← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 94

Sashe 83

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Ahmad suna isa asibiti a gwajin farko aka gano cikin da ke jikin Rumana É—an watanni biyu, wanda Ahmad yake hasashen zuwan su Rumana Saudiyya babu jimawa ta sameshi.
Yayi murna sosai da farin ciki, inda harya kasa haƙuri sai da ya kira Yaya Maryam ya gwargwaɗa mata.
Itama kuma Rumana lokacin tanata barci saboda Ruwan da aka saka mata.
Awarsu kusan shida a asibitin sannan aka sallamesu, lokacin da ruwan da aka sakama Rumana ya ƙare, yanda taga fuskar Ahmad ɗin a washe ya bata mamaki.
Duk da ita ta daɗe da sanin ciki gareta, tunda taga wata ya shige batai jini ba tasan abinda Ahmad ɗin ke fata ya samu, yanda ya koma mafaɗacin ƙarfi da yajine yasa ta danne abunta a rai taƙi sanar masa.
Murmushi ya sake sakar mata yana lumshe idanu, ya jawota ya saka jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, kafin ya É—ago fuskarta yay mata sumba kusan huÉ—u a goshi da kumatunta.
Turesa ta ɗanyi tana faɗin, “Yaya wai mike faruwa hakane?�.
“Kina nufin bakisan mike faruwa bane? Wlhy nasan kin san da abin farin cikinnan kika ɓoyemin Babie R ɗina�.
“Ni bansan komaiba� Rumana ta faɗa tana ɗauke kanta gefe�.
Hannu yasa ya maido da fuskar tata inda take, yace, “Gwal ɗina ke ɗinnan ko, shikenan dai bara sai munje gida kawai�.
Shiru tai bata iya cewa komaiba, suka fito zuwa gida saboda an basu sallama, takumaji daɗin jikinta sosai yanzu babu laifi, sai da suka biya ta makarantar su Haysam suka ɗaukesa, yau ɗinma dai ƙin yarda yayi da Ahmad, sai da yaga Ummien sane saiya gudu ya maƙalƙaleta.
Rumana tai murmushi tana riƙe hannunsa da faɗin, “Oh Sadaukin Abbunsa kana lafiya?�.
Yaron ya faɗa jikinta yana dariyar farin cikin ganinta, koda Ahmad ya miƙa masa hannu sai ya noƙe kafaɗa alamar bazaijeba.
Ahmad yay guntuntun murmushi kawai.
Har suka isa gida Haysam nata bama Rumana labarin abinda take masa tambaya a kai cikin rashin ƙwarewar maganarsa, dan yanzun yanda yake magana da larabci yafi masa sauƙi akan hausar, danma suna ƙoƙarin masa dan basa buƙatar ya manta da yarensa, to dama dai Ahmad ɗinne maijin larabcin sosai a gidan. Sai itama Zainab da yanzu Alhmdllh ta fara ji saboda makaranta, Rumana kam sai jefi-jefi irin na islamiyya da wanda take tsinta annan.

A gida duk yanda Ahmad yaso sakewa da Haysam kamar da can baya sam yaƙi, zai fara kiran ƴan uwa ya baza musu tana da ciki ta fara roƙonshi akan dan ALLAH karyay hakan, badan yasoba dole ya haƙura yabi yanda takeso tunda yasan dai Yaya Maryam ta riga da taji ai.

