Sashe 35
Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da sauri Maman Ama da Kausar da suka haɗa kai suna gulma a ƙofar kicin suka hau washe baki kamar gaske.
“A, Amarya barka fa ƴan tafiya an sauka lafiya�.
Umm-Ruman ta amsa da “Yawa, ngd�.
Tasan dai gulmarta sukeyi, tunda kullumne babu fashi, har maƙwafta surutu suke zuwayi akan wai Yah Ahmad ya watsar da ita tsahon wata shida yaƙi dawowa, ƙilama ya gudune, idan iyayenta sukaji zasuzo su kwasheta itada kayan tunda mai gidan haya dai ba lamuni zaiyiba idan shekara ta ƙare.
Yanzukam gulmarta suke akan wai ashe tasan mijinta zai dawo shiyyasa taketa ɓare-ɓaren gyara jikin tarbarsa, amma da suka tambayeta sai tace kwalliyar bikice.
Kausar harda cewa, “Yo kwalliyar iyakar fatar ido dai zata tsaya tunda ba wata uwa zai iya mataba�.
Sosai maman Ama taita dariya da faɗin, “Wa yaga lagwani� shinema Rumana ta fito ta ritsasu.
Sai da taÉ—an sake É—auraye masa bayin sannan ta ajiye ruwan ta fito.
A ƙofar ɗaki ta iskesa zai fito, hannunsa riƙe da abin wanka da brush da ya sakama makilin, ta matsa ya wuce bayan ya ajiye takalman daya fiddo na silifas.
Aiko harya shige banɗaki su maman Ama na binsa da kallon ƙurilla, so suke suga abin kushewa a samu nayi, sai basu ganiba, dan saima wata ƙiba data ƙara masa cikar zati da kwarjini ya ƙaro.
Sai suka koma faɗin, ba dole ya narko ƙibaba yanacan yanacin daɗinnsa ya bar Rumana anan cikin wahala daga fara da mai sai wainar filawa.
Karaf sai zance a kunnen Umm-Ruman data fito É—auraye filet É—in da zaici abinci.
Kanta kawai ta girgiza tana mamakinsu ta koma É—aki abinta dan gulma ta rufe musu ido basuko farga da itaba.
Koda Umm-Ruman ta koma ɗaki sai ta ɗauki turaren tsinke ta sake kunnawa, duk da dai da safema ta kunna, kuma Alhmdllh ƙamshin ya kama ɗakin saboda nacin saka turaren da takeyi ga firishina ta haɗawa da yaya maryam ta kawo mata mai ɗan yawa, tanata ɓoyen abunta sai kaɗan- kaɗan take sakawa har turaren wutarma, na tsinkenne dai kullum saita kunna saboda da yawa aka kawo mata su..
Tana ƙoƙarin kunna fitila saboda duhun magriba da garin yayi Ahmad ya shigo ɗakin da sallama, Amsawa tai ba tare data juyi ta kallesa ba saboda kunya, duk da tasan akwai jallabiya a jikinsa kuwa.
Batai auneba taji hucin mutum a bayan, cikin ɗan hanzari ta juyo, Ahmad dake tsaye a bayanta ya miƙa hannu zai ɗauki robar mai dake saman madubin, gefe Rumana ta matsa, duk da hakan kuma jikinsa na taɓa nata saboda lungun wajen baida girma sosai.
Baice da ita komaiba, duk da ya lura da yanda taketa zare idanu, ya ɗau mansa ya zauna abakin gadon danya shafa, ganin taƙi wucewa ya ɗago fararen idanunsa ya ɗan kalleta.
Saurin raɓashi tai ta fice, ya bita da kallo kawai yana girgiza kansa.
Tana alwala a bakin rijiya yazo ya wuce zai fita massalaci, ta shaƙi ƙamshin turaren daya saka tana binsa da kallo, sosai taga canji daga garesa, sai taga kamar an wani canja matashi, dan yanda jikinsa kawai ya murje zai baka amsar tafiya tayi riba.
Da wanna tunanin ta shiga É—aki itama ta kabbara salla.
Ana idar da sallar magriba sai gashi ya dawo, a bakin gado ya zauna dai-dai tabarmar data É—ora kayan abincin, waya yakeyi, dan haka ta matso ta fara zuba masa abincin a filet, harta kammala zubawa yana wayarsa, sai dai idonsa na kanta kamar ya samu talabijin, dukda tanajin yanda idonsa ke yawo a jikinta tunÉ—azun ita bata yarda ta kallesanba.
Kauda kwanikan tayi gefe yanda zaiji daɗin sakewa a wajen sosai, ta yunƙura da niyyar ta miƙe kawai babu zato taji ya ruƙo mata hannu, kafin ta gama tantance gaskiyar lamarin ta tsinci kanta ɗare-ɗare bisa cinyarsa.
Kasa magana tayi dan matuƙar al'ajabinsa, ga jikinta sai wani yamm yakeyi, Ahmad ya ajiye wayar gefe tare da kallonta sosai, yanda yake kallon fuskarta babu wani alamun jin ba daidaiba ne ya sakata kasa jurewa ita, gashi fuskarsa sam babu walwala, kamar dai yanda ta saba ganintane acan baya.
