janye bargon baki ɗaya, da lalube ƙafarsa takai ga bakin gadon, ya zurasu gaba ɗaya yana ambaton ALLAH a kan laɓɓansa.
Da sauri yay ƙoƙarin janyewa saboda jin ya ɗora akan mutum, sai dai nan ɗinma sake ɗorasu yay akan jikin nata.
Zafin da Rumana taji a ƙirjinta ne ya sakata farkawa tana faɗin “wayyo ALLAH Kadija zaki kasheni, bakicewa na haska miki fitila, ji yanda kike takani a ƙirji..�
Yanda tai maganar cikin yanayin barci da sanyin murya irin ta wanda yaji zafi sai da tsigar jikin Ahmad ta tashi, bai kawo a ransa tana wajen kwance ba, duk da ma dai zai iya cewa ya manta da ita a É—ikin.
Yana ƙoƙarin janye ƙafafun nasa Rumana ta kunna fitila ɗakin ya gauraye da haske.
Ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba ganin Ahmad zaune, sam ta manta inda takema ita, tai saurin jan gyalenta ta rufe jikinta saboda da daddare takura mata rigarta tayi shine ta zuge zif ɗin ya koma ƙasa sosai.
Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, ya sake ziro ƙafafunsa ƙasan batare da yace mata komaiba.
Itama dai ko motsi bata sakeba harya ɗauki buta ɗaya cikin guda biyu da aka zubama ruwa aka ajiye farkon ƙofar ɗakin.
Hannu yasa ya zare sakatar ɗakin da ta saka ya fice, yanda iskar asuba ke kaɗawa a hankali ce ta sakashi buɗe hanci ya zuƙa sosai sannan ya fesota ta baki yana lumshe idanu.

Rumana dai kasa motsawa tai, sai kalmomin data faɗane ke mata kaikawo a rai, takai hannu saman ƙirjinta daya taka kunya na sake kamata, dukda ba nauyi ya sakiba taji zafi, kuma tana ɗanji har yanzu kaɗan, maida zif ɗinta tayi ta miƙe jiki duk babu ƙwari, ta ɗauke filon data kwanta tare da naɗe tabarmar.
Yanda fitilar tasu taɗan hasko waje tana hangenshi yana alwala a ƙofar ɗakin, da yake gidan bawani girmane da shiba, babu wani isashshen tsakar gida sam....
Ya katse mata tunani yayinda yake É—aga labulen ya ajiye butar, kamar zai tafi sai kuma ya dawo da baya ya shigo É—akin.
Ta gabanta yabi zuwa gaban gadon, ya É—aga filo yana sake duba wayarsa, ganindai babu ita saiya maida kallonsa ga Rumana dake tsaye jikin Wadrobe kanta a sunkuye tana kallonsa gefen ido.
“Sufyan bai bada wata bane?�.
Da farko bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka taɗan ɗago ido ta kalleshi, ganin ya tsareta da idanu tai saurin janye nata, cikin in ina tace, “A'a, ƙila ya manta ne�.
Baice komaiba yazo ya sake raɓata ya fice.
Tana jiyoshi ya buÉ—e gida ya fita, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya itama ta É—auki fitila ta fita duk da tana É—anjin tsoro.
Tana cikin alwala mijin ɗayar matar gidan ya fito, ganinsa da ga shi sai gajeren wando yasa Rumana saurin duƙawa tana wanke ƙafa, bata ce masa komaiba shima baice mata ba ya shige bayi, itama tai saurin faɗawa ɗaki.

★★★★�

Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ƙofar gidan yake, Rumana na zaune saman abin salla tana azkar.
Yanda yay sallama ciki-ciki haka ita ta amsa masa a hankaki, baice mata komaiba yazo ya sake hayewa gadon ya kwanta.
Rumana ta ƙarasa azkar ɗinta sannan tace, “Ina kwana�.
Kamar bazai amsa mataba sai kuma taji ya amsa da “Lafiya�.
Daurewa tai ta sake cewa “Ya jikin?�.
Nanma dai shirun yayi, harma sai da ta fidda tsammanin zai amsa sai kuma yace, “Alhmdullh�.
Daga haka kowa yay shiru, shi dai barcine ya sake kwasheshi, saboda maganin bai gama sakinshi ba.
Itako duniyar tunani ta faɗa, a ranta sai ƙara girmama hukuncin ALLAH takeyi, yanzu nan Yah Ahmad matsayin miji yake a gareta? Wata zuciya tace, “To gashi ma kun kwana a ɗaki ɗaya�.
Nannauyan numfashi ta sauke, wanda har Ahmad ya jiyota sama-sama a É—an barcin da ya figesa.

Umm-Rumana na zaune a wajen har gari ya fara haske, É—akin kawai take bi da kallo daki-daki, Ahmad dai nata barcinsa, wanda daga inda take tana iya jiyo saukar numfashinsa a hankali.
Sama-sama ta fara jiyo motsin matar gidan da yarinyarta dake kuka, sai kuma zuwa can tajiyo maganar mijin shima suna fira.
Idanu ta lumshe tana tuno gidansu, yanzu tasan gidan nacan da hayaniyar yara daga kowanne sashe, musamman ma sashensu da ke da ƙananun yara da sashen baba ilyasu.
Barcine ya sake saceta a kan abin sallar itama.
Chapter 17 · 0% Book details