← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 94

Sashe 25

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

“Zo nan� na tsinkayo muryar Yah Ahmad.
Kallonsa nayi, dan banyi zaton dani yake ba ganin dai muna zaune ba wani nesa sosai da juna ba, yanda ya tsatstsareni da idanu yasa na miƙe zuwa gabansa na tsugunna.
Yace, “zauna da ƙyau�.
Zaman kuwa nayi cikina na sake É—urar ruwan tsoro.
Kallona yay sosai ko ƙyaftawa bayayi, ga fuskarsa babu alamun wasa yace, “Ina wasa da ke?�.
Da sauri na girgiza masa kai idanuna na cika da ƙwalla, dan bansan mi nayi ba, sai matse hannuwana nake cikin na juna.
Ya cigaba da faɗin, “Kinsan daga yau ɗinnan da nake miki magana, idan har na sake ganinki zaune da matarcan kuna wata doguwar hira bayan gaisuwa sai na miki shegen duka a gidannan, wato ma har labarin daren farko kika bata....?�
Da sauri na girgiza masa kaina ina faɗin, “Wlhy A'a Yaya, ALLAH ban taɓa ba tunda nake�.
“Ba gashi tana miki hirarba, ke har kinkai girman sanin akwai wani abu shi daren farko ga amarya daman?�.
Hawayen da suka zubomin a saman fuska na share ina cigaba da girgiza kai dan na kasama magana.
Ahmad dake haɗiye dariyar yanda Umm-Rumana ta rikice da ƙyar ya kuma zazzaro mata idanunsa, danshi duk yana yine danya ƙwaɓeta da wuri karta saka kanta a wannan masifar ta shegen gulma, shiyyasa tunda suka tare a gidan ɗabi'un maman Ama basu masaba har mijinta, sam bayason mu'amularta da Umm-Rumana ɗin.
“Kinga daga yau, bama itaba, ko wannan da aka kawo jiya karnaga wata aminta ta haɗaki da kowace shegiyar mata ama anguwarnan ba gidannan kawai ba, inko hakan ta kasance kema kinsan sauran, tashi ki ban waje�.
“Kayi haƙuri dan ALLAH Yah Ahmad, zan kiyaye insha ALLAHU, amma dan ALLAH ka yafemin�.
Duk da ta bashi tausayi sai cayay kawai, “Ya rage naki�.
Tashi Umm-Rumana tai ta koma gefe tana cigaba da sharar hawayenta.
Ahmad dake buɗe zani ɗaya zai fara yanka yace, “Wlhy kika bari Mudan yazo yaga waɗannan hawayen ko, saina sassafaki a ɗakinnan�.
Babu shiri Rumana ta goge hawaye tsaf, sai ko ga Mudanseer ya dawo É—auke da leda yellow mai layi-layi.
Yana ajiyewa ko zama baiyiba yace zai koma yana da aiki a shago, gashi zaije makaranta da yamma.
Godiya nai masa yay mana sallama ya fice.

Haka na tashi na fidda cefanen, Yah Ahmad nata yankan ɗinkinsa da duk ya maida hankalinsa wajen. Sai da zan fita waje girkine yace nayi anan ƙofar ɗaki basai na fitaba.
Duk da nasan zafin wuta zai ƙarama ɗakin zafi haka nabi umarninsa tunda risho ɗin ba hayaƙi yakeba, kayan miya kawai na fita na wanko tare da ɗanyen kifi da Yah Mudan ya sayo mana a waje nazo ɗaki na niƙa a gireta, kifin kuma nai ƙoƙarin sashi a wuta danna ɗan tafasa da kayan ƙamshi na rage masa ƙarni.
Maman Ama kawai kake iya jiyowa a tsakar gida da yaranta, amaryarmu kuwa suna É—aki sai dai kajiyo sautin dariyarsu.
Da yake girkin bawani mai yawa bane dan danan nagama girka mana shinkafa jalof, wadda a ido kawai dolene ta birgeka saboda aikin nutsuwa ne, na kwashe a kula gaba É—ayanta na gyara wajen kamar banyi komaiba.
Har lokacin kuma Yah Ahmad nata yankan kayan, sai lokaci-lokacine yake amsa waya idan an kirashi, nama lura mafi yawa abokansane ke tambayar lafiya? Sunga bai fitaba, saiko Customers masu amsar ɗinki ko masu kawowa............✍�

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899

*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*(16)*

.............Kiran sallar zuhur da akeyine ya saka koda na gama gyara wajen sai ban zauna ba, na É—auki buta na fita.
Ina fitowa Amaryar jiya da mijinta suka fito daga bayi da alama wanka sukayo tamkar É—azun da safe, harga ALLAH ban kawo komai a raina ba, saima sannun da sukaimin na amsa na shige banÉ—akin.
Na fitone idona ya sauka akan mama Ama dake leƙe ta Windown ɗakinta, sai dai ganin kamar na ganta ya sakata saurin sakin labulen, kaina kawai na girgiza, na zauna bakin rijiya ina alwala.
Sai ko gata itama zumut ta fito da buta a hannu, tazo gab dani take faɗin, “Amarya an tashi kenan?�
Kallonta nayi da ƴar fara'a nace, “Ai dama ba barci nakeba, aiki nake yima a ciki�.
Tai wata ƴar dariya idonta ƙyam akan jelar gashina, “Ai najiyo ƙamshi har nake zance da zuciyata akan yau kuma amarya a ɗaki ake girki? Ko kayan daɗi za'aci tunda naji ƙamshin kifi na tashi�.
Nace, “A'a, kawai dai dan Yah Ahmad na gidane na zauna saboda na tayashi hira�.
Buɗar bakinta sai cewa tai “Ku hirar kuke, wasuko da ranar ALLAH suna gado suna murzar juna, wannan matar inaga da bamu da maza a gidannan lallai da munsha kallo, aini yau naga bariki wai wanka da miji da tsakar rana�.
Shiru nayi danni sam maganar tata tazomin a baibai, na farko dai ban gama fahimtar gundarin maganar ba, na biyu kuma bansan minene matsalarta da wannan amarya ba, miye laifi idan tayi wanka da mijinta? Bayan malamin islamiyyarmu ya taɓa bamu wata ƙissa da MANZON ALLAH ke wanka da *Nana Ai'sha (R.A)*.
Zaram na miƙe saboda fitowar Yah Ahmad daga ɗaki, a duƙe na ƙarasa alwalar maman Ama na tsaye a kaina, tana jiran Yah Ahmad ya gotamu ta ɗora maganarta daga inda ta tsaya.
Da azama na bar wajen ganin ya nufi bayi, na faÉ—a É—akina ba tare da na sake koda waiwayenta ba.
Gaskiya matarcan lamarinta na bani mamaki da ɗaure kai, shikenan kai bazaka damu da rayuwarka ba sai ta wani, dole nazo na roƙi Yah Ahmad komawa makaranta kodan gujema halayyar maman Ama ta son kafa da'irar gulma a gidannan.
Chapter 25 · 0% Book details