← Book details Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 94

Sashe 91

Gudu Da Waiwaye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma bayan Mudan ya dawo daga kasuwa ya kwashesu a motarsa har zuwa anguwar da Ahmad yay gini wanda ko a labari bai taɓa sanarma Rumana ba, dukda ahima dai a hoto kawai yake ganin gidan, dan Mudan ne tsaye akan komai har aka gama.
Gidajene guda uku jere da juna, na Ahmad, saina Mudan, sai Abu kuma.
Anguwar sabuwar anguwace, amma kuma dai ta cika da gine-gine sabbi, sai dai babu hayaniya sosai da yake ba kowane ya gama dawowaba, amare ma sunfi yawa a anguwar.
Tunda suka shigo gate ɗin gidan baƙi da kwalliyar gold a jiki Umm-Ruman ta saki baki tana kallon gidan, bawani ƙato bane amma kuma an masa gini mai ƙayatarwa.
Ta kalli Ahmad dake murmushi, gira ya É—aga mata tare da kashe mata ido yana kama hannunta cikin nasa.
Bata iya cewa komaiba tabisa, hakama yaran binsu sukai suna tsallen-tsallensu.
Mudanseer ya buɗe ƙofar shiga falon yana faɗin, “Kowa ya shigo da addu'a, musamman ke Umm-Ruman dan dagake babu wata a gidanan harma dana Saudiyya�.
Dariya suka sanya, Ahmad yace, “Amma Mudan kai ɗan bukulune, baƙin ciki kake naƙaro amarya?�.
Sosai suke dariya yanzu banda Ruman dake ƙoƙarin ƙwace hannunta tana cika, Ahmad yay saurin sake damƙewa yana dariya da faɗin, “Kinga gimbiyar mata wasa nake, ai kishiya ko a mafarki babuke babu ita�.
Nanma dai dariyar sukayi, banda su Haysam da tuni sun shige cikin falon da gudu sun É—are kujeru.
An gyara falon tsaf, komai an saka a gidan, dan haka suka shiga zagayawa ko ina, a ƙasa akwai ɗakin Rumana sai ɗakin baƙi saina yara, akwai kuma wani anyi ƙofarsa ta fita can waje shima dai na yaranne idan sunyi girma, sai kicin da kafin ka shigesa akwai dani farko.
Kasancewar falon babbane an shirya kujerune har kashi uku a cikinsa, dolene tsarin ya burge mai kallo.
Sai ƙafar bene da zata kaika can sama inda ɗakin boss Ahmad yake, kafin ɗakin akwai falo guda biyu da kuma wani ɗakin bayan nasa.
Gaskiya gidan yayi ƙyau matuƙa, gashi an zuba komai masha ALLAH, Ruman ta rungume Ahmad tana hawayen jin daɗi, yau sune da gidan kansu bayan wahalar haya da sukai na tsahon shekaru har a ƙasar da ba tasuba.
Dariya Ahmad yakeyi, ya jata jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Haba Gwal ɗina, minene abin kuka kuma anan?�.
“Dolene nai kuka Yaya, UBANGIJI yay mana sutura kashi-kashi da baki bazai iya faɗaba, muna godiya a garesa irin wadda bata yankewarnan a saman harshe, Yaya kayi Surprise ɗina wlhy, koda wasa ban taɓa kawo hakan cikin rainaba�.
“Dolene mu godema ALLAH Ruman, zakuma mucigaba da gode masa har ƙarshen numfashinmu, naso na faɗa miki batun gidan amma sai nace bara dai na bari idan mukazo ƙya gani insha ALLAHU, munrigada munyi yawa yanzu, idan mukace zamu zauna acan zamu takura musu muma mu takura, shiyyasa da Mudan ya samu fili nima sai nace ya bincika mana, to sai aka dace aka samu harma na Abu, a hankali mukaita ginawa ana hutawa har gashi an kammala cikin amincin ALLAH�.
DaÉ—i yasa Rumana sake rungume Ahmad.
Ya dungure mata kai da faɗin, “Nima ai na rama ne, kina tare da new baby na amma shine ban saniba ko?�.
Dariya sosai Rumana keyi, ta kama hannunsa ta ɗora saman cikinta, “To kayi haƙuri Yayana, ai gashinan kaji yanzu, ya kamata ace kafin kowa ya ringa sanin inada ciki kaine zaka fara ganewa, amma koda yaushe sai an faɗa kake ganewa�.
“To ya na iya, nidai fa naji gimbiyar ta ƙara ɗanɗano, amma sai ban ranfoba� yay maganar a cikin kunnenta.
Fuskarta ta ɓoye a ƙirjinsa suna dariya, shigowarsu Haysam yasa suka saki juna.

