Sashe 16
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
............Ƙarfe biyu da rabi na rana ɗunbin jama'a suka sake shaida ɗaurin Ahmad akaro na biyu tare da Umm-Rumana, akan sadaki naira dubu ashirin.
Kansa kawai ya duƙar ƙasa yana haɗiyar zuciya, wai shine aka ɗaurama aure a karo na biyu cikin kwana uku kacal, sannan kuma bada Saminar sa ba, wadda ya ɗauki dukkan buri ya ɗoramawa, dukkan rayuwar aurensa da kullum yake tsarawa a zuciyarsa da itane, amma yau gashi ta nuna masa data zauna dashi gara ta kashe kanta ko shi ta kasheshi.
Kenan yanzu da Rumana zaiyi rayuwar aure? Yarinyar da bai taɓa mata cikakken kallon minti biyarba duk da a gida ɗaya suka tashi, shi zaima iya rantsuwa bai taɓa maganar data kai kalma ɗari da itaba cikin lokaci ɗaya, tsakaninsa da ita a kullum gaisuwa ce, saiko aike, shima sai idan wani dalili yasa ta gitta ta gabansa ne........
Da ƙyar ya iya haɗiye abinda ta toshe makoshinsa, ya ɗago kansa saboda dafansa da akayi a kafaɗa.
Baba Iliyasu dake kansa tsaye yay masa nuni akan ya miƙe, babu musu ya tashi tsaye, kama hannunsa kawun nasa yayi har zuwa gaban jama'ar shema, nanfa Ahmad ya shiga gaishesu cike da girmamawa, saboda yasan dayawan cikinsu dukda bawani sosai ma yake zuwa Shema ɗinba.
Atare suka rankaya zuwa cikin gida, inda aka baje musu tabarmi a zaure suka zauna cin abinci, shi dai Ahmad baici komaiba, yana gefe abin duniya duk ya gallabesa, sai sauke ajiyar zuciya yake a jere a jere.
Bayan sun kammalane sukasa aka kawo musu Amarya Rumana, wadda tun a safiyar yau mahaifiyarta ta zaunar da ita cikin hikima da nasiha ta sanar mata abinda ake ciki.
Tasha kuka, amma tasan ko giyar wake tasha bazata bijirema iyayenta ba, dan ba wannan tarbiyyar mahaifiyarta tai mataba, fargabarta ɗaya tayaya Yah Ahmad zai sota? Mutumin da baya kallon kowacce mace da arziƙi inba Samina ba, ita kaɗai ke ganin fara'arsa, ita kaɗai ke iya jin doguwar maganarsa, ita kaɗai tasan sauƙinsa.
Sukam da ko wasa bayayi dasu, iyakarsu dashi su gaisheshi ya amsa, saiko idan hanya ta haÉ—aku ya aikeka idan da bukatar hakan, ko É—inki zai musu baya tsayawa jin style É—in da suke bukata ko wani ra'ayinsu.
Nasihar da mahaifiyarta da ƴan uwanta sukai mata ce ta sata sake ɗammarar sakama ranta haƙuri, koba komai zata zama sanadin dai-daita barakar dake neman shigo musu a family, sannan zasu hana fitar haƙoran maƙiya da sunan musu dariya, bakin ƴan bani na iya zai rufe ruf wajen maida yanda akayi.
Kanta a ƙasa ta rufe fuska sosai da gyalenta ruwan hanta da akaima kwalliyar ruwan madarar les a baki suka fito, tana sanyene da atanfa ruwan madara mai ƙyau, kayantane na salla da Ahmad yay musu ɗinkin ita da su Samina, kasancewar babansu ne yay musu kayan, dayake sawa biyu kawai tai musu sai kayan suke fes tamkar sabbi, sai ƙamshi take mai sanyi.
Inna marwa dake riƙe da ita tai mata izinin ta zauna, dan sun iso soro inda ƴan shema suke.