Hannu ya saka ya ɗago da haɓarta yana ƙoƙarin zare hijjab ɗin, bata hanashi ba, dan batagama fuskar yin hakan daga garesaba, sai sake matse hannayenta take waje ɗaya illahirin jinin jikinta na gudu cikin kowacce jijiya da sauri.
Ya ajiye hijjab ɗin saman gadon ba tare daya tankaba, goshinsa ya ɗora saman nata, mutuniyarku saita sake ruɗewa, cikin in ina tace, “Ya..ya a...b in ....cin za..i zai huce fa�.
Ahankali ya furta “idanma ya huce bakece kika ja ba?�.
Babu shiri ta ɗago idanunta sai suka afka cikin nasa, dan har yanzu goshinsa nakan nata, hancinsu gab da juna suna musayar numfashi, hakama bakinsu babu wata tazara duk da ita Rumana taɗan duƙar da kantane ba kamar yanda nasa yake daret ba.
Ƙasa ta sake maida idanun dan bazata jura kallon cikin nasaba, cikin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace, “Yaya ni kuma?�.
Ahmad da muryar Rumana ta saukar masa da kasala yace, “Uhum mana, ke haka aka koya miki tarbar miji ne? Wata shidda bama tare amma sam banga wani murnar ganina ko kewata a tare da keba�.
Karon farko da kanta ya kasa É—aukar kalamansa, domin batai tsammanin wannan furucin daga garesa ba. Saita kasa bashi amsa, wasa dai taketayi da hannayenta dake bisa cinyarta, itako tana saman tasa zaune ko nauyinta bayaji.
Hannunsa dake zagaye da ƙugunta ya janye ya kamo hannayenta da taketa cuɗawa waje ɗaya.
Sosai jan lallen da akai mata wanda ya gaurayu da zanen baƙi yayma choco fatarta dake kama da tasa ƙyau, ya janye kansa daga goshinta yana sauke sassanyan numfashi tare da murza yatsun hannun nata duka cikin hannayensa.
“Tunda bakiyi murna da dawowar tawa ba, ɗagani na koma inda na fito�.
Da sauri ta girgiza kanta idonta na cikowa da ƙwalla “ALLAH yaya ba haka baneba fa, nayi murnar dawowarka mana�.
Tsura mata ido yay, yanda idanunta suka kawo ruwa suna fidda wani ƙyalli saboda hasken fitilar sun ƙayatar dashi, ɗan yatsa ya ɗora kaɗan ya dangwalosu yayinda suka gangaro kaɗan saman furkarta, “Har yanzu kina nan a shashasharki dai?�.
Baki Rumana ta kumbura kaÉ—an wai ita dole taji haushi ya cemata shashasha.
“Haushi kikaji?�
Yay maganar cikin kunnenta yana sunsunar dokin wuyanta dake kamshin khumrar data shafa.
Da sauri ta sinne kai ƙasa, jikinta na ɗaukar ƙyarma saboda sabon al'amarin da yakeyi mata.
Baki yaɗan taɓe yana saka hannu ya ɗago haɓarta suka kalli juna, “Oh jan ajine komi?�.
Kasa jure kallon tayi tana janye idanunta, “A'a kawai dai banyi zaton dawowar taka bane ba yanzu�. Tai maganar cikin sarƙewar halshe.
Karon farko yayi murmushi har haƙoransa na bayyana, ya yunƙura tare da miƙar da ita shima ya miƙe, harkan tabarmar suka isa hannunsa riƙe da nata, ita dai ji take tamkar ta tsilla da gudu, sai da suka zauna sannan ya saki hannun nata, yakai hannu ya jawo filet ɗin abincin gabansa ya faraci ba tare da ya sake cewa komaiba.
Rumana dai na zaune duk a takure, addu'a take ALLAH ya kawo mai belinta yanzun nan, sai dai addu'ar tata bataci ba, dan kuwa har ya kammala cin abinci babu wanda ya shigo, sai motsin matan gidan da suke jiyowa daga tsakar gida.
Shikam Ahmad yanacin abincine idonsa akanta, musamman ma ƙushinta data gama tsole masa idanu tun shigowarsa gidan, amma da yake jarumin dakewane bazaka taɓa fahimtar hakan akan fuskarsa ba.
Ya kammala cin abincinsa tsaf sannan yasha ruwa yana yin hamdala, dai-dai nan aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.
Wayarsa ya ɗauka yay kiran wani da taji yana ambata da Nura, kusan mintuna biyu suna wayar sannan ya kashe, miƙewa yay tsaye yana zira wayar cikin aljihun jallabiyarsa, “Bara naje salla, daga can zanje gidan dan bamu gaisa dasu baba ba�.
Kan Rumana a ƙasa tace, “Saika dawo a gaishesu�.
“Uhum� ya faɗa yana ficewa daga ɗakin.
Sai da Rumana ta jiyo fitarsa daga gidan gaba É—aya sannan ta sauke numfashi tana murmushi, ta kalli hanunta sosai da yasha murza a nasa ta lumshe ido, wai yau itace bisa cinyar Yah Ahmad zaune É—ane-É—ane, yana mata magana cikin taushin murya da sanyi.
Duk da tasan ba sonta yakeba hakan ba ƙaramin daɗi yay mataba, salla ta miƙe ta gabatar sannan ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage a filet ɗin tana mai jin wani tsagwaron nishaɗi...
★★★★★★