Gida suka koma a ranar, sai a washe garine suka dawo gidansu gaba ɗaya bisa rakkiyar ƴan uwa da abokan arziƙi, kowa nata yaba gida da tsarinsa, sai dare kowa ya kama gabansa aka barsu su kaɗai a gidansu, Zainab dai ta maƙale wajen Gwaggo akan itafa tana can sai idan zasu komane.
To yazam ma zaman su Haysam ba sosai ananba, sai aka bar Umm-Ruman da Ahmad kawai, suma wani lokacin can gidan suke yini.
Suna kwana na tara da dawowa Ahmad yaje gidan Alhajin nan na anguwarsu da suka taɓa haɗuwa a saudiyya dansu gaisa yay masa godiya bisa alkairin da yayma su Baba, da kuma tsayawa da yay akan ginin gidajensu, dan shine yay tsaye akan komai har gyaran gidansu saboda sana'arsa kenan saida gidaje.
Alhaji yayi farinciki da wannan ziyara tasu Ahmad, sun kuma karramasu karramawa ta mutunci da girmamawa, sannan ya bama Ahmad dama akan ya É—auki mota a gidan yaje yay amfani da ita har su tafi, dan baikamata yayta yawo a motar hayaba.
Ahmad yayi godiya da wannan karamci, ya amshi key É—in da Alhajin ya basa suka koma gidama a motar daya bashin aro.

Satinsu biyu cif da dawowa baba ya zaunar da Ahmad akan maganar Samina, da kuma halin da mama gaje ke a ciki na taɓin hankali, dan yanzu lamarinta ya sake turewa sosai, zata zauna taita surutai tana faɗin tsiyatakun da sukai ita da inna mari, wani lokacin kuma saita haɗa kwanaki batai maganaba, sai dai kallon mutane da idanu.
Ahmad yaji tausayinta sosai, ya kuma aminta zaije ya fiddo Saminar kafin a shiga hidimar bikin su Mudanseer.
Washe gari kuwa tamkar yanda yay alƙawari haka ya shirya shida Mudan da Abubakar da baba ba tare da kowa ya saniba suka nufi prison iɗn da aka saka Samina.
Acan suka tadda Alhaji Hamisu dazai taimaka musu tunda shiÉ—in sanannen mutumne kuma mai jama'a.
Koda suka iso prison É—in, Ahmad da Alhaji da babane kawai suka shiga, akabar Abu da Mudan a mota.
Suna nan zaune kusan awa ɗaya da wasu mintuna sai ga Ahmad ya fito ransa a ɓace, ya buɗe baya ya shiga ba tare daya cema su Mudanseer komaiba, sai dai bai rufe murfinba ƙafafunsa duk suna waje ma.
Suma yanayin da suka gansa a cikine ya sakasu yin gum da bakinsu basu iya cewa uffanba.
Suna nan zaune babu mai cema É—an uwansa komai har kusan mintuna talatin sai ga baba da Alhaji sun fito.
Sam Ahmad baiko É—ago kaiba dukda yaji takun isowar su Baba wajen, yanata danna waya abinsa.
Baba yace, “Sannu sarkin zuciya, Amadu wai sai yaushene zaka rage wannan zafin nakane haka? Daga magana sai kayi fushi ka fito?�.
Murmushi Ahmad yay yana É—ago gansa zaiba baba amsa, sai idonsa karaf akan Yamusashshiyar tsohuwa mai kama da Samina.
Duk yanda yaso daurewa kasawa yay sai da yace, “Baba wannan ɗinfa?�.
Baba yay murmushi mai ciwo yana kallon inda Samina ke tsaye kanta duƙe a ƙasa tana hawaye, ya kalli su Mudan da suma sukai mutuwar tsaye suna kallonta sannan ya bama Ahmad amsa da cewar “Ƙanwarkuce Samina�.
A cikin matuƙar firgici sukace, “Samina fa Baba?!!�.
Ƙasa ta durƙushe tana wani irin kuka maiban tausayi da cin zuciya.
Baba yace, “Kunga kushiga mota muje kunji, wannan ba maganar nan baceba, ɗiyata tashi bar kukannan haka ya isa kinji�.
Kasa tashi Samina tayi, sai da Baba ya taimaka mata sannan ta miƙe daƙyar, ita da Baba suka shiga mitar Alhaji, Ahmad kuma dasu Mudan suna a motar Mudanseer ɗin.
Babu wanda ya iya sake tofa komai har suka isa gida, kowa sai saƙawa da kwancewa kawai yake a cikin ransa, gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi musamman ma Ahmad da sam bai taɓa kawoma kansa ganin Samina a wannan yanayinba, yanda yay matuƙar tsanarta sai tausayinta ya rage wani kaso a ciki.
Abu kam kasa daurewa yayi saida ya share hawaye saboda tausayin ƴar uwar tasu, ko iyayensu da suke tsoffi sunfi Samina ƙyawun gani a ido.