Tun shigowarsu kuma Ahmad yake binta da kallo ƙasan ido, wani iri yakeji a zuciyarsa game da wannan auren.....
Nasihar da Æ´an uwan nasu ke musu ta sashi katse tunaninsa ya maida hankalinsa garesu.
An musu nasiha mai ratsa jiki, wadda duk ta kuma sanyaya jikin Ahmad, harma da ita Rumana É—in, dan koba komai ta fahimci wannan auren nasu farin cikin mutane masu yawane, sannan kwaranyewar hawayen mutanene masu É—unbin yawa da Samina taso sakawa kuka.
Bayan an gama musu nasiha kakanni da abokan wasa suka koma tsokanarsu, yayinda wasu acikin Æ´an uwan ke karesu, dansu duka babu mai bakin ramawa, bare dama daga Ahmad É—in har Rumana dama basu da yawan magana.
Bayan sallar la'asar Æ´an shema suka juya zuwa gida, tunda bikine bana shiriba suma basuzo da shirin kwana ba, mutum huÉ—u kawai aka bari suma tsoffine.
Tafiyar ƴan shema tasa hayaniyar gidan raguwa, hakan yasa Ahmad shigewa ɗakinsu ya cire kaya ya ƙwanta saboda zazzaɓin da yakeji sosai, har ya fara rawar sanyi ma.
Daga cikin gida kuwa babu wanda yasan halin da ake ciki, dan sunata shirin kai amarya É—akinta, kayan Samina da aka kaine za'a barma Rumana É—in, tunda dama babu ko cokalin Mama gaje acan, duk dangin su Ahmad É—inne suka tara suka kai.
Ƴan kayan da Ammin Rumana ta fara tarawa na auren Rumana ɗin aka fiddo ake ɗan wankewa, dukda bana kirki bane zasu taimaketa ko yaya dai.
Duk bikinnan da akeyi fa Samina na gidan, saboda ta nuna abinma bai dametaba komanta yinsa take kai tsaye a gadarance a gidan, hakama Mama gaje, har dariya takema Ammi akan haɗin auren Rumana da Ahmad, wai saji sa gani, nan za'a ringa ƙullar tuwo a kwano ana wucewa dashi gidan Rumana, dan sunsan dai Ahmad bashi da abinda zai riƙe Rumana.
Babu wanda ya kulata akan zancen, dan kowa kwllon wawuya yake matama yanzu, daga ita har Æ´ar tata.
Gefe kuma ga munafukan ɓoye irinsu Umma (Sailuba uwargidan baba Iliyasu, aminiyar Mama gaje a gidan idan baku mantaba) dan tana ɗaya daga cikin mai tunzura mama gaje da Samina akan auren Ahmad, bayan itama akwai sangamemiyar budurwa a gabanta Salima, dan sa'arsu Rumana ɗince, tarema suka tashi su uku tamkar tagwaye, Umm-Rumana, Fa'iza ƙanwar Ahmad, sai Salima ɗin.
Ayyah da bataga giccin Ahmad ba tunda aka dawo ɗaurin aurene abin ya dameta, dan haka ta aika a duba matashi ko yana ƙofar gida wajen abokansa.
Koda Abu yaje ya tambayi su Rabilu sai sukace aisu tunda aka dawo daga É—aurin aurenma basu sake ganinsaba, sun zata yana cikin gida yana wani abun.
Babu shiri Ayyah ta fito zuwa É—akinsu Ahmad, saita iskeshi yanata rawar É—ari a bargo, hankalinta ya tashi sosai, tasaka Abu ya kira mata Baba Hamza.
Tunda baba yaga halin da Ahmad yake ciki sai tausayinsa ya kamasa, sunata jera masa sannu shi da Ayyah, a ɓoye ba tare da kowa ya saniba Mudanseer ya kira wani mai aikin asibiti anan kusa dasu ya duba Ahmad ɗin.