Cikin hikima kuma ya cigaba da jan Haysam a jiki, da masa wasa tamkar da, sai a hankali kuma yaron ya koma sakewa da shi tamkar da can baya, shaƙuwa ma ta sake shiga tsakaninsu tunda yanata ƙara wayo.
Haka Umm-Ruman ta cigaba da rainon cikinta dake É—an wahal da ita, dan wannan karon da Amai yazo mata, sai dai tanata jurewa dan kar Ahmad yace bazai nema mata makaranta ba sai ta haihu.
Shiko da yaga kamar da sauƙi yanzu sai ya cigaba da cuku-cukun makarantar tata da taimakon Gaddafi, dan matar Gaddafin ma jin ɓangaren islamic Rumana keson faɗaɗa karatunta, sai itama taji sha'awar komawa karatun, duk da kuwa tayi karatu har matakin masters, to a ganinta hakan bai zama ya wadatarba dan islam shine babban tushen da zaka karanta kai alfahari da shi a duniya da lahirarka, boko kuwa aikin alkairin da zakai ta dalilin karantarsane zai amfanar da kai a duniya da lahira.
Komai tare akai musu, Gaddafi ya bada gudunmawa sosai saboda yafi Ahmad ƙarfi sosai.
Randa Ahmad yazo mata da bayanin komai, tare da takardunta sun kammala, jikinsa ta faɗa tana kukan daɗi, bata taɓa zato ko tsamanin irin waɗannan nasarorinba a rayuwarta, amma gashi a dalilin yima iyaye biyayya tama wuce inda kowa yake zato, dalilin haƙurin da tai da Ahmad a farkon aurensu ya jawo mata alkairin da hasashen zuciya bai taɓa kaiwa nanba.
Ahmad dake shafa bayanta yay murmushi yana magana a hankali cikin kunnenta.
“Gwal ɗina tawace ni kaɗai, hakama farin cikinta nawane ni kaɗai, kin cancanci nasarar data kere haka a rayu Umm-Ruman, duk wanda yay haƙuru da jarabawa da ƙyaƙyƙyawar zuciya badan jiran sakamako ba to lallai sai ya kasance mai tarin nasara a nan gidan duniya ko a lahira, karkaga ka wahala iya wahala a rayuwa baka samu nasarar sakamako irin na labarin novels ba ka ɗauka shikenan kai ka rasa, ɗan uwa/ƴar uwa! Kun manta akwai wata sabuwar rayuwar da tafi ta gidan duniya komai? Labarin littattafai misaline kawai wa rayuwa ake nunawa, Iyakar daɗewar ɗan adam a duniya shekaru ɗari ne kacal, amma ka tuna tun zamanin annabawa ake mutuwa, saika shekara talatin kacal a duniya ka mutu kaje kai shekara dubunnai a barzahu kafin a tashi kiyama, mi kake tunani a iya zaman barzahu kawai idan har baka aikata alkari ba a ƙanƙanuwar rayuwarka ta duniya😭, miyasa haƙuri da juriyar jarawar shekarun da bazasu taɓa haura ɗari ba, su gagareka jurewa? Miyasa daɗin da bai taɓa tsallake shekara ɗari na a duniyarka zai ruɗeka ka manta da dubbunan shekarun dake gabanka na barzahu kawai?, miyasa daɗin dake ƙalilan na duniya zai ruɗeka ka manta da ranar hisabi ranar da bata da kwatankwaci ko misali😭?, ranar rarrabe gaskiya, ranar tonon silili, ranar da uwa ke gudun ɗanta, ranar da ɗa ke gudun iyayensa, ranar da kanka kawai ka sani, ranar buɗe ɓoyyayun sirrika😭 (Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un) ƴan uwana! Ƴan uwana! Mi muke tunani haka da zurfine? Mi muke buri haka da yawane? Mi muke fatan samu haka da yawane? Mi muke ƙoƙarin mallaka haka da yawa ne? Mi yake canjamu haka da yawane? Mi yake ruɗarmu haka da yawa ne? Mi muke taƙama dashi haka da yawa ne? Da mi muka dogara haka da yawa ne? Suwa muke tunanin ko zaton sun tsaya mana haka da yawa ne? Ina mukabar imaninmu tafiya haka da yawa ne? Ina muka bar zukatanmu haka da yawa ne?😭😭.

“🙏🏻😭Ya rabbi ka gafarta mana badan halinmu ba�.