Da suka iso gidanma Samina kasa fitowa tayi a motar saboda kunya da matsananciyar tashin hankali da damuwar da take ciki, taso ace anbar rayuwarta ta ƙare a jail, dan tana jin kunyar haɗa idanu da mutane musamman jama'ar gidansu, tasan dukda tsahon shekarun data ɗauka mutane bazasu gaza tunawa da ta'asar data aikataba a baya, kuma bazasu gaza yin zunɗentaba, sannan babu abu mafi ɗaga mata hankali a yanzu irin ganin Ahmad da tayi.
Baba ne ya kamo hannunta ya fiddota, kasancewar yanzun ƙofar gidan nasu yazama wata ƙaramar kasuwa yasa idanu sukayo musu ca, dukda babu wanda ya gane Saminar saboda fita hayyacinta da tayi.
Lokacin da zasu shiga gidan sai kawai ta fashe da kuka mai ban tausayi, wanda yaso É—aga hankalin su Ahmad fiye da wanda tayi a baya.
Raɓasu yay ya shige abinsa tamkar abun bai damesa ba, hakan yasa baba ya bisa da kallo yana girgiza kai kawai, yasan Ahmad idan har ya tsani abu tofa ya tsanesa kenan sai kuma ta ALLAH kafin ya sake waiwayensa.
Da lallashi ya samu Samina ta shiga gidan, kai tsaye sashinsu ya wuce da ita, hakan yasa su Gwaggo da sukasan da zuwa ɗakkotan suma hankalinsu ya tashi matuƙa.
Gwaggo ta kama hannun Saminar ta saka a jikinta itama tana hawaye, hakama Ayyah kuka takeyi, iyama da Abu yaje ya kira ganin Samina ya matuƙar ɗaga hankalinta.
Sauran matan gidan babu wanda yasan mike faruwa, sai su Haysam dake gidan da sukai tsaye suna kallon Samina, Abu-Turab ma zuwa yay bayan baba ya ɓoye yana kuka wai tsoron Samina yakeji.
Baba yay murmushi tare da ɗaukarsa yana lallashi, “Haba Iliyasu minene abin kukan to, wannanfa ba abin tsoro bace innarkace kaji�.
Noƙe kafaɗa Abu-Turab yayi yana sake ɓoye fuska a jikin baban.
Baba ya sake yin murmushi yana shafa bayansa.
Chapter 91 · 0% Book details