Bai ɓoye musuba ya sanar musu damuwace tai masa yawa, shine harta haddasa masa zazzaɓi, dan baya samun isashshen barci ma, ga malleria kuma a gefe itama.
Magunguna ya basa, yace yaci abinci sannan yasha ya kwanta danya samu isashshen barci.
Har Ayyah ta kawo masa fura yasha da ƙyar, zata bashi maganin baba ya dakatar da ita akan ta barshi ba yanzuba, tunda likitan yace akwai na barci suɗan ɗaga ƙafa zuwa anjima, dan Malam yace yau za'a kai Rumana, to kenan bayasha magani yay barci a nanba kuma, bayan an kaita sai yasha yatafi can ya kwanta.
Dole Ayyah tabi wannan umarni na mijinta, suka bar Ahmad, sai dai ruwan ɗumi da aka kawo masa yay alwala yay sallar magriba da isha duk a ɗaki, lokacinne kuma Ayyah ta sawo Gwaggo gaba a ɓoye tazo ta duba Ahmad ɗin.
Sannu tai masa sau É—aya ta É—auke kanta sai kace bata damuba, nanko ranta sai suya yake da halin da yaronta ke ciki, amma kawaici ya hana agani koda a fuskartane.
Kusan ƙarfe tara aka mika Rumana da tasha kuka tamkar hawayenta zasu ƙare ɗakinta, tasha nasiha a wajen iyayenta da dangin mahaifiyarta, malam ya bata ƙyautar da ko ita batasan minene a cikiba, hakama Iya ta bata.
Duk wanda yaga yanda take kuka saita bashi tausayi.
Haka suka mikata, basu wani jimaba suka barota tana cigaba da sharɓar kukanta.
Tunda Ayyah taga ƴan kai amarya sun wuce tazo ta tada Ahmad, da ƙyar ya iya tashi ya watsa ruwan zafi da Ayyah ta ɗumama masa, Abu yakai masa bayi, bai wani jimaba ya fito, jallabiya kawai ya bukaci a basa ya saka, dan haka Mudan ya fesheta da turare sannan ya bashi.
Baice komaiba ya saka, Ayyah tai zaman lallaɓashi yasha magani, da ƙyar yasha kuwa yana tsuke fuska da yamutseta, harda yunƙurin amai saboda tsanar da yayma magani.
Suka dai samu ya haÉ—iye duka da kyar.
Nasiha Ayyah ta sake masa da baba, kafin Mudanseer ya rakoshi inda Sufyan ke jiransa da mashin.
Shine ya ɗaukesa ya kaisa gida, kafin suje sai rawar sanyi yake, yanata sake ƙudundune hannunsa a ƙirji, ga jiri na ɗibarsa sabida rashin ƙwarin jiki.
Dole Sufyan ya taimaka masa har cikin gida, yay sallama a ƙofar ɗakin Umm-Rumana da har lokacin take zaune tana kuka ta amsa.
Izinin shiga Sufyan ya nema, ta bashi sannan ya shiga riƙe da Ahmad cikin ɗakin.
Babu shiri ta mike tana kallonsu a firgice, dan sam batasan Yah Ahmad baida lafiya ba, da taimakon Sufyan Ahmad ya kwanta saman gadon, Sufyan ya mikama Rumana ledar maganin Ahmad da kazar da suka saya musu da lemon ɓawo sai kankana.
“Amarya kiyi hakuri, angonki ya shigo miki ba yanda kowanne ango ke shigoma amryaba, bashi da lafiyane, muna fatan zaki kula mana dashi nanda kwanaki kaɗan ya dawo mana Ahmad ɗinsa jarumi mai yawan juriya da kowa ya sani, ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba, ya kara muku hakuri da fahimtar juna, ya dasa muku soyayyar juna a zukatanku mai karfi daban mamaki da kwatance ga ma'abota soyayya�..
Itadai kanta a kasa tana hawaye bata iya bashi amsaba, ya juya ya fita yana faɗin ta rufe ƙofar shi ya wuce.
★★★★