← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 94

Sashe 28

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Haka rayuwar wannan gida ta cigaba da tafiya mana, inda nake ganin sabbin salon É—abi'u daga matan gidan, dan a hankali dai maman Ama kejan kausar jikinta, kullum kuma babu fashi sai sunba junansu labarin maganin mata da sukai amfani dashi da dare, harma da gwargwadon aikin da yayi akan mazansu, gefe kuma maman Ama na zuge Kausar akan Uwargidanta, dan tanada kishiya a wani gidan da ban.
Lokaci ƙanƙani saiga amintaka mai ƙarfi ta ƙulle a tsakaninsu, inda kuma idan ɗaya na ɗaki yazama ina tare da ɗaya a waje kaji yana sukar ɗan uwansa da gulma.
Kamar yanda Yah Ahmad ya ƙwaɓe ni babu ruwana to haka naja kaina, iyakata dakin gama nace ALLAH ya ƙyauta kawai nabar miki wajen, koma kina cikin faɗar nasan dabarar da zanyi na bar wajen.
Basa iya riƙe sirrinsu, kowacce cikin zayyanema ƴar uwarta halin da take ciki suke, hatta da abinda sukaci da dare idan miji yaɗan sayo saisun bama juna labari, wani lokacinma na lura da biyu akeyi saboda ni, sai kuma lamari yaso juya akala kan maman Ama, dan kuwa dai Kausar tafi zaƙewa akan sayayya irinta ƙwalam da naƙulashe da mijinta ke mata, dan da safe har sauran naman kaza ko tsire ko balangu ake kasowa a filet ni da maman Ama duk dan mugani, tun ranar farko Yah Ahmad ya takan birki akan amsa, dan haka na bama Kausar amsa da ni bama nacin nama kwata-kwata, sai ta koma bama Maman Ama kawai, itako maman Ama zata amsa taci amma hakan na sakata baƙin ciki, dan zakiga tanata fushi da kawomin sukar Kausar wai tana badawane dan ace ta fimu jin daɗi wajen miji, nidai bancewa komai.
A kwana biyunnan kuma sai naga itama maman Ama ta fara ɗabi'ar kaso abu ta bamu wai a zuwan tsarabar kasuwa baban Ahmad yazo dashi, itama dai bana amsa saboda gudun ɓacin ran Yah Ahmad.
Ƙiri da muzu sai gulmarsu ta koma kaina, yayinda a gefe kuma suke kishi da juna, ni lamarin nasuma dariya ya koma bani, duk da sun gimeni amma idonsu na kaina, ni kuma bawani abu gareni na nunawa a garesu ba, tunma danazo gidan inaga sau uku nasan naci nama, biyu nama ɗaya kifi, suma duk na abincine da ake saye bai kuma wuce na ɗari biyu.
Zuwan da yaran gidanmu ke yawan yine yake É—aukemin kewa, muyita hirarmu a É—aki, sai kuma sukace na fara musu wani abu na saidawa kamar alawar madara ko aya ko iloka da makamantansu.
Banyi musuba nace su bari idan Yah Ahmad ya dawo zan sanar masa, idan ya amince to zan ringa yi musu.

Tun daga wannan ranar na fara sana'ar abubuwan yara, dan kuwa Yah Ahmad koda na gaya masa sai bai musaba, ya bani dubu É—aya da É—ari biyar yace nayi jari, godiya nai masa sosai.
Abun har yayta bama Ahmad mamaki, domin kuwa yakan tuna Samina da kuɗi kaɗan kansata tayi fushi, idan ta tambayesa 3k ya bata 2500 aka tai haƙuri bashi dasu, to ranar kam sai tayi fushi dashi akan 500 da babu koda zata amsa 2500 ɗin kuwa, sai idan ya cika mata ɗari biyar ɗinne zasu dawo dai-dai.
Amma yau gashi ya bama Umm-Ruman 1500 kawai matsayin jari tanata masa godiya kamar ya bata 100k.
Yaji daɗin hakan sosai, musamman ma da yaga ta bada himma akan sana'ar, dan kuwa gida ta aika dasu Ammi ta sai Gyaɗa da aya aka soya aka ƙullo daga can, ƙannenta suka ɗauki wata sauran aka aiko mata nan gidan saboda yara masu shigowa.
Akan wannan sana'a ba ƙaramin dariya Kausar da maman Ama sukayiba, acewar Kausar ita yanzu ai bata da time ɗin wata sana'a, yaushe ma ta gama morar amarcinta da har zata takura tunaninta wajen wasu ƙulle-ƙulle.
Maman Ama kuwa tace ai ita bama zata iya sana'ar naira biyar ba, domin sana'ar yarace.
Rumana dai batace komaiba, sai ma murmushi da tai musu kamar yanda ta saba.
Duk kuma wannan abun da suke Ahmad na É—aki kwance yana jiyosu, su kuma basuyi tunanin yana nanba, dan da takalmansa ya shige ciki bayan ya dawo sallar juma'a, lokacin da ya shigo duk suna cikin É—akunansu.
Koda Rumana ta shigo É—akin baice mata komaiba game da maganar, dan shima takaicin abinda Samina ta masa yau ne a gidansu ya sakashi zuwa ya kwanta.

______________________________
Chapter 28 · 0% Book details