Umm-Ruman ta sake ƙanƙame Ahmad tana zirar da hawaye, jikinta na sake yin sanyi game da komai ma, shi kansa da yake maganar hawayen yakeyi......
“Abbu! Kuka kakeji?�.
Sukaji maganar Haysam a kansu a bazata.
Saurin sakin Rumana Ahmad yayi, ya goge hawayensa cikin dabara kafin ya duƙa gaban Haysam dan ya daidaita tsahonsa da shi, ya dafa kafaɗun Haysam ɗin yana murmushi.
“A'a Sadauki na, ba kuka nakeji ba, abune ya faɗamin a ido sai Ummineka take ciremin fa�.
Haysam yay shiru kamar ya yarda, sai kuma ya sake jehoma Ahmad tambaya,
“To Abbu itama ai naga ruwa na fita a idonta?�.
Kai Ahmad ya dafe, yasan Haysam yarone mai matuƙar wayo da basira, kullum ta ALLAH kuma ƙwalwar kansa faɗaɗa takeyi, ya sake girgiza masa kai, ƙasan ransa na tunanin wace amsa zai bashi ya huta.....
Durƙusawar da Rumana itama tayi kusa da shine ya sakashi kallonta, ta dafa hannun Ahmad dake a kafaɗar Haysam tace, “Babana tausayin Abbunka nefa ya sakani hawaye, kaga abu ya faɗa masa cikin ido, amma kuma sai yake gayamin naji tsoron ALLAH a duk inda nake, karna ringa shiga maganar manya, karna ringa shiga abinda ba'a sakaniba, karkuma na saɓama UBANGIJINA, idan nayi akan kuskure na nema gafararsa, dan dukkan mai saɓama UBANGIJI to ƙarshensa baya ƙyau, hakama mai saɓama iyaye baya gamawa da duniya lafiya, wuta ake sakashi, sannan MANZON ALLAH baya cetonsa a ranar kiyama.......�
“Ummie!� Haysam ya kirata cikin katseta.
Ta amsa da “Na'am Haysam�.
“Ummie ita lahirar to a ina take?�.
Kallon juna Ahmad da Umm-Ruman sukayi, sai kuma duk suka maida kallonsu ga Haysam É—in.
Ahmad yace, “Lahira ba'a ganinta, sannan babu wanda zaice maka yaje ya ganota balle ya baka labarinta, sai dai UBANGIJIN al'arshi ya bamu labarinta a littafinsa mai tsarki na AL-QUR'ANI, a wajaje daban-daban, yayi mana bayanin abubuwa masu yawa da zasu faru a cikinta, duk wanda ya mutu a yanzu yana barzahu ne, sai ranar da za'a busa ƙahone kowa zai tashi yaga kansa a lahira, harda ƙwari da dukkan nau'in kowacce halitta da UBANGIJI ya taɓa rayawa a doron duniya�.
Nanma dai shiru Haysam yayi, dan maganganun sun masa girman da bai fahimci komaiba a cikinsu sai ƙalilan, kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru saboda chocolate ɗinsa daya hango, dama ita yazo ɗauka.
Jikinsa ya zame daga garesu yaje ya ɗauki abarsa ya dawo jikin Ahmad ya zauna yana bashi akan ya ɓare masa.
Amsa Ahmad yay ya ɓare masan, yana amsa ya miƙe yafice yana ƙwala kiran sunan Aunty Zainab.
Da ga Ahmad har Umm-Ruman ajiyar zuciya mai ƙarfi suka sauke suna kallon juna, Rumana ta kwanto jikin Ahmad shiko ya rungumeta.
“Abu Haysam!�
Ta kira Ahmad murya a narke.
Idonsa a kanta ya amsa da “Uhyim Umm-Haysam!�.
“Daga yau karmu sake ɓoye masa abu mai muhimmanci da ya shafi rayuwa ko addininmu, ƙwaƙwalwarsa a yanzu a wanke take, komi muka sanar masa zai zauna a cikinta, zama irin na har abada, zai kuma riƙesu a ransa su amfanesa harma da yaran da zasuzo a bayansa�.
Kanta Ahmad ya shafa tare da sumbatar laɓɓanta, sai ya zarce da kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ture kansa tana faɗin, “Yaya wlhy yaronnan zai iya dawowa�.
Murmushi yayi yana lumshe idanunsa da har sun kaÉ—a sun canja launi.

★★�**★★★★�**★★�
Chapter 83 · 0% Book details